Site icon Dubawa

Bidiyon Rikicin Sudan ne aka nuna a matsayin Rikicin da aka fafata tsakanin soja da ‘yanta’adda a Najeriya

Sudan conflict footage used to portray battle between Nigerian Army and terrorists

Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook ya yada wani bidiyo inda yayi da’awar cewa ‘yan ta’adda na kai farmaki kan dakarun sojan Najeriya.

Bidiyon Rikicin Sudan ne aka nuna a matsayin Rikicin da aka fafata tsakanin soja da ‘yanta'adda a Najeriya

Hukunci: Karya ce. Wannan bidiyo bai nuna ‘yanta’dda na fafatawa da dakarun sojan Najeriya ba, shedu da aka tattara sun nunar da cewa fada ne da ake ci gaba da yi a kasar Sudan.

Cikakken Sako

Dakarun sojan Najeriya na ci gaba da fafatawa da ’yanta’adda masu dauke da makamai a fadan soja daban-daban a fadin kasar. Sai dai daga lokaci-lokaci ana ci gaba da samun wasu hotuna da bidiyo da ake sake yada su ana yaudarar al’umma da cewa ana fada ne tsakanin dakarun sojan Najeriya da ‘yanta’ada. 

Wani mai amfani da shafin na Facebook mai suna, @Issiaka the blogger, ya yada wannan bidiyo inda yayi da’awar cewa ‘yanta’adda na fafatawa da dakarun sojan Najeriya. 

Wannan bidiyo mai tsawon kimanin dakika 26 kamar yadda aka alkinta shi (a nan)ya nuna wasu mazaje guda biyu a wani budadden wuri mai tarin rairayi. Daya daga ciki yana barin wuta, yayin da dayan ke daukar kansa hoto a kusa.

Bayananin da aka rubuta a wannan bidiyo na cewa “‘yanta’adda na fafatawa da dakarun sojanmu.” 

Wani taken labarin na cewa: “Labari da Dumi-Dumi! Fada tsakanin dakarun sojan Najeriya da ‘yanta’adda.”

Ya zuwa ranar 10 ga watan Agusta,2026 wannan wallafar ta samu wadanda suka nuna sha’awarsu 393 da masu tsokaci 92 da wadanda suka sake yadawa 21 da masu kallo 100,000.

DUBAWA ta duba irin tsokaci da mutane ke yi don fahimtar inda suka dosa a dangane da da’awar.

@SkhandaMeva InjaYethafa ya asanya alamar tambaya ne a dangane da asalin ina ake wannan abubuwa: “Wa ke daukar nauyi?? Kamar duk kun mayar da hankalinku kan Afurka ta Kudu yayin da kasarku ke ci gaba da cin wuta.”

@Emmanuel Unuakhalu ya rubuta cewa “Suna da karfin gwiwa kasancewar suna da daurin gindi daga sama an fada masu cewa babu abin da zai faru da su.”

@Gawori Hasan  ya aza ayar tambaya ne kan yadda sojojin ke tunkarar lamarin, inda yayi tambaya da cewa, me yasa kuke bata lokaci kuna yakarsu ta kasa bayan kuna da jiragen sama na yaki da za ku iya kai farmaki.” 

@Tahir Muhammad shima yayi tambaya ne da cewa, “Wane harshe suke amfani da shi? Ina zaton na al’ummar Sudan ne.”

Wasu masu amfani da shafin na Facebook sun yada wannan labarin kamar yadda za a iya gani nan da nan.

DUBAWA ta ga dacewar gudanar da bincike don tabbatar da ganin cewa ko da gaske ne wannan fafatawa ce aka yi a tsakanin dakarun sojan na Najeriya da ‘yanta’adda, saboda ci gaba da yada wannan bidiyo zai kara kawo rudani da yaudara a shafukan sada zumunta kan yadda sojojin ke gudanar da ayyukansu dama yadda halin tsaro yake a fadin kasar.

Tantancewa

DUBAWA ta yi filla-filla da bidiyon ta hanyar amfani da manhajar InVID ta sake nazartar wadannan hotuna, wannan ya kaimu ga wannan wallafa a Facebook wacce aka yada a ranar 31 ga watan Yuli, 2026, wacce ta nuna irin wannan bidiyo amma an yi rubutun da harshen Arabiya.

DUBAWA ta yi amfani da Google wanda yayi fassarar da ta nuna “Jaruman Kordofan.”

DUBAWA ta sake neman karin bayani a dangane da Kordofan inda ta gano cewa yanki ne da ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula tsakanin sojan gwamnati na Sudan’s Armed Forces (SAF) da masu tawaye na  Rapid Support Forces (RSF). 

An fitar da rahotanni da dama kan rikicin da ke faruwa a bangarorin nan biyu har da musayar wuta da ake samu, wannan za a iya alakantawa da harbin da tunkarar da aka gani a bidiyon.

Sauran bangarorin biyu kuma sun nunar da tarin rahotanni kan yadda ake ci gaba da fafatawa a Sudan, wannan ya kuma kaimu ga wata wallafar a shafin na Facebook wanda dai shi mai shafin na Facebook ya sake yi a ranar 31 ga watan Yuli,2026.

Wannan shafin na Facebook ya zo da taken labari da ke cewa “Babban sauyi yazo daga Sudan gwamnati da ke karkashin jagorancin Hameti ta samu koma baya, lamari da ya ritsa da dakarun sojan Sudan da wasu kabilu na yankin Darfur.

Dakarun na RSF na samu tallaf idaga Daular Larabawa ta Emirate da wasu kasashe kamar Libiya da dama daga bangaren Haftar da Habasha da Chadi, sai dai a yanzu za a iya cewa labarin zai canza ganin irin koma bayan da dakarun na RSF suka samu koma baya da rasa sojoji, sun dade suna shiri 

Sun yi abubuwa da dama ga dakarun na kasar Sudan.” 

A duk binciken DUBAWA babu inda ta ga alakar wannan bidiyo da abin da ke faruwa a Najeriya, wanda ya wallafa wannan bidiyo a watan Yuli, 2026 ya alakanta abin da halin da ake ciki a Sudan yayin da wanda ya wallafa a watan Agusta,2026 ya ce lamarin ya faru a Najeriya ne.

Domin kara samo wasu bayanan dai DUBAWA ta sake bincikar shafin sada zumunta na  dakarun sojan Najeriya, ko za ta ga wannan bidiyo a baya-bayan nan amma babu abin da ta gani.

DUBAWA ta kuma bincika ko akwai wani rahoto da aka wallafa kan yadda aka fafata tsakanin dakarun sojan na Najeriya da ‘yanta’addar amma anan ma babu wani rahoto da ya nuna hakan, duk bidiyon da aka gani suna da alaka ne da Sudan.

A karshe 

Da’awar da bidiyon ya nuna cewa ‘yanta’’adda na kai farmaki kan dakarun sojan Najeriya karya ce. Shedu da DUBAWA ta gano sun gano cewa lamari ne da ya shafi Sudan ba Najeriya ba. 

Exit mobile version