Da’awa: Wani mai amfani da shafin X (@BishopPOEvang) ya yada wani bidiyo inda yayi da’awar cewa Mutane ne Hausawa aka raba da muhallansu da yin garkuwa da su da wadanda aka kashe sakamakon ayyukan ta’addanci na Fulani a karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara.

Hukunci: Yaudara ce. Bidiyon ya fito ne daga rikicin El Fasher, na Sudan ta Arewa.
Wannan bidiyo kungiyar kare hakkin bil’Adama ta Amnesty International ta yi amfani da shi, haka kuma jaridar Daily Sabah da Shai Fund sun nuna shi a irin bayanan da suka tattara na halin rikici da aka samu kai a yankin.
Cikakken Labari
A ranar Juma’a 3 ga watan Yuli,2026 wani mai amfani da shafin X ya yada bidiyon mai tsawon dakika15 kamar yadda za a gani an alkinta shi nan, inda aka yi wa labarin take da zargin cewa mutanen da ake ganin Hausawa ne wadanda rikici ya raba da muhallansu a Zamfara.
”Ga abin da taken ke cewa, “Mafi akasari Hausawa ne da aka raba da muhallansu da wadanda aka yi garkuwa da su ko wadanda Fulani suka kashe a karamar hukumar Bangudu ta jihar Zamfara. ”
Bidiyon ya nuna yadda mutanen ke tafiya a hankali a wani yanki mai kama da dajin sahara, wasu na dauke da jakunkuna a kansu wasu kuma na dauke da su a hannayensu.
Mun kuma ga wani yaro da kurar daukar kaya an makare ta da kaya daga gefe kuma motar sojoji ce dauke da dakaru a cikinta.
Ya zuwa ranar 4 ga watan nan na Yuli,2026, wannan bidiyo ya samu wadanda suka kalle shi 1,726 (views) da wadanda suka sake yada shi 22 (reposts) da masu nuna sha’awarsu 24 (likes) da masu ba da amsa a sashin tsokaci 2 da masu nuna cewa za su sake duba wallafar 3.
Wannan da’awa ta ja hankali na masu mayar da martani da dama.
Wani mai amfani da shafin na X @watk98913, ya rubuta, “ Za su wajen su mamaye zinare da ke a wajen.”
Wani mai amfani da shafin, @Clinton207O, yayi tsokaci da cewa “Gwamnoni na arewacin Najeriya da shugaban kasar Tinubu sun gaza wajen cika bukatar al’umma.”
Wannan wallafa an yadata a shafin na X da Facebook.
Duba da nau’i na wannan da’awa da irin hadarin da take tattare da shi na iya harzuka zukatan al’umma ga matsalar tsaro a Najeriya, hakan ya sanya ya zama wajibi a gudanar da binciken gano gaskiya kan da’awar.
Tantancewa
Mun nazarci wannan bidiyo ta hanyar amfani da manhajar bin diddigin bidiyo ta InVid, mun tsakuri wani bangare na bidiyon inda aka gudanar da binciken gano asalinsu.
Bincikenmu ya kai mu ga wani bidiyo irin wannan da aka wallafa a shafin LinkedIn na hukumar kare hakkin bil’Adama ta Amnesty International a ranar 2 ga watan Yuli,2026. Hukumar ta nuna halin da al’umma ke ciki na kunci a yankin sakamakon ayyukan dakarun RSF a lokacin da suka je aiki na kwace sansanin El Fasher da ke arewacin yankin Darfur na Sudan. Kungiyar ta kasa da kasa ta bukaci a tsayar da bude wuta a yankin nan take don ba da kariya ga fararen hula.
Dakarun na RSF dakaru ne masu damara da ke aiki tare da sojojin kasar ta Sudan don tunkarar duk wata barazana daga ciki da wajen kasar. Sai dai rahotanni daga kafafan yada labarai musamman na kasashen ketare da ma na cikin gida kamar su Daily Sabah da Arise News, na bayyana abin da ke faruwa cikin ayyukan na RSF a El Fasher, da ke arewacin Dafur na Sudan a matsayin kokari na kawar da wata kabila daga doran kasa ta hanyar kisan fararen hula da basu ji ba basu gani ba.
Haka kuma ita ma wata kungiya ta Amurka mai zaman kanta Shai Fund da ke aiki a Sudan a ranar 29 ga watan Oktoba,2025 ta fitar da wani rahoto inda tayi bayani mai kama da na kungiyar ta Amnesty International.
Rahoton ya nuna yadda dakarun na RSF ke nuna hali na rashin imani suna kisan fararen hula inda suke binsu gida-gida suna kisa saboda dalilai na kabilanci da addini.
Haka kuma akwai wasu hotuna na tauraron dan’Adam da ya nuna manyan kaburbura na mutanen da aka binne, yayin da a bangare guda dubban al’umma ke gudun tsira da ransu inda suke tafiya a dajika masu Sahara wasu a motoci makare da mutane inda rahotanni ke cewa wasu na mutuwa a hanya lokacin tafiya.
Duk da cewa a binciken da aka yi ta hanyar amfani da wasu muhimman kalmomi ya nuna wani rahoto na AP News a ranar 27 ga watan Yuni,2026, inda aka nuna wani hari na ‘yanta’adda a Talatar Mafara a jihar Zamfara, wannan hari bai kama da wanda mai da’awar ke ikirari ba, domin shi a nan mutane 15 aka kashe.
A karshe
Tantancewar ta nunar da cewa babu wata alaka hoton da ake nunawa mutane da dama da ake zargin Hausawa ne an raba su da muhallansu ko yin garkuwa da su ko kashe su a hannun ‘yanta’adda da ke zama Fulani a karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara, don haka da’awar yaudara ce.
Wannan aiki an aiwatar da shi karkashin Cibiyar koyon Aikin Jarida da Kirkire-kirkire da Ci gaba (CJID) tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai.