Bidiyon da ke da’awar sojoji sun lalata gonakin jama’a a 2021 ya sake bullowa.

2021 video of alleged soldiers destroying farmland resurfaces
Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani a shafinsa na X ya wallafa bidiyo da ya nuna yadda wasu sojojin Najeriya ke lalata gonakin mutane bayan mutane sun tunkari wani Fulani makiyaya bayan dabobbin sun sun yi barna a gonakin mutnane wanda hakan ke nuna cewa sojojin na kare “Fulani ‘yan ta’adda” 

Hukunci: karya ce! Bidiyon an dauke sa tun a shekarar 2021 sannan rundunar sojin Najeriya ta karyata aiyukkan da bidiyon ya nuna ma’aikatanta na yi.

Cikakken Labari.

A ranar 2 ga Adusta 2026 wani Daniel Somtochukwu a shafinsa na X (@Somtolism7) ya wallafa wani bidiyo da ya nuna an lalata shukan da aka yi a wasu gonaki sannan bidiyon ya dora alhalin haka wa dakarun rundunar sojin Najeriya.

Da’awar ya nuna cewa “An ga Sojojin Najeriya a lokacin da suke lalata shukan dake gonakin mutane sannan hakan ya faru ne bayan mutanen sun tunkari Fulanin da suka kora dabobbin su cikin gonakin mutanen. Wannan ba yana nuna yadda sojojin Najeriya ke kare Fulani ‘yan ta’adda bane?

Zuwa ranar 4 ga Agusta da’awa da aka saka a nan mutum 24,000 sun duba, 115 sun mai da martani, 921 sun mai da martani da 793 na son da’awar.

Da’awar ya jawo ce-ce-ku-ce musamman ta fannin kabilanci da rashin amincewa da hukumomi inda wadanda suka martani ke cewa bidiyon ya nuna cewa sojoji na kare Fulani makiyaya.

“Ku sani, sojojin Najeriya makiyan ku ne, ‘yan sanda makiyan ku ne” wani @DerealCEO ya rubuta. Wannan rubutu da ya yi mutum 741 sun mai da martani a kai.

“Wannan shine runduar sojin Najeriya kuma suna bukatan Kudu maso Gabas su shiga ciki ne” @greasedbygrace ta tambaya.

“Ga dukkan alamu rundunar sojin Najeriya sun zama makami a hannun Fulani makiyaya  @Dika_scorch ya ce.

“Sojoji na basu kariya” @GeraldUkperu ya rubuta.

@Somtolism7 wanda ya fara saka da’awar a shafinsa ya yi gargadin cewa ba kowani lokaci bane idan an ga mutane sanye da kayan sojoji suke zama sojojin gaske ba. “Sai dai wadannan sojojin Najeriya ne bisa ga rahotan”.

DUBAWA ganin yadda da’awar ya ja hankalin mutane da yadda zai iya canza ra’ayin mutane kan amincewar su da sojojin Najeriya da tada hankalin mutane musamman ta fannin kabilanci ya sa ta gudanar da bincike.

Tantancewa 

Mun gudanar da bincike ta hanyar amfani da ‘Reverse Image’ da ‘Keyword Searches’ domin gano asalin inda aka samu bidiyon.

Sakamakon binciken ya nuna cewa an saka bidiyon a shekarar 2021 a Facebook sannan Biafra News App da sake wallafa bidiyon. Hakan ya nuna cewa bidiyon ya yi shekaru yana shawagi a yanar gizo kafin @Somtolism7 ya saka a shafinsa. 

Bidiyon ya yi daidai da wani bidiyo da ya kareda yanar gizo a watan Yuli 2021 inda ya nuna wasu mutane dake sanye da kayan sojoji na lalata gonakin mutane a wani wuri. An wallafa bidiyon domin nuna aiyukkan da sojojin Najeriya ke yi.

Rundunar sojin Najeriya ta musanta haka kamar yadda gidajen jaridu da suka hada da (TVC News, Vanguard, The ICIR, da The Guardian) suka rawaito.

Rundunar sojin najeriya ta alakanta bidiyon cewa kage kawai kungiyar ‘Eastern Security Network (ESN)’ ke kokarin yi da gangar domin bata mata suna musamman yadda ake kokarin nuna dakarun sojin Najeriya a matsayin makiyan mutane.

Sai dai kuma duk da musun aikata hakan da rundunar sojin Najeriya ta yi a 2021 an sake wallafa bidiyon a 2025 in wani Chinasa (@chinasanworu) a shafin sa na X ya saka bidiyon sannan bodiyon ya sake bullowa a 2026 inda @Somtolism7 ya saka a shafinsa.

Sakamakon binciken da gidan jarida ta gudanar ya nuna cewa babu bidiyon da ya tabbatar cewa sojoji sun aikata wannan aikin aika-aikan a watan Agusta 2026 ko wani bayani da rundunar sojin Najeriya, Hedikwatan tsaro DHQ, ko wata runduran tsaro suka yi game da biyoin a wannan shekara.

A Karshe 

Bidiyon da @Somtolism7 ya saka a shafinsa ba sabon bidiyo bane domin binciken da aka gudanar ya nuna cewa an dauki wannan bidiyo tun a shekarar 2021sannan rundunar sojin Najeriya ta musanta cewa ma’aikatan ta ne a bidiyon.

Wannan aiki an aiwatar da shi karkashin Cibiyar koyon Aikin Jarida da Kirkire-kirkire da Ci gaba (CJID) tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai.