Site icon Dubawa

Bidiyon rikicin Ethiopia ake yadawa a sunan mamayar ‘yan jihadi a yankin Arewacin Najeriya

Ethiopian conflict video shared as Jihadist takeover of Northern Nigerian villages

Da’awa: Wani mai amfani da shafin X ya wallafa bidiyon wasu mutanen da ke dauke da makamai suna tafe kan hanya, tare da da’awar cewa ‘yan jihadi ne ke ihun “Allahu Akbar” yayin da suke mamayar kauyukan Najeriya ba tare da an kalubalance su ba. 

Bidiyon rikicin Ethiopia ake yadawa a sunan mamayar ‘yan jihadi a yankin Arewacin Najeriya

Hukunci: Karya. Wannan bidiyon ba Najeriya ba ne kuma ma mutanen da ke ciki ba su yi wani ihun “Allahu Akbar” ba. Bidiyo ne da ya yi mafari daga rikicin Oromia a Ethiopia kuma ba shi da wata dangantaka da harkokin tsaron Najeriya.

Cikakken bayani

Ranar 20 ga watan Agustan 2026 wani mai amfani da shafin X, Falana Muyiwa (@Muyiwa66), ya wallafa wani bidiyo mai tsawon minti daya da dakiku 23 eanda ke nuna wadansu mutanen da ke sanye da kayan sojoji dauke da makamai suna tafiya a layi daya a kan wata hanyar karkara. Bidiyon na dauke da wasu bayanai biyu a rubuce. Daya tambaya ce “To ina sojojin saman Najeriya?” na biyun kuma: “Sun mamaye mana kasarmu.”  

Bayanin da aka yi a karkashin bidiyon kuma shi ne, “A ko da yaushe na kan yi tambaya kan inda sojojin saman Najeriya suka shiga? Yaya za’a yi a ce wadannan ‘yan jihadin suna yawo cikin walwala suna kuwar allahu akbar suna mamayar kauyuka a Najeriya.”

Wannan labarin wanda za’a iya gani a nan mutane sama da dubu 30 sun kalla, an yi kwament 93 an kuma sake wallafawa sau 486 akwai alamar like 610 ranar 22 ga watan Agustan 2026, wuni biyu da wallafawa abin da ya karu daga mutane 4,400 masu kallo da kwament 8 da alamar like 78 yayin da wadanda suka sake yadawa kuma 47 jim kadan bayan da aka wallafa, abin da ya nuna yaduwar da labarin ya yi cikin gaggawa.

Wannan labarin ya dauki hankali da martanoni da dama, kuma yawanci sun dauki bidiyon a matsayin gawawar gwamnati abin da suka yi amfani da shi wajen bayyana takaicinsu kan sauran batutuwan da suka dade suna ci musu tuwo a kwarya.

Onyebuchi Nwaiwu (@NWAIWUJr) cewa ya yi, “Ba za su kai mu su hari ba domin ‘yan ta’adda ‘ya’yansy ne da ‘ya uwansu. Abin da suka sani shi ne kai hari kan kungiyar ‘yan awaren IPOB/BIAFRANS,” su na danganta zargin da yunkurin fafutukar #BiafraReferendumNow.

Jaridar Njaba Times (@njaba_times) ta ma kara da, zargin wai, “Sojojin sama da na kasa a Najeriya mambobin, kungiyoyin ‘yan bindiga Fulani ne da ISWAP. Yanzu Najeriya ta zama kasar Fulani a hukumance, marigayi tsohon shugaba Buhari ne ya tabbatar da hakan. Idan har ba ku son wannan tsarin, tilas ne ku tashi tsaye ku kare kanku da iyalanku.”

Shi kuwa MindGame (@KokoEdem) tsokaci ya yi yana cewa, “Ku jira sai sadda muka sami gwamnatin da za ta sa al’umma kan gaba, a lokacin ne za ku ga karfin ikon dakarun Najeriya. A halin yanzu ba mu da gwamnati.”

