Site icon Dubawa

Bidiyon kungiyar ‘yan tawayen Amhara Fano na Ethiopia a ka yi amfani da shi wajen kwatanta matsalar tsaro a Najeriya

Video of Ethiopia’s Amhara Fano militia used to depict security threat in Nigeria

Asalin hoton: Lawrence Ibe.

Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook, Lawrence Ibe, ya wallafa wani bidiyo da ke nuna wani babban taron maza cikin kayan sojoji ya na da’awar cewa ‘yan bindiga ke nan a Najeriya yayin da suke shirin kai hari.

Bidiyon kungiyar 'yan tawayen Amhara Fano na Ethiopia a ka yi amfani da shi wajen kwatanta matsalar tsaro a Najeriya

Hukunci: Yaudara ce. Binciken da muka yi ya nuna cewa wadannan masu kama da sojoji a bidiyon na da alaka da mayakan Amhara Fano na kasar Ethiopia, ba ‘yan Najeriya ba ne.

Cikakken bayani

Ranar hudu ga watan Yunin 2026, Lawrence Ibe, ya wallafa bidiyo na wasu daruruwan maza sun taru a wani wurin da ke kama da sansani na wucin gadi. Mawallafin labarin (da aka adana a nan) ya yi zargin cewa mutanen da ake gani ‘yan bindiga ne a Najeriya wadanda ke shirin kai farmaki kan wadanda ba su ji ba su gani ba kuma ya yi kira ga al’umma da ta tashi tsaye ta kare kanta.

“Ku zauna cikin shiri. Abin da ke zuwa ba ku taba ganin irin sa ba. A cewarsu wannan sansani daya ne, suna da wasu karin sansanonin. Ku yi duk wani abun da za ku iya yi wajen kare kanku da iyalanku. Yanzu da ku sai Allah,” mawallafin ya bayyana.

Daga 5 ga watan Yunin 2026, jama’a sun kalli bodiyon har sau 50,000, wasu 216 sun yi ma’amala da batun, 132 sun yi tsokaci sa’annan an sake raba labarin sau 152.

Duk da cewa mawallafin bai fayyace ko an nadi bidiyon a Najeriya ba ne, gargadin da ya yi ya firgita jama’a, abin da ya kuma  janyo hasashe a tsakanin masu amfani da shafin wasu har suna kokarin gano asalin bidiyon, yayin da wasu kuma kai tsaye suka fassara bidiyon a matsayin babban barazanar tsaro.

Muhammad Sani Nalele cewa ya yi “duk yadda za ku yi ku guji tafiya da mota.”

Yayin da shi kuma Adekunle Kolawole cewa ya yi, “Wannan tsohon bidiyo ne kuma ba Najeriya ba ne.”

Da ya ke mayar da martani ga Adekunle, mawallafin sai ya dura masa ashar kamar haka “mahaukaci mai goyon bayan mugunta,” Shi ma  Wake Up NegroChristian David ya amsa Adekunle da na sa kalaman da ke masa gatse kamar haka “A cocin ka ne ko masallacin ka.”

DUBAWA ta kuma ga cewa wani mai amfani da shafin Facebook din shi ma ya wallafa bidiyon a nan ranar biyar ga watan Yunin 2026 da taken “ on June 5, 2026, with the caption “Kungiyarsu ta yi dammarar nuna adawa ga kiristoci. Yanzu kun fahimci abin da na ke nufi ifan na ce an kaddamar da kisan kare dangi a kan kiristoci.”

Mun kuma sake ganin wannan barazanar a shafin  YouTube a nan da shafin  X a nan.

Daga Juma’a 5 ga watan Yunin 2026, labari na biyun da aka sanya a Facebook ya ambaci Najeriya a nan kuma har mutane sama da  21,000 sun kalla, wasu 123 sun yi ma’amala da shafin, akwai tsokaci sama da 143 sa’annan an sake rabawa sau 38. 

Bisa la’akari da ra’ayoyi mabanbantan da aka yi a kan da’awar da ma yunkurinmu na dakile ire-iren labaran da ke haddasa tashe-tashen hankula ne ya sa DUBAWA daukar nauyin tantance gaskiyar wannan lamarin.

Tantancewa

Domin gano mafarin bidiyon, mun yi amfani da mahimman hotunan cikin bidiyon ta yin amfani da manhajar reverse-image searches. Manhajar tantance mafari da sahihancin hotuna ta google.

Bincikenmu ya hada mu da bidiyon da aka wallafa a jaridar Tigray Times a shafin Facebook, wata jarida mai zaman kanta, kuma kafar yada labarai ta daya daga cikin yankunan Ethiopia wadda ke mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi tattalin arziki da zamantakewa, siyasa da harkokin yau da kullun a Tigray na kasar Ethiopia. Jaridar ta danganta bidiyon da mambobin kungiyar Amhara Fano, wata kungiyar ‘yan bindigar da ke gudanar da ayyukanta a yankin Amhara na kasar Ethiopia.

Kungiyar Amhara Fano kungiya ce da ke da rajin kare hakkoki da ‘yancin kabilarta a Ethiopia kuma ta dade ta na tawaye da bijirewa gwamnatin tarayyar kasar. Ta fara ne a matsayin kungiyar tsaro na sa-kai wadanda suka taimakawa sojojin tarayya sadda aka yi yakin Tigray amma bayan yakin sai suka zama ‘yan tawaye a shekarar 2023 bayan da gwamnatin ta yi yunkurin rusa kungiyoyin tsaron da suka bulla a yankunan a wancan lokacin.

Karin bincikin da muka yi ya kai mu ga binciken da shafin tantance sahihancin bayanai irin na mu, Africa Check ya wallafa wanda shi ma ya tabbatar cewa mutanen da ke bidiyon dakarun ‘yan tawayen kungiyar Amhara Fano ne a Ethiopia. Bisa bayanan da suka wallafa, dama can an taba yawo da wannan bidiyon a shafukan sada zumunta tare da’awowi masu nufin yaudarar jama’a dangane da asalin shi. Haka nan kuma yawancin sakamakon binciken da muka yi kan hotunan ya zo daidai da abinda aka wallafa a Africa Check.

A Karshe

Bincikenmu ya nuna mana cewa mambobin kungiyar ‘yan tawayen Amhara Fani ne ke cikin bidiyon. Dan haka wannan da’awar yaudara ce.

Cibiyar Habbakawa da Koyon Sabbin Dabarun Aikin Jarida (CJID) ke aiwatar da wannan horaswar ta musamman tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai.”

Exit mobile version