Site icon Dubawa

BINCIKE: Mutuwar fararen hula, raunatawa da wasu labarai boyayyu a harin jirgin sama na yaki a Shiroro  

BINCIKE: Mutuwar fararen hula, raunatawa da wasu labarai boyayyu a harin jirgin sama na yaki a Shiroro  

A lokacin da shelkwatar rundunar sojan Najeriya ta yi watsi da rahoto da ke cewa an kashe fararen hula a harin jiragen sama da aka kai a ranar 10 ga watan Mayu,2026 a yankin Kusasu, da yankuna masu makotaka da su a karamar hukumar Shiroro ta jihar Niger ta bayyana da’awar da cewa karya ce ta kuma jajirce cewa wadanda aka hara ‘yanbindiga ne.

A binciken da kafar yada labaran PRNigeria ta gudanar ya nunar da cewa ta gano shedu da suka ci karo da da’awar sojojin cewa babu farar hula da aka kashe a lokacin harin.

Duk da cewa mai dauko rahoton bai samu damar shiga Kusasu ba, saboda matsalar ta tsaro dama yawaitar masu dauke da bindiga a yankin, tattaunawa da aka yi da wadanda suka tsallake rijiya da baya a yayin harin da wadanda aka kashe masu mambobi na iyalansu da bayanan da aka tattara daga asibitin  Shalom Nursing Home and Maternity a New Zamba sun sake fito da bayanan da suka sauya labarin da aka bayar a baya.

Hoton wani yaro yana karbar magani a asibiti bayan kai farmakin ta jirgin sama. Wanda ya dauki hoto: Abdulsalam Baba Mahmud.

Mazauna garin da wadanda suka tsallake harin sun fadawa PRNigeria cewa jirgin saman yaki ya kai farmaki Kusasu bayan harin da ya kaiwa ‘yanbindiga, lamarin da ya jawo kisan fararen hula da raunata wasu daga cikinsu da wadanda suka gudu a kokari na neman tsira da ransu.Yadda suka yi bayani na kai farmakin sojan saman da daukar marasa lafiya zuwa asibiti da yadda wasu suka samu raunika dama rasa rayuka na wasunsu da ya biyo baya, hakan yayi daidai da bayanan da  Misis Polina Damidami, babbar jami’ar lafiya kuma darakta a asibitin Shalom Nursing Home and Maternity ta gabatar. 

Misis Damidami ta bayyana cewa ‘yansanda sun isa asibitin jim kadan bayan kai marasa lafiya suka tattara bayanai suka dauki hotuna kafin a fara kulawa da marasa lafiya. Iyalai da PRNigeria ta tattauna da su sun bayyana cewa su suka biyawa marasa lafiyarsu kudin jinya basu da wata masaniya kan wasu kudaden tallafi daga gwamnati.

PRNigeria ba za ta iya cewa ga hakikanin mutanen da aka kashe ba kasancewa shedun gani da ido suna bayyana mabanbantan adadi, yayin da abangare guda kuma matsalar tsaro ta hana a shiga yankin na Kusasu. Duk da haka shedu sun tabbatar da cewa fararen hula sun kasance cikin wadanda harin ya shafa wadanda daga bisani wasunsu suka rasu sakamakon raunika da suka samu. 

Ezekiel Bala.

Daya daga cikin wadanda suka tsira daga harin ya bayyana cewa harin ya faru ne yayin da wasu daga cikin mazauna garin na Kusasu suka fara komawa gida bayan da ‘yanbindigar suka janye.

“Lamarin ya faru ne kamar kiftawar idanu, kafin a kai ga lura mutane sun rasu wasu kuma sun jikkata sosai. Ni kaina ban san na samu rauni ba sai da wani ya ja hankalina cewa jini na zuba ta hannuna. Rana ce da ba za mu taba mantawa da ita ba,’’ a cewarsa.

Shedun da ya bayyana sun sha bambam da abin da shelkwatar sojoji ta bayyana, inda al’ummar gari suka kafe cewa wadanda lamarin ya shafa fararen hula ne a harin da aka kaiwa ‘yanta’adda..

Su kuwa dakarun tsaro sun ci gaba da jaddada cewa babu farar hula ko da daya da harin ya shafa, sun kawar da ‘yanta’adda ne.

Bin diddigin abin da ya faru

Sake bin diddigin abin da ya faru a ranar 10 ga watan Mayu, wanda ya hadar da jin ta bakin wadanda lamarin ya faru a gaban idanunsu, da bayanan da aka samu daga asibitin Shalom Nursing Home and Maternity da tattaunawa da iyalan wadanda lamarin ya faru da su da shugabannin al’umma.

