Site icon Dubawa

Bidiyo ne na Mali aka yi karyar barazanar kai harin ta’addanci a Najeriya

Mali video falsely used to portray terror threat against Nigeria

Da’awa: Wani mai amfani da shafin X (@razorblade300) ya yada wani bidiyo inda yayi zargin cewa ‘yanta’adda daga bangaren Fulani na barazanar kai hare-haren ta’addanci a wasu yankuna da dama a Najeriya.

Bidiyo ne na Mali aka yi karyar barazanar kai harin ta’addanci a Najeriya

Hukunci: Karya ce. Wannan bidiyo daga Mali ne ba Najeriya ba, kuma mai maganar ba barazana yake ba kamar yadda mai da’awar ke cewa.

Cikakken Labari

Wani mai amfani da shafin X a ranar 12 ga ewatan Yuni,2026 ya yada wani bidiyo mai tsawon minta daya da dakika shida kamar yadda za a gani (anan), inda ake zargin cewa Fulani ‘yanta’adda na barazanar kai hare-hare a sassa daban-daban na Najeriya.

Bidiyon ya nuna wasu mutane sanye da kaya na soja iri daya suna tsaye a bayan wanda ke maganar. Mun kuma lura cewa mutanen dauke da bindigu ga kuma wasu can suna daga nesa a kan babura.                                                                                                                                                             

As of June 20, 2026, the post had gained over Ya zuwa ranar 20 ga watan Yuni,2026 wannan wallafa ta samu wadanda suka kalla 313,000 (views) da wadanda suka sake yadawa  440 (reposts) da wadanda suka nuna sha’awarsu 1,300 (likes) da masu ba da amsa 235 (replies) da wadanda suka nuna alama ta cewa za su sake dubawa 318 (bookmarks).

Wannan da’awa ta samu martani kala daban-daban.

”Idan kasashen Afurka basu hada kansu ba, su lura da iyakokinsu za su fuskanci zagon kasa ta fuskar tattalin arziki daga masu Jihadi da ‘yanta’adda da ake daukar nauyinsu. Ya kamata mu zama masu kulawa iyakokinmu basu da tsaro sosai a Najeriya, ” wannan shine abin da mai amfani da shafin na X ( @Tony08Anyika) ya rubuta.

Wani mai amfani da shafin na X, Big Solz (@BigSolzz), yayi tsokaci da yin tambayoyi, “ Wa ke shirya masu babura da ababen hawansu? Ta yaya suke samun alburusai, shin ba sa rasa alburusai? Ta yaya suke samun magunguna shima? Kai akwai hanyoyi da dama da ya kamata a bibiye su amma gwamnati na kyalesu, a kare iyaka yanzu.

Wani ma da ke nuna tasa kulawar  Sammy Mills (@agbaje_sammy), yayi tambaya ne da cewa “Shin ta wace hanya ce ake samarwa baburansu fetir?”

Ganin yadda wannan wallafa ta yadu ga barazanar tsaro a Najeriya ya zama dole a tantance wannan da’awa.

Tantancewa

Mun nazarci bidiyon ta hanyar amfani da manhajar InVid, 

 Mun dauko wasu bangarori na bidiyon don gudanar da bincike a kansu sai muka lura cewa an wallafa wannan bidiyo tun a ranar 13 ga watan Yuni,2026 wanda kafar yada labarai ta Jeune Afrique, da ke Paris wacce ke ba da labari kan abubuwan da suka shafi Afurka da ake ganin irin labaransu daga Mali da yankin Sahel.

Taken labarin a harshen Faransanci shine, “Du Mali au Nigeria: le nouvel arc de crise et les fragmentations à venir dans le Sahel.”

Wanda idan aka fassara zuwa Hausa zai zama, “Daga Mali zuwa Najeriya: sabon yanayi na tashin hankalin dama zuwan rarrabuwa a yankin Sahel.”

Rahoton yayi karin haske ne kan yawaitar matsalar tsaro a yankin na Sahel da Afurka ta Yamma dama karin tasiri na Jama’at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM), kungiyar ‘yanta’adda mai alaka da  Al-Ka’ida wacce ke gudanar da ayyukanta a yankin Afurka ta Tsakiya da Arewacin Mali da sauran kasashe makota.

Ganin yadda ‘yanta’addar na JNIM ke gudanar da ayyukansu ta hanyar amfani da babura gwamnatin Mali ta kara tsaurara matakan tsaro.

A nata martani a ranar 4 ga watan Yuni,2026, kafar yada labarai ta Afrikinfos Mali ta ba da rahoto  cewa gwamnatin Mali da ke samun jagorancin sojoji ta haramta shigar da mashi ko siyarwa ko rarraba shi muddin yana da karfin inji da ya kai ko ya haura 125 cc a wajen biranen kasar manya.

Wannan sharadi da aka sanya ya jawo raguwar motsin kungiyoyi masu dauke da bindigu irinsu JNIM kamar yadda ake ganin kai kawonsu ana kai hare-hare.  

Sake nazari kan bidiyon ya nunar da cewa wanda ke maganar na magana ne da harshen Bambara daya daga manyan harsuna da ake amfani da su a kasar ta Mali. Wannan kungiya kuma ta JNIM ce. Bayanan muryar an fassara su daga Bambara zuwa Turanci ta hanyar amfani da Gemini, ga kuma fassara zuwa Hausa:

“Ko a kan babura ko manyan motoci ko kananan motoci ko mutane ya kamata mu duba, duk mai tuka abin hawa ko mai tafiya, idan Allah SWT ya nuna ma alama ya kamata a duba babura ne ko mota, dole a tafi a hankali a duba komai, kasa ta Allah ce.”

“Dole mu tsaya a ko’ina, a manyan garuruwa da kananan kauyika; da unguwanni da ko’ina, idan Allah bai so abu ya faru ba ba abin da zai faru.Kowa ya tafi a hankali kada ya kade mutane ko yayi wa kansa illa. Mu tsayar da motocinmu.” 

Duka a cikin wannan jawabi babu inda aka ga wata barazana sabanin abin da mai da’awar ke fadi.

A Karshe

Asalin bidiyon ya fito ne daga Mali babu wata alamar barazanar tsaro a ciki kamar yadda aka yi da’awa. Abin da mai da’awar ke fadi ba makawa ba shine abin da ke cikin bidiyon ba, yayi rubutu ne a kansa wanda ba haka yake ba. Don haka da’awar karya ce.

Wannan aiki an aiwatar da shi karkashin cibiyar koyon Aikin Jarida da Kirkire-kirkire da Ci gaba (CJID) tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai.

Exit mobile version