Site icon Dubawa

Bidiyon da aka yi amfani da shi wajen nuna harin ISWAP a Sokoto yaudara ce kawai

Misleading video used to depict ISWAP attack in Sokoto

Mambobin ISWAP Asalin hoton: ICIR.

Da’awa:  Mai amfani da shafin X @biafra_newsUSB ya wallafa bidiyo ya na da’awar wai kungiyar ISWAP ta yi amfani da yara mazan da ba su kai shekaru 15 na haihuwa ba wajen kai hari kan sansanin sojoji a Sokoto.

Bidiyon da aka yi amfani da shi wajen nuna harin ISWAP a Sokoto yaudara ce kawai

Hukunci: Karya ce! Bincikenmu ya nuna mana cewa bidyon ya dade, tun shekarar 2025 ya ke shafukan sada zumunta kuma an dade ana amfani da shi wajen yada bayanan karya a lokuta daban-daban.

Cikakken bayani

Najeriya na cigaba da fama da matsalar rashin tsaro, musamman a yankin arewacin kasar, inda hare-hare daha kungiyoyi irin su ISWAP suka shafe shekaru su na addaban al’ummomin da ke yankin. ‘Yan ta’adda sun kai hare-hare da dama kan sansaninin sojoji. Wani harin da ake dangantawa da ISWAP wanda ya afku kwanan nan a wani sansanin sojoji a Borno, ya kai ga hallakar sojoji da dama.

Bisa la’akari da wannan bayanin ne, wani shafi a X mai suna Biafra News & World News (@biafra_newsUSB)  ya  wallafa (kuna iya gani a nan) ya na da’awar wai ‘yan ta’addan ISWAP sun yi amfani da ‘yan maza masu shekaru 15 na haihuwa wajen kai hari kan sansanin sojoji a Sokoto.

Duk da cewa ba’a iya ganin hoton bidiyon da kyau, ana iya ganin wasu ‘yan samari suna harbin kan mai uwa da wabi kan wani gini. Kyamarar ta kuma gwado wadansu daban wadanda su kuma suke dauke da manyan bindigogi yayin da wasu kuma su ke kan babura. Da kyar ake jin sautin maganar wadanda ke cikin bidiyon, amma ana iya jin mai daukar hoton ya na cewa “Allahu Akbar”

Daga ranar Juma’a 19 ga watan Yunin 2026, mutane sama da 6,114 suka kalli bidiyon. An sake rabawa sau 8, sa’annan da alamar like 31. Sai dai kuma martanonin da aka maida dangane da batun sun nuna ra’ayoyi mabanbanta.

Wani mai amfani da shafin X, Controversial Adult (@CntrvslAult), wanda ya yi tsokaci a kan batun, kai tsaye ya karyata sahihancin da’awar,  da cewa, “Sai ku yi ta karya kawai. Wannan ba ma Najeriya ba ne.”

To sai dai akwai masu amfani da shafin da suka yi imanin cewa lallai ISWAP ta kai hari kan sansanin na Sokoto.

Wani mai amfani da shafin na X, Khal Drogo (@mayokun_olonade), ya yarda da batun, da cewa, “Idan har ‘yan bindiga na iya kai hari kan sansanin sojoji ba tare da wani fargaba ko tsoro ba, ke nan babu mafaka wa ‘yan kasa irin mu.”

Wani shi ma mai amfani da shafin, Sof (@PSofiyah3963 ), ya ce,     

“Mun gama yawo a kasar nan. Ina sojojin su ke sadda aka kai hari kan sansanin na su. Su na bacci ne??”

Ganin yadda aka sami ra’ayoyi mabanbanta da ma sarkakiyar da da’awa irin wannan ke da shi ya sa DUBAWA tantance gaskiya.

Tantancewa

DUBAWA eta fara da tantance mahimman hotuna cikin InVID kafin mu ka sa cikin google reverse search dan gano mafarin hoton.

Wannan binciken ne ya kai mu ga wani labarin da aka wallafa a shafin X cikin watan Afrilun 2025 inda aka kwatanta bidiyon a matsayin fursunonin da ke kokarin kubucewa a Chadi.

Mun fassara taken kamar haka: “Chadi: Fursunoni fiye da dari sun kubuce daga wani babban kurkukun da ke birnin Mongo da ke Chadi. Fursunonin sun shiga ofishin mahukuntan ne sun kwace makamansu. Mutane uku sun hallaka yayin da wasu uku kuma suka yi rauni a cikinsu har da gwamnan yankin.”

Binciken da muka cigaba da yi nuna mana kafofin yada labaran da suka yi rahoto dangane da batun na kurkukun Mongo a Chadi. To sai dai an riga an wallafa bidiyon a shafukan Face wata daya kafin nan a watan Maris na shekarar 2025, su ma suna dauke da take daban daban masu da’awar harin ‘yan ta’adda a jihohin  Borno da Zamfara

Binciken DUBAWA ya kuma gano wani labarin shi ma da aka wallafa a shafin  X ranar 7 ga watan Yunin 2026, inda nan ma aka yi amfani da wannan bidiyon ana da’awar wai ISWAP ce ta yi amfani da matasa wajen kai hari a wani sansanin sojojin da ke Jamhuriyar Nijar. Ko da shi ke da muka nemi ko labarin ya bulla cikin rahotannin baya-bayan nan dangane da irin wannan harin ba mu sami komai ba.

Dan dai samun tabbaci DUBAWA ta sake bincika labaran baya-bayan nan dangane da ko ISWAP ta kai hari wani sansani a Sokoto inda nan ma ba’a sami wani labari mai sahihanci ba.

A waje guda kuma, binciken ya kai mu ga wasu rahotannin da aka wallafa a shafukan ICIR da TheCable a watan Satumban 2021, dangane da harin ‘yan ta’adda kan sansanin sojoji a Sokoto. Sai dai  wadannan rahotannin suna da alaka da wani harin da ya faru shekaru hudun da suka gabata ne basu da dangantaka da wannan sabuwar da’awar..

DUBAWA ta kuma duba kafofin sadarwar  Hedikwatar Rundunar Sojojin Najeriya , amma kamar sauran sakamakon binciken na mu, can ma babu wani rahoton da ya tabbatar da harin ISWAP kan wani sansani a Sokoto.

A Karshe

Bincikenmu ya nuna cewa tsohon bidiyo ne wanda aka yi amfani da shi sau da yawa a kafofin sada zumunta wajen yada labaran karya kan Najeriya da sauran kasashe da dama. Babu wasu hujjoji masu sahihancin da suka tabbatar wai ISWAP ta yi amfani da matasa masu shekaru 15 wajen kai hari kan sansanin sojoji a Sokoto. Dan haka karya ne kawai.

Wannan aiki an aiwatar da shi karkashin Cibiyar koyon Aikin Jarida da Kirkire-kirkire da Ci gaba (CJID) tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai.   

Exit mobile version