Site icon Dubawa

Bidiyon da aka nuna ‘yan ta’adda sun mamaye kasuwa a Zamfara yaudara ce

Video used to depict bandits surrounding Zamfara market, misleading

.

Da’awa: Wani mai amfani da shafin X ya wallafa wani bidiyo, inda yayi zargin cewa ‘yanbindiga sun mamaye wata kasuwa a jihar Zamfara bayan da ‘yanbijilanti suka kai farmaki ga wani mamba na ‘yan bindigar.

Bidiyon da aka nuna ‘yan ta’adda sun mamaye kasuwa a Zamfara yaudara ce

    Hukunci: Karya ce! DUBAWA ta gano cewa babu wata sheda da ta nuna cewa wannan lamari ya faru a jihar Zamfara. Irin wannan bidiyo an yada shi a wasu kafafen a shafukan intanet da taken labarai kala-kala.

    Cikakken Labari

    Wata mai amfani da shafin X, chi… (@nnamanichi93717), ta yada wannan bidiyo (kamar yadda aka alkinta nan) bisa da’awar cewa ‘yanta’adda sun zagaye kasuwa bayan abin da ya faru da ake zargin cewa ‘yanbijilanti sun kashe daya daga cikinsu.

    Wannan bidiyo an wallafa shi a ranar 10 ga watan Yuni, 2026: “Yanzu-yanzu; ‘yanbindiga sun zagaye kasuwa a jihar Zamfara bayan da ‘yankato da gora ko bijilanti suka kashe wani mamba nasu.’’

    A bidiyon an nuna yadda mutane suke ta guje-guje ba tare da sanin ina za su je ba, abin da ya jawo sanya tsoro da kawo rudani a wannan yanki.

    Ya zuwa ranar 21 ga watan Yuni, 2026 wannan wallafa ta samu masu kallo(views) 5,400 da wadanda suka sake yadawa (repost) 32 da wadanda suka nuna sha’awa (likes) 63, wannan ya jawo martani kala-kala wadanda suke cin karo da juna.

    Yayin da wasu suke nuna amincewarsu da labarin wasu kuwa na taka tsantsan a dangane da sahihancinsa.

    Wani mai amfani da shafin X Tugis Art Studio (@tugisart),yayi tsokaci kan mutanen da ke guje-guje da cewa, duk da damar da suke da ita su ja daga idan suna dauke da makamai.

    Haka shima, OmoBenDel (@omobendel_)ya ba da shawara cewa ba da horo da kananan makamai ga matasa da ke zaune a yankuna zai taimaka wajen dakile duk wata barazana.

    ”Bara su yi wa ‘yanta’addar kwantan bauna ka ga yadda za su kawar da ‘yanta’addar.” a cewarsa.

    Shi kuwa mai wannan shafi(@yoursdesirously) ya sanya alamar tambaya ne a dangane da sahihancin bidiyon. 

    “Shi mai daukar bidiyon baya mutuwa ne?” Wani mai amfani da shafin CITY (@Dr_Dindu), shima ya sanya alamar tambaya ne da cewa shi mai daukar bidiyon ba zai iya fuskantar barazanar harbi ba? Ya dauki yanayi irin wannan mai rudani.

    DUBAWA ta kuma gano wani bidiyon shima da irin wannan da’awa a shafin na X

    Duba da irin martani da ake a shafin tsokaci da irin matsala da ake fuskanta ta fuskar tsaro DUBAWA ta ga wajibcin gudanar da bincike kan wannan lamari.

    Tantancewa

    DUBAWA ta bibiyi wannan bidiyo filla-filla, ta lura da cewa shi mai daukar bidiyon ya ci gaba da daukar hoton bidiyo ba tare yayi kokarin kaucewa samun harbi ba don tsira da ransa. 

    Idan har da gaske ne ‘yanbindiga sun zagaye kasuwar da shima mai daukar hoton da ya rika gudun tsira da ransa.

    Idan aka kalli bidiyon a tsanaki babu inda aka ga alamun ‘yanbindigar. DUBAWA ta kuma lura da harshen da ake magana a cikin bidiyon duk da cewa maganar ba ta fita amma da alama ba Hausa ba ce ko Fulfulde.

    Duba da rashin tafiyar bidiyon adaidai mun yanke shawarar sake nazari ko wannan bidiyo an hada shine ta hanyar amfani da kirkirarriyar basira ta AI.

    Mun binciki bidiyon ta hanyar amfani da  ISFAKEAI, wanda ya nuna cewa kaso 46% na bidiyon da manhajar AI aka yi shi.

    Exit mobile version