A tsakanin 1 zuwa 3 ga watan Yuli mai dauko rahoto yayi tafiya zuwa Shiroro zuwa New Zumba, inda da dama wadanda suka samu raunika ake basu kulawar lafiya a asibitin na Shalom Nursing Home and Maternity. 

Allon sanarwa na Shalom Nursing Home and Maternity a New Zumba, inda wadanda suka samu raunika ke karbar magani. Mai daukar hoto: Abdulsalam Baba Mahmud.

A lokacin ziyarar, duk wadanda suka tsallake rijiya da baya an sallame su, duk da cewa PRNigeria bata samu damar tattaunawa da su baki daya ba, tattaunawa da wasu daga cikinsu da tattaunawa da babbar jami’ar jinya kuma darakta a asibitin na Shalom Nursing Home and Maternity da iyalan wadada ‘yanuwansu suka rasu sun taimaka wajen tattara bayanan hakikanin abin da ya faru bayan kai farmakin.

Mazauna garin sun fadawa PRNigeria cewa ‘yanbindiga dauke da makamai sun shiga garin na Kusasu da yankuna masu makotaka da shi, wannan ya sanya mazauna garin suka yi kaura, bayan sun janye jiki ne sai mazauna garin suka fara komawa gida bisa tunanin cewa matsalar ta kare, a wannan lokaci ne sai jirgin saman yaki na soja ya kai farmaki garin.

Hoton wani mashin da ya lalace bayan farmakin, wanda ya dauki hoto: Abdulsalam Baba Mahmud.

Mazauna wannan garin sun bayyana lokuta mabanbanta kan lokacin da aka kai harin dama yawan mutanen da harin ya halaka. Wasu na cewa harin ya faru da misalin karfe 6 na safe yayin da wasu ke cewa abin ya faru ne tsakanin karfe 8 zuwa 9 na safe.

Wadanda suka tsallake harin sun bayyana cewa babu wani daukin gaggawa da aka kai masu bayan harin. A maimaikon haka sai aka rika daukar marasa lafiyar daga Kusasu zuwa Shalom Nursing Home and Maternity a New Zumba a kan babura ana bin hanya mai wahala da sarkakiya mara kyau.

Hoton bidiyon yara da aka kashe a ranar 10 ga watan Mayu, an sakaye hoton.Wanda ya dauki hoto: Abdulsalam Baba Mahmud.

A cewar Misis Damidami, wadanda aka kai asibiti sune Faith Hassan da Victor Solomon da Dalili Iliya da Saitu Emmanuel da Talatu Ishaya da Auta Bala. Tace Auta Bala daga baya ta rasu tana karbar magunguna haka nan Talatu Ishaya ta rasu sanadin cutar da take fama da ita bayan an sallameta. Sauran mutane hudun sun rayu bayan harin.

Wadane bayanai suka fita daga asibiti

Bayanai da aka tattara daga asibitin Shalom Nursing Home and Maternity sun yi karin haske kan mutanen da aka basu kulawa bayan harin da aka kai ta jiragen sama.

Misis Damidami ta bayyana cewa marasa lafiyar sun fara isa asibitin jim kadan bayan kai harin jirgin sama, a cewarta mutane shida ne suka isa asibitin biyu kananan yara da biyu dattawa da biyu mata masu matsakaitan shekaru.

Daya daga cikin wadanda harin ya shafa yana karbar kulawar likitoci a asibiti, inda aka daura masa bandeji a kwankwasonsa. Wanda ya dauki hoto:  Abdulsalam Baba Mahmud.

Misis  Damidami tace ba da bata lokaci ba suka sanar da ‘yansanda wadanda daga bisani suka ziyarci wurin da lamarin ya faru, suka kuma dauki hotuna kafin a fara bawa marasa lafiyar kulawar likitoci.

“Duka ciwukan da suka samu akwai damuwa ta burbushin kai farmaki,” a cewarta marasa lafiyar an kawo su da raunika da dama da kuna akwai kuma burbushi na ababen fashewa a bangarori da dama na jikinsu.”

Tayi kiyasin cewa asibitin ya kashe kimanin miliyan daya da dubu dari biyu ₦1.2M don duba marasa lafiyar, kuma ma an rage kudaden ne saboda iyalan wadanda suka samu raunikan ba za su iya biyan kudaden ba baki daya. Tace guda daga cikin wadanda suka samu raunikan wacce nata yafi muni itace wata mata da wani bangare na cikinta ya bude ake iya ganin hanjinta. 

