Site icon Dubawa

Bidiyon dakarun Amurka da ‘yan bindiga a Sokoto da fasahar AI aka kirkiro 

Video of US soldiers capturing bandits in Sokoto, AI-generated

Asalin hoton: Reuters

Da’awa: Wani mai amfani da shafin X na da’awar  wai dakarun Amurka sun kama ‘yan bindiga uku a jihar Sokoton Najeriya.

Bidiyon dakarun Amurka da ‘yan bindiga a Sokoto da fasahar AI aka kirkiro 

Hukunci: Karya ce. Nazari da binciken DUBAWA ya nuna cewa da fasahar da ke kwaikwayon dabi’un dan adam na AI ne aka kirkiro bidiyon. Babu wani bayani a hukumance da ce nuna cewa dakarun Amurka na aiki ko ma kama ‘yan bindiga a jihar Sokoto.

Cikakken bayani

Ranar alhamis 11 ga watan Yunin 2026 wani mai amfani da shafin X, AJ. (@AJSMILE911), ya wallafa bidiyon da ke nuna wasu mutane uku sun durkusa cikin wani filin da ya bushe, su na kuma kewaye da wasu sojojin da suka yi dammara cikin kayayyakin da suka yi kama da kayan sojojin Amurka. 

Taken da aka yi wa hoton shi ne, “labarai da dumi-dumi, tdakarun sojin Amurka wadanda su ke aiki a Sokoton Najeriya sun kama ‘yan bindiga uku wadanda a yanzu haka su roko suna neman ceto rayuwarsu.”

Bidiyon wanda za’a iya gani a nan ya janyo ra’ayoyi mabanbanta. 

Wani mai suna, teji (@mrteji_), ya yi maraba da wannan cigaban da ake da’awar an samu ”ya yi daidai a cigaba da yin haka.”

To sai dai akwai da yawa da suka musanta batun suka nuna amincewarsu da sahihancin bidiyon. 

Wani shi ma mai amfani da shafin, Harm (@harm3t), ya yi tababan kasancewar dakarun ketare a kasar, tare da tambaya kamar haka: “Yaushe dakarun Amurka suka zo Sokoto?” 

Daga 11 ga watan Yunin 2026, mutane sama da 16,000 sun kalli bidiyon wasu 38 sun sa like an yi tsokaci 28 a karkashi wasu 14 kumasun sake raba labarin.

Ganin yadda wannan batun ke da sarkakiya da ma yadda zai iya kai ga yaduwar labaran karyar da za su iya barazana ga ‘yancin cin gashin kan Najeriya da kawancen tsaron da ta kulla ya sa DUBAWA bin diddigin labarin.

Tantancewa

DUBAWA ta yi bitan hotunan bidiyon inda ta kula da wasu abubuwan da ba daidai ba wadanda suka nuna mata cewa bidiyon na bogi ne.

Na farko mun lura da yadda sojojin ke tsaye a cikin bidiyon, ko daya bai yi kama da yadda mutun zai tsaya ba. Su kan su ‘yan bindigan da ake da’awarsun kama, yanayin yadda suke motsi da sigar jikinsu ba su zo daidai da yadda ainihin siffar mutun ya ke ba.

Wannan ne ya sa DUBAWA yin amfani da manhajojin gano abubuwan da aka kirkiro da fasahar AI. 

Nazarin Hive AI  ya nuna cewa an yi wa hotunan gyara da manhajojin AI da kashi 76.8 cikin 100.

Bidiyon dakarun Amurka da ‘yan bindiga a Sokoto da fasahar AI aka kirkiro 

Hoton nazarin da Hive ta yi a kan bidiyon

Mun kuma sake yin amfani da wata manhajar da ke dago duk hotunan da aka kirkiro da AI mai suna ISFAKEAI, kuma wannan sakamakon shi ma ya nuna cewa an yi amfani da AI.

Manhajar ta nuna cewa kashi 88 cikin 100 na bidiyon da AI aka yi yayin da sautin kuma ke kan kashi 66.3 cikin 100. Wannan ya nuna mana cewa daga hoton har sautin duk da AI aka yi.

Bidiyon dakarun Amurka da ‘yan bindiga a Sokoto da fasahar AI aka kirkiro 

Hoton nazarin Isfakeai ta yi a kan bidiyon 

DUBAWA ta kuma yi binciken mahimman kalmomi dan ganin ko akwai wata sanarwa ko kuma labaran da aka tantance da ke bayanin ko akwai dakarun sojin Amurka a Sokoto. Ba mu sami wata kafa mai sahihanci ba, ko sanarwar daga hedikwatar tsaro ko ma sanarwa daga hedikwatar tsaron Amurka dangane da wani batu kamar haka.

Idan ba ku manta ba a baya Hedikwatar Tsaron Najeriya ta fito ta jaddada cewa sojojin Amurkan da ke Najeriya ba mayaka ba ne. 

A Karshe

Bidiyon da ke da’awar wai dakarun Amurka sun kama wasu ‘yan binduga a jihar Sokoto kirkirowa aka yi da fasahar AI. Dan haka wannan da’awar karya ce kawai.

“Cibiyar Habbakawa da Koyon Sabbin Dabarun Aikin Jarida (CJID) ke aiwatar da wannan horaswar ta musamman tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai.”

Exit mobile version