Da’awa: Wani bidiyo da ya bazu ya nuna wasu matasa a Bodinga, Jihar Sokoto, suna lakadawa wani Babban Limami duka saboda ya yi wa’azi yana kamfen ɗin takarar shugaban ƙasa na APC ta Musulmi da Musulmi.
Hukunci: Yaudara ce. An ɗauki bidiyon ne a Sudan, yayin da hoton da aka yi amfani da shi wajen yaɗa da’awar AI ne ya ƙirƙire shi. Sakataren Ƙungiyar Alarammomi ta Bodinga ya tabbatar da cewa ba a yi wa wani malami duka ba.
Cikakken Bayani
A yayin da ake ci gaba da muhawara kan batun siyasar takarar Musulmi da Musulmi na jam’iyyar APC a Najeriya, wasu da’awoyi sun bazu a kafafen sada zumunta cewa fusatattun matasa sun yi wa wani malamin addinin Musulunci duka a Jihar Sokoto.
Wani rubutu da aka wallafa da harshen Hausa a ranar 24 ga Agusta, 2026, ya yi iƙirarin cewa lamarin ya faru ne yayin da limamin ke wa’azi, inda ya ce duk wanda bai zaɓi Musulmi/Musulmi ba ya kamata ya yi shakkar imaninsa.
Wani ɓangare na da’awar na cewa, “Wasu matasa sun yi wa limamin wani masallaci duka saboda ya yi wa Tinubu kamfen a kan mimbari; lamarin ya faru a Ƙaramar Hukumar Bodinga ta Jihar Sokoto.”
Labarin ya samu yaɗuwa sosai bayan tsohon minista Solomon Dalung ya kuma wallafa da’awar, inda ya bayyana cewa bai da tabbacin labarin.
Wani shafin Facebook mai suna Hausawa, ya yaɗa wani bidiyo (an adana shi nan) wanda ake ikirarin ya nuna lokacin harin, tare da taken, “wannan shi ne bidiyon da wasu matasa a Bodinga suka yi wa babban limami duka saboda kiran mutane da su zaɓi Musulmi Musulmi”.
Ya zuwa ranar 26 ga Agusta, 2026, bidiyon ya samu kallon mutane 79,000, sama da martani 2,100, sharhi 384 da kuma yaɗashi sau 482.
Da’awar ta jawo martani iri-iri a kafafen sada zumunta. Hassan Yahaya Dahiru ya yi sharhi da cewa, “Kun yi abin da ya dace, wallahi.”
Wani mai amfani da Facebook, Kefas Trump Habila, ya rubuta, “Madalla, dole ne mu tsaya kafada da kafada domin ceto ƙasarmu.”
A gefe guda, Rukkayya Dangwaram ta nuna shakku, inda ta tambaya, “Wannan wasa ne ko gaskiya?”
Saboda yanayin da’awar da kuma yiwuwar ta haifar da rikicin ƙabilanci, addini da siyasa, DUBAWA ta binciki da’awar.
Tantancewa
DUBAWA ta gudanar da binciken kalmomi, amma ba ta samu rahotannin da za a iya dogaro da su daga manyan kafafen yaɗa labarai na Najeriya da kafafen yaɗa labarai na jihar Sokoto da ke tabbatar da cewa an yi wa wani limami duka saboda kalaman siyasa a Bodinga ba.
Binciken ɗaya daga cikin hotunan da aka yi amfani da su wajen yaɗa labarin, ta hanyar amfani da manhajar SynthID ta Google, ya nuna cewa hoton AI ne ya ƙirƙire shi.
Bincike na kusa da ido ya kuma nuna wasu alamomin hoton da aka ƙirƙira ta hanyar AI, ciki har da gurɓatattun hannaye, yatsun da suka haɗe, da kuma siffofin fuskokin wasu mutanen da ba su yi kama da na zahiri ba a bayan hoton.

Hoton da ke nuna alamomin da ke tabbatar da cewa AI ne ya ƙirƙire shi.
Domin tantance bidiyon, DUBAWA ta ciro wasu hotunan bidiyon tare da gudanar da binciken hotuna. Sakamakon binciken ya gano cewa an fara wallafa bidiyon ne a Facebook a ranar 15 ga Disamba, 2025, a cikin shafin wata ƙungiyar al’ummar Sudan mai suna “زول ماركت | سوق السودان” (Kasuwar Zol | Kasuwar Sudan).
Taken Larabcin da aka wallafa tare da bidiyon, wanda aka fassara zuwa Hausa, ya ce, “Rikici a cikin wani masallaci a birnin Nyala… Ina zaman lafiya, ina ‘gwamnatin zaman lafiya’?” Nyala na nufin babban birnin Jihar Darfur ta Kudu a Sudan.
Wannan ya tabbatar da cewa bidiyon ba na baya-bayan nan ba ne, an ɗauke shi a Sudan, kuma ba shi da alaƙa da Bodinga ko siyasar Najeriya.
Bugu da ƙari, DUBAWA ta tuntubi Jabir Umar, Sakataren Ƙungiyar Alarammomi ta Bodinga. Jabir ya yi watsi da da’awar, inda ya bayyana ta a matsayin ƙarya tsagwaronta.
Da yake fayyace abin da ya faru a Masallacin JIBWIS na Bodinga, Jabir ya bayyana cewa an gyara masallacin ne, kuma Gwamna tare da wasu manyan jami’an gwamnati sun shirya halartar bikin ƙaddamar da masallacin a hukumance a ranar 21 ga Agusta, 2026.
Sai dai, ruwan sama mai ƙarfi a ranar Juma’a ya kawo cikas ga jadawalin da aka shirya daga ƙarfe 12:00 na rana zuwa 1:40 na rana, lamarin da ya sa aka samu tsaikon yin sallar Juma’a zuwa ƙarfe 2:30 na rana. Wannan jinkiri ya sa wasu daga cikin masu ibada suka tafi da wuri, yayin da aka kuma ga wasu na nuna rashin jin daɗi.
Ya ƙara da cewa, “Bayan wannan jinkirin, ba a samu wata hatsaniya ko tashin hankali ba.”
DUBAWA ta kuma duba shirin kai tsaye na taron da gidan talabijin na Rima, mallakin hukumar kafafen yaɗa labarai ta jihar Sokoto, kuma ta tabbatar da cewa babu wata arangama da ta faru yayin bikin ƙaddamar da masallacin.
A Karshe
Da’awar cewa wasu matasa fusatattu sun yi wa wani limami duka a Bodinga, Jihar Sokoto, saboda ya yi kamfen ɗin tikitin Musulmi-Musulmi na APC, Yaudara ce. Bidiyon da aka yi amfani da shi wajen yaɗa da’awar an ɗauke shi ne a Sudan.