Wasu daga cikin  dabbobi da aka kashe a lokacin ruwan bama-bamai. Mai daukar hoto bdulsalam Baba Mahmud.

Wani likita ne da aka dauko yazo yayi mata aiki cikin gaggawa inda ya ceci rayuwar matar. Wata daga cikin marasa lafiyar mace ce mai ciki wacce ta samu rauni na kuna amma dai ba a rasa yaron ba, akwai kuma wani yaro da ya samu kuna sosai a fuskarsa.

Iyalai biyu, wadanda aka rasa biyu

Daga bangaren iyalan Auta Bala kwanaki da suka biyo bayan harin kokari ne na ganin an ceci rayuwarta, ta kasance guda daga cikin wadanda aka kai asibitin na Shalom Nursing Home and Maternity bayan ta samu raunika da dama. 

Duk da kokari na ganin an tseratar da rayuwarta, ta rasu tana karbar magani. Daya daga cikin ‘ya’yanta da bata so a bayyana sunanta ba, tace iyalan suna kallo jikinnata na tsananta babu abin da za su iya yi mata.

“Tana cikin matsanancin hali, mun yi ta addu’a ko za ta iya ci gaba da rayuwa amma ina sai da ta rasu.” a cewarta. “Mutuwarta ta barmu da kewa da matsi na tattalin arziki kuma har yanzu muna rayuwa cikin fargaba ta rashin tsaro a Kusasu.”

Hoto na sunayen wadanda aka duba a asibitin na Shalom Nursing Home and Maternity, wanda shugabar asibitin kuma babbar jami’ar lafiya Misis Polina Damidami ta rubuta da hannunta.Wanda ya dauki hoto: Abdulsalam Baba Mahmud. 

Har an samu karfin gwiwa a cikin iyalan Talatu bayan da aka dawo da ita gida daga karbar kulawar likitoci. Mai shekaru 57 ta dawo garin na Kusasu tare da iyalanta bisa fatan cewa ta hau hanyar samun waraka. 

Amma raunika musamman wadanda ta samu akanta sun ci gaba da tabarbarewa.

Danta mai suna Enoch Ishaya mai shekaru 25, yace sun ci gaba da kula da ita a gida saboda komawa asibiti abu ne mai wahala a wajen su.

Gidajen laka da aka lalata a harin da aka kai ta jirgin sama a ranar 10 ga watan Mayu. Mai hoto: Abdulsalam Baba Mahmud.

“Mun ci gaba da yi mata magani a gida a garin na Kusasu kafin daga bisani ta mutu. Ta samu mummunan rauni a kai da kafa,” a cewarsa. Ya kara da cewa sun kadu matuka da mutuwartata, bayan fatan samun kwarin gwiwa na tunanin za ta sake murmurewa.

Rayuwa bayan kai farmakin sojan na sama

A wajen wadanda suka tsira daga harin jirgin sama, ya nuna bude sabon babi na rayuwa, A lokacin da aka dauke su zuwa karbar magani a asibitin na Shalom Nursing Home and Maternity da ke New Zumba sun shiga tantama kan yadda za su biya kudaden asibiti ba tare da samun tallafi ba daga waje,

Hoto da aka sakaye na wata tsohuwar da ta samu raunika a harin da aka kai a ranar 10 ga Mayu.Wanda ya dauki hoto: Abdulsalam Baba Mahmud.

Abel Yahaya Habila, wanda diyar dan’uwansa na cikin wadanda suka rasa rayukansu, yace sun hada kudade don biyan kudin magani da ‘yanuwansu da suka samu raunika. Yace bisa kiyasi al’umma sun kashe kusan miliyan daya wajen ganin sun tseratar da ‘yan’uwansu, “Wadanda harin ya ritsa da su basu samu tallafi ba daga mahukunta ko bangaren sojojin, a cewarsa. “An bar komai a hannun iyalai da al’umma.”

Abdullahi Aliyu.

Dan shekaru 31 Abdullahi Aliyu, wanda shima haifaffen Kusasu ne, yace mazauna wannan gari sun shiga tashin hankali ba kawai saboda harin da aka kai masu ba, har ma da da’awar cewa wadanda harin ya ritsa da su ‘yanta’adda ne ba fararen hula ba.