Nana Obiri II (@NanaobiriII) ya yi amfani da wannan labarin ne wajen fadada wadansu labaran marasa tushen da ke danganta batun da addini da lamuran siyasar da suka shafi tasirin kasashen duniya. A cewar Nana, “Saudiyya ce ta kowa mu su wadannan abubuwan sa’annan suka dako su suka kawo su Afirka suka zamar da su musulmi dan su rika zuwa hajji kowace shekare suna kashe kudi kan tattalin arzikin kasar.”

Babu martanin da ya bukaci sanin asalin bidiyon ko ma sahihancinsa. A maimakon haka kowa ya amince da shi a matsayin zahiri sa’anan suka yi amfani da shi wajen bayyana na su takaicin.

Bisa la’akari da yadda labarin ya ke cewa ‘yan Jihadi ne ke kutsawa a Najeriya da yadda ya ke zargin dakarun Najeriya da hannu da ma yanayin yadda ya dauki hankalin jama’a wanda zai iya haddasa tsoro da rashin yadda a kasar da ke fama da rashin tsaro ne ya sa DUBAWA tantance sahihancin batun.

Tantancewa

Mun fara da tantance da’awar da aka yi cikin bayanin da aka wallafa da bidiyon wanda ke cewa ana iya jin mutanen suna” ihun all@hu akbar.” Mun yi bitar bidiyon mun saurari baitukan sautin da kyau kuma ko daya ba mu ji mutanen suna cewa Allahu Akbar ko ma wani abin da ke kama da haka ba. Sautin yadda kafafunsu ke tafiya a kasa kadai muka ji da sauran sautukan da ake iya samu daga irin wurin da su ke.

Daga nan sai muka duba hotunan dan gano asalinsu kan dandaloli daban-daban.

Bidiyon ya fara bulla ne cikin wani labarin Facebook a wani shafin da ke amfani da harshen  Afaan Oromoo mai suna Jl Kaayyoo Egeree ranar 31 ga watan Yulin 1016, makwanni uku kafin wannan da’awar ta bulla a shafin X.

Bayanin da aka yi dangane da shafin a cikin harshen Oromo, ya kwatanta bidiyon a matsayin abin da ya kira “nasara” a gundumar Alge Sachi na yankin Ilu Abba Bora a yankin Oromia na kasar Ethiopia.

Ilu Abba Bora wani sashe ne a yankin yammacin Oromia, Ethiopia wanda ke da iyaka da yankin Benishangul-Gumuz kuma ya dade yana fama da rikicin da ke da alaka da rundunar ‘yantar da mutanen Oromo wadanda aka fi sani da OLA, wadda wata kungiya ce mai dammara a Ethiopia kuma ba ta da wata alaka da Najeriya.

Harshe, da kalamai, da yankunan da ake amfani da su a wannan shafin duk sun danganci Ethiopia ne ba Najeriya ki ma wasu kungiyoyin jihadi da na tsaro a Najeriya ba.

Ba mu sami wata hujjar cewa an dauki bidiyon a Najeriya ba, kuma babu wani rahoton ‘yan jihadi suna mamayar kauyukan Najeriya kamar yadda aka nunar. Haka nan kuma babu wani bayani daga hedikwatar sojojin Najeriya ko ma dai wata ma’aikata ko hukumar tsaron Najeriya dangane da batun.

A Karshe

Da’awar wai ‘yan jihadi na mamayar kauyukan Najeriya karya ce. Bidiyon ya yi mafari ne daga wani rikicin da ba shi da wata alaka da Najeriya. Rikici ne da ke garuwa a yankin Abba Bora na Iromia da ke kasar Ethiopia.


Wannan aiki an aiwatar da shi  karkashin Cibiyar Koyon Aikin Jarida da Kirkire-Kirkire da Ci-gaba (CJID) da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai ta EU.   

Exit mobile version