Site icon Dubawa

Bidiyon da aka nuna karamin yaro yana kokarin tashin mahaifiyarsa bayan ta mutu ba a Najeriya ba ne a Sudan ne

Video of child with dead mother from Sudan, not Nigeria

,

Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook Evang Peter Otene, ya yada wani bidiyoinda yayi da’awar cewa wani yaro na kokarin ya tashi mahaifiyarsa bayan kuwa ‘yanta’adda sun halaka ta a Najeriya.

Bidiyon da aka nuna karamin yaro yana kokarin tashin mahaifiyarsa bayan ta mutu ba a Najeriya ba ne a Sudan ne

Hukunci: Yaudara ce. Shedu da aka tattara sun nunar da cewa wannan bidiyo ya dade ana ganinsa a shafukan intanet kafin daga bisani aka yi karyar alakanta shi da Najeriya. Wallafa da dama da aka yi a ranar 27 ga watan Yuli, 2026 ta nuna cewa wannan bidiyo na da alaka da tashin hankali da ake fama da shi a Sudan. 

DUBAWA ba ta ga wata sheda ba da ta nuna alakar wannan bidiyo da harin ta’addanci a Najeriya.

Cikakken Labari

A ranar 29 ga watan Yuli, 2026 wani shafin Facebook mai suna Evang Peter Otene, ya yada a wani bidiyo kamar yadda aka alkinta shi a nan inda aka yi da’awar cewa wani yaro na kokarin ya ga ya tashi mahaifiyarsa ba tare da sanin cewa ita ta riga ta mutu ba. Wannan da’awar ta kara da cewa ‘yan’adda ne suka halaka masa mahaifiya a Najeriya.

Ya zuwa ranar 30 ga watan Yuli, 2026, wannan wallafa ta samu martani 1,000 da tsokaci 367 da wadanda suka sake yadawa 597 da mutane 57 da suka nuna alama ta cewa za su sake nazarta ko kalla inda mutane da dama suka rika nuna alhini. 

Frederick Akor Ocheme ya rubuta cewa, “Abin tashin hankali.”

Adekunle Taiwo Olakunle yayi tsokaci da cewa, “Duk wanda ke da hannu, a wannan aikin ta’addanci a Najeriya karshen rayuwarsa ba zai yi kyau ba.”

Nelson Kampeligi ya rubuta cewa “Ta yaya mutum zai yi wannan mummunan aiki yace da sunan Allah yake yi?”

Anagbogu Valentine Chigbogu ta yi martani da cewa“… Wayyo Allah wannan abun yayi yawa,…Akwai bukatar a fito a yi magana.”

Duba da yadda ake ta kalamai masu motsa zuciya abin da kuma ke iya harzuka zukata, DUBAWA ta ga wajibcin gudanar da bincike don tabbatar da sahihanci na abin da ke faruwa.

Tantancewa

DUBAWA ta tsakuro wasu sassa na bidiyon don aikin tantance su ta hanyar gano asalin bidiyo a manhajar Google.

Binciken ya nunar da cewa wannan tarin bidiyo da suke nunawa sun fito ne daga Sudan ba wai daga Najeriya ba.

Daya cikin wallafar da aka fara ganowa wallafa ce a shafin X na Typical African (@Joe__Bassey), ya wallafa a ranar 27 ga watan Yuli,2026 tare da taken: “Halin da ake ciki a Sudan abin tausayawa ne.”

Wani mai amfani da shafin na X, a ranar 28 ga watan Yuli,2026  @jowleenwood ya sake yada wallafar da aka yi a ranar 27 ga watan na Yuli, 2026 kuma @jowleenwood yace lamarun ya faru ne a Sudan ba a Najeriya ba.

Haka shima, @ABO_Watan9 ya yada irin wannan bidiyo a ranar 28 ga watan na Yuli,2026 inda yake addu’a ga kasar Sudan.

Da aka zurfafa da bincike a shafin YouTube ya dai sake nunar da alakar bidiyon da kasar ta Sudan.

A wannan rana dai ta 27 ga watan Yuli,2026 wani shafin Instagram @afroenergyworld ya yada hoton da aka dauko daga wannan bidiyo inda aka yi masa taken:”Labari da Dumi-dumi: Sojoji da ke samun goyon bayan Daular Larabawa ta UAE sun halaka wata uwar yaro dan shekara daya.”  

Wannan wallafa an hada ta da bayanai masu sadara hudu, wadanda suka ce lamarin ya faru ne a Sudan inda aka halaka uwa a gaban danta mai shekara daya a fadan da ake yi da dakarun RSF.

Domin tantance da’awar DUBAWA ta duba a shafin Google da wadannan kalmomi da aka sa a Instagram, wannan ya kaimu ga wallafar da aka yi a ranar 27 ga watan Yuli,2026 wanda Ajak-Kuac TV, ta wallafa, da aka kuma bincika an gano shafin na Facebook a kasar Sudan ne. 

Wannan shafi dai ya sake yada wani bidiyon da taken: An kashe mahaifiya a gaban danta yayin wata taho mu gama tsakanin dakarun SAF da na RSF a fafatawar da aka yi a Kordofan.” 

Wadannan wallafai an yi su tun kafin ma mai da’awar ya fitar da tasa, kuma duka nasu ya nunar da cewa lamarin ya faru ne a Sudan.

DUBAWA ta gaza gano wani rahoto daga wata kafar yada labarai sahihiya ko wasu bayanai da aka tattara na jinkai ko wani jawabi daga bangaren gwamnati da ya nuna wannan bidiyo da cewa ‘yanta’adda ne suka kai hari a Najeriya.

Duk da cewa wannan bidiyo ba za a ce ga asalin inda ya fito ba, ko ga dalilin samar da shi kai tsaye, bayanai da aka tattara sun nunar da cewa wannan bidiyo na da alaka da rikicin Sudan ba na Najeriya ba.

A karshe

Da’awar da aka fitar cewa yaro karami na kokari ya tashi mahaifiyarsa bayan kai harin ta’addanci a Najeriya ya kashe ta a Najeriya, wannan yaudara ce.

DUBAWA ta gano cewa wannan bidiyo  da aka wallafa a karo da dama na da alaka da rikicin da ke faruwa a Sudan musamman a rikicin da ake fafatawa tsakanin dakarun na (SAF) da na (RSF).

Wannan aiki an aiwatar da shi karkashin cibiyar koyon Aikin Jarida da Kirkire-kirkire da Ci gaba (CJID) da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai.

Exit mobile version