“Muna kira ga gwamnati ta kara taimaka mana wajen kubutar da mu daga hannun ‘yanta’adda,” a cewarsa. “Maimakon abin da ya faru ana fadin cewa babu abin da ya faru.”

Aisha Shuaibu.

Mallama Aisha Shuaibu, wacce ta ga abin da ya faru tayi fatali da da’awar sojojin wacce tace babu farar hula da abin ya shafa.

“Mun gudu don tsira da ranmu, maimakon bibiyar ‘yanta’adda an yi ruwan bama-bamai kan fararen hula wadanda ke neman mafaka a kauye.” a cewarta.

Grace Samari

Misis Grace Samari, wata mazauniyar garin na Kusasu wacce ita ma ta tsallake harin ba tare da jin ciwo ba, tayi watsi da da’awar sojojin cewa an kwashe fararen hula daga yankin kafin kai harin.

”Babu wanda ya kwashe mu, tace mutane suna cikin kauyen lokacin da sojojin suka yi ta ruwan wuta a kauyen.”

Shiroro ba kawai anan ne aka yi irin wannan ba

Tsawon shekaru dakarun sojan Najeriya suna amfani da jiragen sama wajen kai hare-hare kan ‘yanta’adda da masu fashin daji, ko da dai cewa irin wannan hari na kawar da ‘yanta’addar da mayakan, wasu lokutan suna sanadi na rayukan fararen hula da raunata su.

Harin jirgin saman da aka yi a ranar 10 ga watan Mayu a Kusasu, ya kara jan hankali kan yadda harin soja kan yi sanadi na rayukan  fararen hula maimakon basu kariya.

An yi amfani da jirgin yaki na sojan Najeriya don ba da misali. Tushen hoto: Arise News.  

Yadda irin wannan lamari ke faruwa ke kara jan hankali na masu fafutukar kare hakkin dan’Adam da kungoyoyi na taimakon al’umma inda suke kira da a kara inganta yadda ake tattara bayanan tsaro da tabbatar da inda za a kai hari da gudanar da bincike mai zaman kansa bayan kai harin.

Wasu bincike na baya da PRNigeria ta gudanar da wasu kungoyoyi na taimakon al’umma da kafafan yada labarai sun nuna cewa irin wannan lamari ya faru a wasu jihohi da dama da suka hadar da Borno da Kaduna da Niger da Zamfara da Sokoto da Yobe da Adamawa da Nasarawa. 

Cikin wadanda aka ba da rahotanni akansa da yafi yaduwa shine na watan Janairu 2017 inda aka kai hari sansanin ‘yangudun hijira na  Rann, a jihar Borno, inda fararen hula da dama da masu aikin agaji suka rasa rayukansu; Haka kuma an kai wani harin a shekarar  2022 a yankin Kurebe a karamar hukumar Shiroro; a watan Disamba ma shekarar ta 2022 an kai harin ta sama a Mutumji a jihar Zamfara, sai harin da aka kai a Disamba,2023 a Tudun Biri na jihar Kaduna yayin da al’umma suka taru don hidima ta addini; sai harin da aka kai a kasuwar Jilli a Afrilu,2026 a jihar Yobe. 

Matsayar Gwamnati bata Canja ba

Bayan kammala rahotonta, PRNigeria ta tuntubi daraktan  sashin yada labarai na rundunar sojojin bangaren gudanar da ayyuka Manjo Janar Michael Onoja, don jin ko dakarun sojan sun cika alkawarin da suka dauka na gudanar da bincike kan rasa rayukan na fararen hula, amma babu wani abu sabo daga bangarensu.

Major General Michael Onoja, Daraktan kula da harkokin yada labarai a rundunar sojan Najeriya.Tushen Hoto: Shelkwatar Rundunar Tsaro a Najeriya. 

Matsayarsa na nan inda take.

“Mun yi watsi da bayanan, matsayarmu na nan inda take,” a cewarsa. “Babu gaskiya a wadannan rahotanni da ake gani a shafukan intanet, bincikenmu bai gano komai ba, idan muka samu wani bayani za mu kira manema labarai.”

Wannan bincike anyi shi a wani bangare na aikin bincike da kwarewa na OSINT a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya don taka birki ga bayanai masu tada hankali aikin da aka gudanar karkashin Cibiyar koyon Aikin Jarida da Kirkire-kirkire da Ci-gaba (CJID) bisa daukar nauyin Kungiyar Tarayyar Turai. An wallafa a karon farko a kafar yada labaran ta PRNigeria a ranar 2, ga Agusta,2026. 

Exit mobile version