Site icon Dubawa

Bidiyon Fulani na wasa da wani makamin da Amurka ta harbo, a jihar Sokoto ne?

Inda makamin Amurka ya faɗa a Jabo da ke Sokoto. Hakkin Mallaka: BBC Hausa

Inda makamin Amurka ya faɗa a Jabo da ke Sokoto. Hakkin Mallaka: BBC Hausa

Da’awa: Bidiyo ya nuna wasu Fulani na wasa da wani makami ko sassan makami da Amurka ta harbo a jihar Sokoto.

Bidiyon Fulani na wasa da wani makamin da Amurka ta harbo, a jihar Sokoto ne?

Hukunci: Yaudara Ce. Bidiyon ba daga Sokoto yake ba, kuma shaidu sun nuna cewa sojojin Nijeriya sun kwashe tarkacen da aka samu a wurin da lamarin ya faru.

Cikakken bayani

A ‘yan kwanakin nan, wani bidiyo (an adana a nan)ya kara yawo a kafafen sada zumunta, musamman Facebook da WhatsApp, inda ake da’awar cewa wasu Fulani ne ke wasa da wani makami ko tarkacen makami da ake cewa Amurka ta harbo a jihar Sokoto.

Masu yada bidiyon na kokarin hada shi da batun harin da Amurka ta kawo a Najeriya inda ta ce ta jefa makamai akan ƴan ta’addan ISIS a yankin arewacin kasar.

Bidiyon da ake yadawa bai bayyana fili ko alamar wuri ba da ke nuna jihar Sokoto ne kai tsaye. Abin da ake gani a bidiyon shi ne wasu mutane suna wasa da wasu karafan abubuwa da ake ikirarin sassan makami ne. 

Zuwa ranar Litinin, an kalli bidiyo sau 13,000, inda ak yaɗa shi sau 77.

Saboda yaɗuwar bidiyon da kuma yadda mutane da dama suka aminta da bidiyon, DUBAWA ta bincika wannan batu domin tantance sahihancinsa.

Tantancewa

Rahotanni sun tabbatar da cewa Amurka ta kai hare-hare kan maboyar ƴan ta’adda a Nijeriya, kamar yadda Shugaba Donald Trump ya sanar a shafinsa na sada zumunta. 

Duk da cewa harin ya sauka a kan ƴan ta’adda a yankin karamar hukumar Tangaza da ke jihar Sokoto, to sai dai kuma harin da aka kai garin Jabo da ke ƙaramar hukumar Tambuwal ya sauka ne a wani fili da ke bayan wani asibiti da ke ƙauyen na Jabo.

A cikin bidiyon da aka yaɗa babu wata kalma ko bayani da ke nuna inda aka ɗauke shi, sai dai kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito, yankin Jabo ne kawai ake jama’a ke iya zuwa su gani yayin da yankin Tangaza ya ke cikin da haɗari.

Domin tantance wannan da’awa, lokacin da wasu ‘yan jarida suka kai ziyara zuwa daya daga cikin yankunan da ake ikirarin cewa lamarin ya faru a jihar Sokoto, sun tattauna da mazauna yankin, da wasu da suka ce sun shaida abin da ya faru a lokacin.

Bayanan da aka tattara sun nuna cewa, bayan wani lamari da ya shafi wasu tarkace da suka fado daga sama a yankin, dakarun Sojin Nijeriya da ke aikin tsaro a garin Jabo na karamar hukumar Tambuwal sun gaggauta kai dauki. 

Shaidu daga mazauna yankin sun tabbatar da cewa sojoji sun killace wurin nan take, sannan suka kwashe duk wasu abubuwa da ake ganin suna da alaka da lamarin.

Binciken DUBAWA ya kuma gano cewa wannan bidiyon ba AI ta kirkire shi ba, kamar yadda manhajar Hive AI ta tabbatar.

Bidiyon Fulani na wasa da wani makamin da Amurka ta harbo, a jihar Sokoto ne?

Sakamakon binciken bidiyon a manhajar Hive

Duk da cewa ba a tabbatar da takamaiman inda aka dauki bidiyon ba, babu wata hujja da ke danganta shi da jihar Sokoto ko da’awar da ake yi a kai.

A Karshe

DUBAWA ta tabbatar da cewa da’awar cewa bidiyon ya nuna wasu Fulani na wasa da makamin da Amurka ta harbo  ba a Sokoto ba ne.

Exit mobile version