Site icon Dubawa

Bidiyon da ya nuna ‘yan ta’adda na dukan mabiya addinin Kirista yaudara ce

Video of terrorists flogging Christians, misleading

Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook, Glory Goodluck, ya yada wani bidiyo a ranar 19 ga watan Afrilu, 2026 inda yayi zargin cewa ‘yanta’adda daga arewacin Najeriya sun ware mabiya addinin Kirista suna dukansu tare da ‘yan ta’adda da terrorists.

Bidiyon da ya nuna ‘yan ta’adda na dukan mabiya addinin Kirista yaudara ce

Hukunci: Yaudara ce. DUBAWA a bincike da ta gudanar ta gano cewa wannan bidiyon an dauke shine a 2022 lokacin da aka yi garkuwa da wasu mutane da suke cikin jirgin kasa, babu wani rahoto ko wata sheda da ta nunar da cewa an ware wadanda aka yi garkuwa da su inda aka banbance su tsakanin mabiya addinin Kirisa ko Musulinci.

Cikakken Labari

A ranar 19 ga watan Afrilu, 2026 wani mai amfani da shafin Facebook Glory Goodluck ya wallafa wani bidiyo kamar yadda ake iya gani a nan da da’awar cewa ‘yanta’adda sun ware mabiya addinin Kirista suna zabga masu bulala a arewacin Najeriya. 

Taken labarain da aka hada da bidiyon shine: “Ka duba yadda ‘yanta’adda suka ware mabiya addinin Kirista suke zabga masu bulala, wannan yankin arewacin Najeriya ne, kasar da shugabanta yayi rantsuwa cewa zai jagoranci mutane ya ba su kariya.”

Ya zuwa ranar 20 ga watan na Afrilu,2026 wannan bidiyo ya samu wadanda suka kalla 3,500 (views) da wadanda suka sake yada labarin 880 (reshares) da masu tsokaci (comments) 700 da masu nuna sha’awa (likes)1,300.

Masu amfani da shafin da dama sun mayar da martani kala-kala daya daga cikinsu Oduwoga Oluwaseun, ya rubuta cewa “ zan iya cewa dukkaninku mahaukata ne, har yanzu kuna da lokaci na kallon cewa an ware Musulmi da Kirista. Kuma wani bangare ne na matsalar kasar.”

Wannan ma da ke amfani da shafin Ray Akomor, ya rubuta cewa, “mafita guda daya ce a yi juyin-juya hali babu wani dan siyasa da zai iya tseratar da wannan kasa.”

Harry Duku ya kara da cewa “wadannan masu aikata kisa sune dai gwamnatin Tinubu ta yafewa aka mayar da su cikin al’umma. Wace irin gwamnati ce wannan?”

Shi kuwa a nasa bangare Ibrahim Hesham yayi tambaya ne da cewa “ta yaya kuka sani cewa wadanda aka doka mabiya addinin Kirista ne?”  

DUBAWA ta ga dacewar gudanar da bincike kan wannan da’awa ganin irin matsalar tsaro da kasar ke fama da ita, haka kuma ana ganin irin wannan da’awa na iya harzuka zukatan al’umma, a yada fargaba da rikici na addini.

Tantancewa

DUBAWA ta sake kallo na tsanaki kan hoton wannan bidiyo da aka yada , mun kuma gano bidiyon da ke zama mai tsawo kimanin mintuna biyar da dakika bakwai. An kuma wallafa wannan bidiyo a shafin Tawadah HTV a 2023 da taken labarai na Hausa.

Da muka fassara taken labarin daga Turanci sai ya nunar da cewa “Yadda fasinjoji a jirgin kasa Abuja zuwa Kaduna suka sha duka bayan an yi garkuwa da su.”

Da muka kara zurfafawa da bincike sai muka ga irin wannan bidiyo da aka wallafa a shafin SaharaReporters a watan Yuli,2022 inda aka bashi take da cewa “BIDIYO: ‘Yanta’adda sun yiwa mutane bulala bayan garkuwa da su a jirgin kasa a hanyarsu ta tafiya daga Abuja zuwa Kaduna. 

A cewar rahoto wadanda aka gani a bidiyon fasinjoji ne da aka kama su a ranar 28 ga Maris,2022 a cikin jirgin kasa a lokacin da suke kan hanyarsu daga Abuja zuwa Kaduna.

DUBAWA ta kuma gano cewa ita ma kafar yada labaran Arise TV ta yada wannan hotuna daga bidiyon na watan Yuli, 2022 inda aka ba da rahoto na garkuwa da fasinjoji da suka sha gallazawa a hannun ‘yanta’adda wadanda kuma suke yin barzana ga bangaren gwamnati.

A Karshe

Da’awar cewa ‘yanta’adda sun ware mabiya addinin Kirista a arewacin Najeriya tare da yi masu duka a watan Afrilu,2026 yaudara ce. Bincike ya tabbatar da cewa wani bidiyo ne da ya nuna mutanen da aka yi garkuwa da su a 2022, a lokacin da jirginsu ya kama hanya daga Abuja zuwa Kaduna.

Exit mobile version