Da’awa: Mai amfani da shafin Facebook na da’awar wai wasu sojoji sun kama wata motar da ke tafiya daga jihar Binuwai za ta Kwara makare da makamai a cikin wani akwatin gawa.

Hukunci: Karya ce. Bidiyon bai nuna wani binciken sojoji bakuma hujjojin da DUBAWA ta tara sun nuna cewa AI aka yi amfani da shi wajen kirkiro bidiyon.
Cikakken bayani
Da’awar safara ko kuma kama makamai da kayan yaki yawanci ya kan dauki hankali sosai musamman a shafukan sada zumunta na soshiyal mediya saboda ya kan tabo abubuwan da yawancin ‘yan Najeriya suka fi damuwa a kai.
Kwanan nan wani mai amfani da shafin Facebook ya yi da’awar cewa sojoji sun kama wata motar da ta fito daga jihar Kwara (kamar yadda aka adana a nan) tmakare da makamai da albarusai wadanda aka boye cikin wani akwatin gawa, a sunan wai gawar ce a ciki.
Taken da aka yi wa labarin na cewa “Mota guda a kan hanyarta ta zuwa jihar Kwara daga Binuwai a sunan za’a jana’iza sojoji suka kama. Dubi abin da suka gano a ciki.”
Bayan duba bidiyon, DUBAWA ta ga wasu mutane sanye da kayan soja suna kokarin bude akwatin gawar, kuma bayan da suka ajiye suka bude sai aka ga makamai a maimakon gawa kamar yadda aka zata.
Can gaba a cikin bidiyon, an nuna wasu mutane duk sun mika kai ga sojojin bisa yadda aka nuna su a sunkuye a bayan motar da aka tsayar lokacin binciken.
Daga 24 ga watan Yunin 2026, ya sami alamar like sama da 800, akwai tsokaci 114 an raba sau 894 sa’annan an kalla sau 7000
DUBAWa ta duba wasu daga cikin tsokace-tsokacen da aka yi dan jin ra’ayoyin wadanda suka yi ma’amala da labarin.
Wani mai amfani da shafin, @Adebayo Oldipupo, ya yi martani kamar haka, “Na jinjinawa rundunar sojojin Najeriya.”
Ra’ayin @Lateef Abudu, kuwa ya sabawa haka inda ya ce, “Wannan tsohon labari ne. Shekaru 10 da suka gabata aka yi batun.”
@Bala Sani, shi ma ya musunta sahihancin batun, “ Ba su yi kama da sojojin Najeriya ba ma.”
Mutane da dama sun raba wannan da’awar a wadannan shafukan, wato nan, nan, nan, nan nan, nan, nan, da nan.
Ganin yadda irin wannan labarin zai iya kasancewa babban barazana ga tsaro ya ma harzuka jama’a ya sa ne DUBAWA ta dauki nauyin tantance gaskiyar batun.
Tantancewa
DUBAWA ta fara sanya bidiyon cikin manhajar tantance hotunan bidiyo na InVID dan cire mahimman hotuna. Da wadannan mahimman hotunan ne ta yi amfani da manhajar google na gano mafarin hotuna wato google reverse search. Sai dai binciken bai nuna cewa an taba amfani da hoton a wani wuri ba in banda wannan sabon da’awar.
Binciken da muka yi a kafofin yada labarai masu nagarta dan ganin ko akwai wani labarin dangane da motar makaman da aka kama bai haifar da da mai ido ba. Babu labarin motar da ta taso daga Kwara za ta Binuwai.
Da aka sake duba bidiyon yadda ya kamata, sai DUBAWA ta gano kura-kurai da dama. Yadda mutanen cikin bidiyon ke tafiya, musamman wadanda ke sanye da kayan sojojin bai yi kama da yadda dan adam zai yi ba. Haka nan ma ko yadda aka ajiye akwatin gawar ba’a yi shi kamar yadda ya kamata a yi idan da dan adam ya yi ba, dan haka duk hotunan sun fi kama da irin wadanda ake kirkirowa da fasahar AI.
Domin tabbatar da wannan hasashen sai muka sake dora bidiyon cikin manhajar tantance ko AI aka yi amfani da shi wato Hive.ai, wanda ya nuna mana cewa akwai yiwuwar an yi amfani da AI din ne da wajen kashi 95.6 cikin 100.

sakamakon Hive.ai
Mun kuma yi nazarin bidiyon da manhajar Deepware.ai, wanda tun da farko ya yi shakkar sahihancin bidiyon. Inda shakkun ya nuna kashi 73%, da 51% cikin 100.

sakamakon Deepware.ai.
Mun kuma sake gudanar da binciken da Zhuque AI Detection Assistant. Shi wannan ya nuna kashi 86.01% cikin 100 wanda ya nuna mana cewa tabbas da AI aka kirkiro bidiyon.

A Karshe
Binciken DUBAWA ya nuna cewa AI aka yi amfani da shi wajen kirkiro bidiyon haka nan kuma duk binciken da muka yi ba mu gano wasu kwararan hujjojin da za su tabbatar da afkuwan wannan lamarin na sojojin da suka kama masu safarar makamaki cikin akwatin gawa ba.