Da’awa: A wani bidiyo da aka sa a Shafin sada zumunta na facebook dake yanar gizo ya nuna cewa wasu ‘yan ta’adda ‘yan Fulani sun kai harin ramakon gayya kan kabilar Kamuku a jihar Nejar bayan da wasu sojoji sun kai musu farmaki.

Hukunci: Karya ce! Hujojjin da aka samu sun nuna cewa rikicin kabilanci ne ya barke tsakanin kabilun Fulani da Kamuku amma ba harin ramakon gayya ba.
Cikakken bayani
A ranar Asabar 18 ga Yuli 2026 a wani Shafin facebook mai suna ‘Political Affairs Int.’ ya wallafa wani bidiyo da ya nuna yadda wani gida ya kama da wuta tare da da’awar wai ‘Harin ramakon gayya da ‘yan ta’adda ‘yan Fulani suka kai wani kauye bayan rundunar sojin Najeriya ta kai musu farmaki a jihar Neja’.
Da’awar ya kuma kara da cewa ‘Fulani ‘yan ta’adda’ sun kai wa ‘yan kabilar Kamuka hari inda suka kashe mutum 143 a jihar Neja. Wanda ya wallafa bidiyon ya bayyana cewa gwamnan jihar ya yi zaman gaggawa.
Zuwa ranar Talata 21 ga watan Yuli 2026 da’awar da aka sa a (nan) mutum 122 sun yi ma’amala da bidiyon, 58 sun mayar da martani, 53 sun sake wallafawa, biyar sun saka alamar bookmark.
Dubawa ta gano wannan bidiyo wadda wata jarida ‘Hausaland Magazine’ ta sa a shafin ta na facebook ranar 18 ga Yuli 2026 da irin wannan da’awar.
A ranar Talata 21 ga Yuli 2026 da’awar da aka saka a (nan) mutum 175 sun yi ma’amala da bidiyon, 99 sun mayar da martani, 166 sun sake wallafawa, 10 sun saka Alamar bookmark.
Martanin da mutane suka mayar ya nuna cewa wasu da dama sun amince da da’awar cewa gaskiya ce kuma sun nuna rashin jin dadin su game da bidiyon.
Wani Madu Sale ya rubuta cewa ‘ Idan har matasa basu mike tsaye sun kawo karshe wadannan muggan aiyukkan ba gwamnati ba za ta yi ba. Kamata ya yi mu yi tunani mai zurfi domin gano hanyoyin da za su taimaka wajen ceto kayukan mu’.
Shi ma Apiyanteide Franco ya rubuta cewa ‘Su kare kansu, rayukansu da dukiyoyin su’.
Meka’c Anagor ya rubuta cewa ‘Allah mai girma mai iko duka, hakan shine ake nufu da ka girbi abin da ka shuka’.
Ganin martanin da mutane ke maidawa da yadda martanin ka iya tada wani rikicin kabilancin ya sa DUBAWA ta gudanar da bincike.
Tantancewa
DUBAWA ta gudanar da bincike domin gano labarai ko rahotani dake da alaka da bidiyon amma bata samu bayanin da ya fito daga wata hukuma mai halaccin da ta bayyana harin a matsayin harin da ‘yan ta’adda ‘yan Fulani suka kai wa ‘yan kabilar Kamuku ba.
Rahotani da dama masu tushe sun tabbatar cewa rikici ne ya barke tsakanin Fulani da Kamuku a karamar hukumar Rafi dake jihar Niger.
Rahotanin da gidajen jaridu da suka hada da PREMIUM TIMES da TVC da sauran su tabbatar cewa rikicin kabilanci ne ba harin ‘yan ta’adda ba.
Sakamakon binciken ya kara nuna cewa rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta bayyana harin a matsayin rikicin kabilanci.
Rundunar ‘yan sandan jihar a shafin ta na facebook a da’awar da ta wallafa ranar 6 ga Yuli 2026 ta yi Karin haske game da haka. Bayan ta ziyarci Kagara rundunar ta shaida cewa kwamishian ‘yan sandan jihar, CP Adamu Elleman tare da wasu manyan hafisoshin tsaro da mataimakin gwamnan jihar sun ziyarci kauyukan da rikicin ya shafa musamman wadanda ke kan hanyar zuwa Tegina zuwa Kagara dake karamar hukumar Rafi.
Rundunar ta tabbatar cewa jami’an tsaron sun ziyarci wadannan kauyuka ne bayan rikicin kabilancin da ya barke a yankin amma ba domin harin da ‘yan ta’adda Fulani suka yi ba.
Domin tabbatar da binciken, DUBAWA ta nemi ganawa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar SP Wasiu Abiodun amma sai bai ce komai ba kuma sai ya hada wakilin gidan jaridar da bayanan da gwamnan jihar, Bago ya yi sadda ya ziyarci masarautar Kagara inda yake cewa gwamnan ya riga ya yi bayani game da harin.
DUBAWA ta duba bayanan da gwamnan ya yi wanda aka wallafa a shafinsa na facebook ranar Juma’a 17 ga Yuli 2026.
A bayanan da gwamna Bago ya yi y ace ‘Yau, na ziyarci masarautar Kagara bayan rikicin kabilancin da aka yi tsakanin Fulani da Kamuku dake karamar hukumar Rafi.
Gwamnan ya tausaya wa mutanen da harin ya shafa sannan ya yi alkawarin cewa gwamnati za ta tallafawa duk wadanda harin ya shafa kuma ya yi kira ga mutanen da su zauna lafiya da junan su.
Kamar yadda rundunar ‘yan sandan jihar ta shaida shima gwamnan ya tabbatar cewa rikicin kabilanci ne ba harin ‘yan ta’adda ba.
Bayanan da gwamnantin jihar Neja, rundunar ‘yan sanda da kafaffen yada labarai masu tushe suka bada sun karyata bayanan da ake ta yadawa a facebook.
A Karshe
Da’awar dake nuna cewa harin ramakon gaiyya ne aka yi wa kabilar Kamuku dake jihar Neja karya ne.
Hujojjin da DUBAWA ta samar sun tabbatar cewa rikicin kabilanci ne da ya barke tsakanin Fulani da Kamuku. Bayyana cewa Fulani ‘yan ta’adda ne suka kai harin bai bayyana gaskiyan lamarin ba kuma hakan ka iya tada wani rikicin kabilanci.
Wannan aiki an aiwatar da shi karkashin Cibiyar koyon Aikin Jarida da Kirkire-kirkire da Ci gaba (CJID) tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai.