Site icon Dubawa

Bidiyon da ke da’awar wai mahara ne ke dafa naman mutane ba gaskiya ba ne

Viral video of bandits cooking human flesh, misleading

Da’awa: Wasu a shafukan sada zumuntanda suka hada da Facebook, X da Instagram sun wallafa wani bidiyon da ke da’awar wai wasu ‘yan bindiga ke dafa naman mutane kuma fararen hula ne wadanda suka yi garkuwa da su.

Bidiyon da ke da'awar wai mahara ne ke dafa naman mutane ba gaskiya ba ne

Hukunci: Yaudara ce kawai! DUBAWA ta gano cewa bidiyon bai nuna yadda mahara ke dafa naman mutane ba. Ainihin bidiyon an dauke sa ne yayin da wasu Fulani ke taron bukin daurin aure  a karamar hukumar Shongom dake jihar Gombe.  

Viral video of bandits cooking human flesh, misleading

Cikakken bayani

Bidiyon ya nuna yadda wasu maza ke dafa abinci a manyan tukwane a wani fili. Bidiyon dai ya yadu a shafukan sada zumunta na yanar gizo musamman FacebookX da Instagram da da’awar cewa ‘yan bindiga na dafa naman mutane.

Wasu da’awar da gidan jaridar ta gani sun nuna yadda ‘yan bindiga ke dafa naman mutum wasu sun nuna cewa nan na mutane ‘yan farin hula da maharani suka yi garkuwa da su.

@pcfjbl a shafinsa na X ya rubuta cewa cewa ya ga bidiyon yadda mahara ke dafa naman mutane a manyan tukwane  bakwai a Tiki Tok.

Zuwa ranar Litini 20 ga Yuli 2026 da’awar ya samu mutum 80,200 sun duba, 190 sun sakew wallafawa, 960 sun nuna alamar so, 868 sun saka Alamar bookmark da mutum 90 da suka kara mai da martani. Bidiyon ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin mutane inda wasu sun amince sannan wasu na bukatan tabbatar da ingancin bidiyon.

Misali Ade(@Ade_Lee19)ya rubuta cewa “Wanen eke biyan mutane suna shafawa Najeriyab akin fenti? Ta yaya aka sani cewa naman mutum ne? yaya aka sani cewa mutanen ‘yan bindiga ne? akwai hujojjin da suka tabbatar da haka?

Wani geeked Rick (@badboyriick) shima ya ki amincewa da bidiyon inda yake cewa akwai hujjan da ya tabbatar cewa naman na mutane ne?

Daga nan Sabc Six ya wallafa bidiyon da da’awar cewa ‘Yadda mahara ke dafa naman mutum a Najeriya. Ba za mu taba hada kan mu da su ba su nemi wasu.

PAN AFRICASTS ba za su amince da haka ba balle har mu haka kai da su. Bazai taba yiwu ba. Gwamnati ta kasa shawo jan matsaloli irin haka sanan ana bukatan mu hada kai da su  ‘AFRIKA DAYA’.

Ojong Oyingha ya wallafa bidiyon a shafin s ana Facebook da da’awar “Yana faruwa yanzu haka a Najeriya. Da ni da ke muna da masaniyar abin da mahara irin haka ke girkawa domin ba naman sa bane ko na wani dabba da ake cewa suna cin naman mutanen da suka yi garkuwa da su.

Vgeeked RICK (@irality) da yadda bibiyon ke ci gaba da kareda kafaffen sada zuminta nay ana gizo ya sa DUBAWA gudanar da bincike domin tabbatar da ingancin bidiyon.

Tantancewa

Sakamakon binciken da Dubawa ta gudanar game da bidiyon ya nuna cewa maza ne suka taru gaban wasu manyan tukwanen dake kan wuta ana girka abinci a fili wanda hakan ke kama da yadda mazauna karkara ke gudanar da aiyukkan su.

Bidiyon ya nuna yadda wasu suka ajiye baburan sun a hawa a gefe Yatin da sauran ke sauraron wakar hausa. Baya ga haka bidiyon bai nuna inda aka dauki bidiyon ba, bada bayanai kan mutanen dake cikin bidiyon da irin abincin da ake girkawa.

DUBAWA domin gano ainihin bidiyon ta yi amfani da ‘Reverse Image Searches’ dake amfani da GOOGLE Lens, Yandex Images da TinEye. Sakamakon da aka samu bai tabbatar da inda aka dauki bidiyon ba balle ya tabbatar da abin da mutanen ke girkawa.

DUBAWA ta gane bidiyon dake kareda kafafen X, Facebook da Instagram dake dauke da tambarin TicTok na wani @ahmadumuhammed463 inda DUBAWA ta gydanar da bincike a Tik Tok.

DUBAWA ta gano inda aka fara saka bidiyon a Shafin TikTok inda ta gano cewa bidiyon da aka fara sakawa baya dauke da da’awar cewa mahara na dafa namomin mutane.

DUBAWA domin karin haske ta nemi mai Shafin Tik Tok  Muhammad Ahmadu ( da aka fi sani da sunan Gombawa) ta lanbarsa ta Whatsapp da ya saka a shafinsa na Tik Tok inda yayin da ake tattaunawa da shi a wayar hannu inda ya tabbatar cewa abin da ake fada game da bidiyon karya ne.

Ahmadu ya ce wanda aka saka a nan an dauke sa ne yayin da ake wani bukin daurin auren Fulani  inda aka daura wa Kannan sa biyu maza aure  Adamu Musa da ahmadu Musa, da aka yi a kauyen Fandi dake Kara Lalaipido dake karamar hukumar Shongom a jihar Gombe.

Gombawa ya ce an yi daurin auren ranar Asabar 31 ga Janairu 2026 sannan bidiyoin an dauka yayin da ake bukin dafa abinci washe garin auren ranar daya ga Fabrairu 2026.

Muhammad Ahmadu ya bai wa DUBAWA bidiyo 17 da aka dauka lokacin bukin daurin auren.

Bidiyon da DUBAWA ta gani ya nuna yadda aka fara hidimomin yinin bikin daga yankan Shannu, dafa abinci da sauran hidimomin bukin.

Bidiyon dake kareda kafaffen sada zumunta na bukin ne amma bari daya ne na bidiyoyin da aka dauka a yinin bikin.

Gombawa ya yi takaicin yadda wasu masu amfani da kafafen sada zumunta na yara gizo suka canza abin da bidiyon ke nunawa musamman yadda bidiyon bai nuna yadda mutane ke karya doka ba.

DUBAWA ta gano cewa babu wani abu da ya alakanta mutanen dake bidiyon da ‘yan bindiga musamman yadda ba a ga rigunan sojoji ko makamai ba.

A Karshe

Da’awar dake nuna cewa mahara na dafa naman mutane yaudara ce.

DUBAWA ta gano cewa bidiyoin an dauke sa ne yayin da ake daurin auren gargajiya na Fulani da aka yi a Fandi dake Kara Lalaipido dake karamar hukumar Shongom a jihar Gombe ba a sansanin ‘yan bindiga ba.

Wannan aiki an aiwatar da shi karkashin Cibiyar koyon Aikin Jarida da Kirkire-kirkire da Ci gaba (CJID) tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai.

Exit mobile version