Site icon Dubawa

Bidiyon Fulani ‘yan ta’adda na horasawa da kananan jirage marasa matuka na drones, tsoho ne

Viral video of Fulani terrorists training with drones, recycled

'Yan fashin daji a Najeriya. ASalin hoton: BBC

,

Da’awa: Wani mai amfani da shafin X  ya wallafa bidiyon da ke da’awar wai wasu ‘yan Filani ta’adda sun fara horas da kansu kan yadda ake amfani da kananan jiragen nan marasa matuka. 

Bidiyon Fulani ‘yan ta’adda na horasawa da kananan jirage marasa matuka na drones, tsoho ne

Hukunci: Yaudara ce. DUBAWA ta gano cewa bidiyon ba sabo ba ne. Bifiyon ya fara bulla cikin watan Mayun shekarar 2024 dan haka an sake amfani da shi ne tare da taken da ba daidai ba.

Cikakken bayani 

Wani mai amfani da shafin X ranar 9 ga watan Yulin 2026 ya wallafa wani bidiyo mai tsaown daiku 45 ya na da’awar wai yanzu Filani ‘yan ta’adda sun ma fara horas da kan su kan yadda ake amfani da kananan jiragen drones wato marasa matukan nan.

Mawallafin ya yi wa labarin taken “”yan ta’adda Filani yanzu su na koya wa kansu yadda ake amfani da kananan jiragen yaki marasa matuka. Mun shiga yanayin daga dagar da za ta dauki lokaci mai tsawo.”

Bidiyon ya nuna matasa maza da dama sun taru a wani wurin da ya yi kama da daji haka. Daya daga cikinsu na kwance a kasa yayin da wani ke amfani da na’urar da ake amfani da ita wajen sarrafa na’urori daga nesa yana sarrafa yadda jirgin ke yawo. Dukkansu na kallo cikin wani yanayi na doki da raha.

Daga 13 ga watan Yulin 2026, mutane sama da 140,200 sun kalli bidiyon, 97 sun mayar da martani, wasu 203 sun sake wallafa labarin, akwai alamar like sama da 474, wasu 182 kuma sun adana labarin.

Wannan labarin dai ya janyo ra’ayoyi mabanbanta daga masu amfani da shafin. 

Wani mai amfani da shafin, @olamidedad, tambaya ya yi, “Wa ke saya mu su drones kuma Dan Allah? 

Wani kuma, @LibraryCos78, ya yi tsokaci kamar haka, “Lallai wadannan suna kara inganta wannan wasan na su na ta’addanci da fashin daji. Ko daya ba suwa wasa.”

Wannan batun dai ya dauki hankali a shafukan Facebook da YouTube

Ganin yadda matsalar tsaro ta yi kamari da ma yiwuwar tasirin da irin wannan labarin ke da shi kan tsaron ne ya sa DUBAWA tantance labarin.

Tantancewa

DUBAWA ta fara da amfani da manhajar INVID wajen zabo mahimman hotunan da za ta yi amfani da su cikin manhajar da ke tantance asalin hotuna.

Wannan binciken ya kai mu ga wani labarin da aka wallafa ranar 19 ga watan Mayu a jaridar Daily Trust da taken “‘Yan fashin daji na amfani da jirage marasa matuka a wani wurin da ba’a tantance ko ina ba ne.” Rahoton ya kuma bayyana cewa Zagazola Makama ya wallafa bidiyon a shafin X. Shi kansa Zagazola ya kwatanta bidiyo da cewa ‘yan fashin daji yanzu sun lakanci yadda ake amfani da irin wadannan jiragen.

Haka nan kuma DUBAWA ta sake gano wani rahoton makamancin wannan wanda aka  wallafa a shafin Tori.ng ranar 20 ga watan Mayun 2024, wanda shi ma ya danganta labarin da gargadin Zagazola Makama.

“Shin kuna iya tunanin ma abin da zai biyo baya idan har wadannan miyagun suka sami ilimin fasahar amfani da irin wadannan nau’rorin? Ku gani fa, ‘yan fashin dawa na amfani da jirage marasa matuka da fasahohi da shafukan sada zumunta irin su TikTok, Facebook, da Instagram. Dole ne mu farga.”

Da muka bi hotunan dalla-dalla muka kwatanta su gefe da gefe mun gano cewa an yanka wasu bangarorin ainihin bidiyon na 2024 aka hada sabo, kuma ba hujja ba ce ta afkuwar wani sabon lamari.

Bidiyon Fulani ‘yan ta’adda na horasawa da kananan jirage marasa matuka na drones, tsoho ne

Hoton kwatancin da muka yi na lokacin da ke kan tsohon bidiyon da sabon da aka kirkiro.

Tsohon bidiyon na da tsawon dakiku 46 yayin da sabon da aka kirkira kuma ke da tsawon dakiku 45. Duka bidiyoyin biyu iri daya ne, abin da ya nuna cewa tsohon ne kawai aka rage.

DUBAWA ta gudanar da binciken mahimman kalmomi dan gano ko wani abu ne da ya faru kwanan nan amma ba ta ga labarin cikin shafukan kafofin yada labarai masu nagarta ba. Haka nan kuma babu wani labarin da ke nuna cewa an nadi bidyon cikin shekarar 2026 ko ma wani atisaye irin shi wanda Fulani ‘yan ta’addan suka gudanar.

A Karshe

Wannan da’awar wanda ya nuna atisayen Fulani yaudare ce kawai. Binciken DUBAWA ya nuna cewa bidiyon ya dade a yanazr gizo, hasali ma tun watan Mayun 2024, an sake wallafa shi ne kawai da sabon take dan ya yi kama da abin da wani abin da ya faru kwanan nan.

Wannan aiki an aiwatar da shi karkashin cibiyar koyon Aikin Jarida da Kirkire-kirkire da Ci gaba (CJID) tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai.

Exit mobile version