Da’awa: Mai amfani da shafin X, Crusader (@Armylucifer001), ya wallafa wani bidiyo ya na ikirarin cewa ‘yan bindiga sun fara koya wa matansu yadda ake amfani da bindigogi.

Hukunci: Karya ce! Bidiyon tsoho ne kuma ba shi da wata alaka da Najeriya. Rahotannin da muka samu a matsayin hujjoji duk sun danganta bidiyon da wani abin da ya faru a kasar Sudan a shekarar 2018.
Cikakken bayani
Wani mai amfani da shafin X da suna, The Crusader (@Armylucifer001), ya wallafa bidiyo (kuna iya ganin inda aka adana a wannan makalar) ya na da’awar cewa ‘yan bindiga yanzu har koya wa matansu yadda za su yi amfani da bindigogi suke yi, kuma ana iya jin sautin muryoyinsu cikin bidiyon yayin da suke koyar da matar ana ma iya ganin wata daga cikinsu ta na murmushi.
Taken da aka yi wa bidiyon na cewa, “‘Yan bindiga sun koya wa matansu amfani da bindigogi kirar AK-47.
Daga 13 ga watan Yulin 2026, mutane sama da 33,700 sun kalla ko kuma sun yi ma’amala da labarin, wasu 76 sun sa alamar like, 56 sun adana. Haka nan kuma an sake yada labarin a wasu shafukan inda a nan ma da dama suka yi ma’amala da batun kamar yadda za’a iya gani a shafukan X, Instagram daFacebook: nan, nan, da nan.
Akalakuta Tufa, a cikin tsokacin da ya yi ya karyata zargin. Alakuta ya ce, Mu ba fararen hula ba ne; mu bi dokoki. In kun yarda, ina girmama wannan dandalin a matsayin wani wurin gwaji, idan kun yarda masu kula da shafi ku rika tantance wasu bidiyoyin kafin ku wallafa su; hakan zai mutunta mu. Ya na iya kasancewa gaskiya amma wannan ba Najeriya ba ne.”
Yata McDonald, wata ita ma mai amfani da shafin cewa ta yi, “Matar dan bindiga mai goyon bayan mijin da ya yi nasara”
DUBAWA ta tantance wannan batun saboda nasabar da ya ke da shi da tsao da ma dai ganin yadda batun ya janyo ra’ayoyi mabanbanta.
Tantancewa
Dan tantance gaskiyar wannan da’awar, mun fara da binciken mahimman kalmomi amma ba mu ga labarin a kafofin yada labarai masu nagarta ba.
Mun tantance mahimman hotunan da muka dauka daga cikin bidiyon, wanda ya danganta mu da wani bidiyon da aka dauka a 2018 shekaru da dama kafin aka danganta bidiyon da wani abin da ya faru a Najeriya.
Binciken ya hada mu da labarin da aka wallafa a jaridar Sudan News (an adana makalar a nan) inda aka yi amfani da wannan bidiyon na wata mata tana rike da bindiga a tsakiyar rikicin da ake yi a Khartoum, babban birnin kasar Sudan ranar uku ga watan Maris na shekarar 2018.
An rubuta taken bidiyon cikin harshen larabci kamar haka, “.. ويتواصل مسلسل الفوضى في #السودان !” tare da fasarar da ke cewa, “Rudani ya cigaba a #Sudan!”
A watan Maris na shekarar 2018, Sudan ta yi fama da abin da aka kwatanta da ta’azarar rikicin siyasa da tattalin arziki sakamakon faduwar darajar takardun kudin kasar, wanda ya ninka farashin biredi sau uku abin da kuma ya kai ga zanga-zangar adawa da matakan tsuke bakin aljihu.
Karin binciken da muka yi ya kai mu shafin YouTube na @alhowshalsudani, inda shi ma ya wallafa bidiyon da taken “حتى النساء تعلمن ضرب السلاح في دارفور,” fassarar ita ce “hatta mata sun koyi yadda za su yi harbi da bindiga a Darfur na Sudan.
Ranar 5 ga watan Maris, 2018 aka wallafa bidiyon.
A Karshe
Bidiyon da aka yada a shafin soshiyal mediaya ba shi da alaka da Najeriya. Bidiyon daga wani abin da ya faru a watan Maris na shekarar 2018 ne a kasar Sudan. Dan haka da’awar yaudara ce kawai.