Site icon Dubawa

Binciken wasu da’awa biyar kan tattalin arziki da Shugaba Tinubu yayi a jawabinsa

Fact-checking five economic claims in viral response to Tinubu’s speech

Tinubu, Shugaban kasar Najeriya. Asalin hoton: Jaridar ThisDay

Cikakken Sakon

Shuagaban Najeriya Bola Tinubu, yayi jawabi ga ‘yankasa a ranar 4 ga watan Agusta,2024 kwanaki bayan da aka fara zanga-zanga (nationwide protest) ta kwanaki 10 a fadin kasar. A cikin jawabinsa (his speech,) ya bayyana cewa gwamnatinsa ta himmatu wajen sama wa ‘yankasa saukin rayuwa, kasancewar gwamnatin ta zo da tsare-tsare cikin shekara guda da yayi a ofis. Ko da yake yayi da’awar cewa zanga-zangar na da alaka da siyasa ya bukaci masu yi su zama masu kyakkyawan fata ga gwamnatinsa ta yadda za su sha romon dimukuradiyya.

Duk da haka shugaban ya sha suka a kafafan sadarwar zamani , inda ake ganin cewa shugaban bai ce komai ba game da bukatun masu zanga-zanga, wasu ma na ganin jawabin nasa barazana ce a gare su maimakon lallashi da biyan bukatunsu.

Wani jawabi da ke zama martani ga jawabin shugaban da ya yadu a shafin WhatsApp shine da’awar cewa gwamnatinsa ta kashe makudan kudaden al’umma ga shugabanni ta yadda za su ci gaba da rayuwar nuna isa, Jawabin na nufin irin kudaden da aka kashe wa gwamnati inda ake diga ayar tambaya ganin halin kuncin tattalin arziki da ake fuskanta a kasa.

Duk da cewa DUBAWA bai gano asalin inda jawabin ya fito ba, an dai yada shi a shafin na WhatsApp. Charles Oputa (Charly Boy), sannan danfafutukar nan ya yada wannan jawabi a shafinsa na X   verified X. Da dama masu amfani da shafin Facebook suma sun yada shi kamar a wadannan wurare( here, here, here, here, da here. )

Yadda wannan da’awa ke iya rarraba kan al’umma da irin martani da ake yi ya sanya DUBAWA gudanar da bincike kan batun.

Da’awa ta  1: Wannan gwamnati ta kashe miliyan dubu 21 don gyara gidan matamakin shugaban kasa.

Yayin da aka ce aikin zai lakume miliyan dubu 21, an fara aikin ginin construction a 2010 lokacin Shugaba Goodluck Jonathan a lokacin ya ba da miliyan dubu 7. Anyi watsi da aikin 2015 har sai Janairu,2024 lokacin da Tinubu ya ba da miliyan dubu 14 don a kammala aikin da Kashim Shettima mataimakin shugaban Najeriya ya bude a ranar 7 ga watan Yuni,2024, wannann na nufin wannan gwamnati ta kashe miliyan dubu 14 ne kawai , sabanin miliyan dubu 21 da ake da’awa. Ministan babban birnin tarayya Nyesome Wike shima ya bayyana (revealed) cewa kudaden da aka samar za su hadar har da aikin gidajen ma’aiakatan fadar a Legas  da ma samar da fasahar sadarwa a Abujar da ofishinsa a Legas da gidajen suma na Legas.

Fact-checking five economic claims in viral response to Tinubu’s speech

Hoto da aka dauko na kudaden da za a kashe a aikin gyara gidan mataimakin shugaban kasa. Asalin hoto daga Economy Post

Binciken wasu da’awa biyar kan tattalin arziki da Shugaba Tinubu yayi a jawabinsa

Hukunci: YAUDARA CE. Gwamnati mai ci ta kashe Naira miliyan dubu 14 don kammala aikin gyaran gidajaen fadar shugaban da ke Legas da Abuja a kan kudi miliyan dubu 14, wanda ya hadar da samar da fasahar sadarwa a gidajen.

Da’awa ta 2: Gwamnati mai ci ta ba da naira miliyan dubu 70 don siyo manyan motoci kirar SUV ga mambobin majalisar dokoki.

Majalisar dattawan Najeriya ta amince da karin kasafi na kudi miliyan dubu N819 billion a ranar 28 ga Disamba,2022 lokacin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari. Wannan kasafi an tsara shi don ba wa ma’aikatu hudu ne: miliyan dubu 69 ma’aikatar ayyukan gona da miliyan dubu 704 ga ma’aikatar ayyuka da miliyan dubu 30 saboda ma’aikatar birnin tarayya da miliyan dubu 15.5 ma’aiakatar albarkatun ruwa.

A watan Yuli, 2023 Shugaba Tinubu ya mika wa majalisar dokoki bukata ta kari miliyan dubu 500 daga kasafin kudi na 2022  don rage radadi na matsin tattalin arziki dalilin cire tallafin manfetir. A wannan kasafi da aka yiwa kwaskwarima an ware miliyan dubu 70 don rage wahalar ayyukan ‘yanmajalisa 469 wadanda kowannensu zai samu mota Toyota Prado SUV wacce kudinta ya kai naira miliyan 130 da miliyan 160.

Binciken wasu da’awa biyar kan tattalin arziki da Shugaba Tinubu yayi a jawabinsa

Hukunci: GASKIYA CE. Ko da yake an amince da kasafin a 2022, Tinubu ya sake shigar da kudin ya kuma amince da kwaskwarimar kasafin na 2022. 

Da’awa ta 3: Wannan gwamnati ta amince da kashe Naira miliyan dubu 7 don gyara Dodan Barrack a Lagos. Mista Tinubu a ranar 1 ga Nuwamba 2023,  ya ware naira miliyan dubu 7 don yin kwaskwarima ga Dodan Barrack gidan shugaban kasa na Legas  wanda kuma majalisa ta amince a ranar 6 ga watan Nuwamba,2023, kudaden sune naira miliyan dubu 4 da naira milyan dubu 3 daya na bin daya. Kudaden kuma za su hadar da gyaran gidan shugaban kasa da mataimakinsa da suke a Legas.

Binciken wasu da’awa biyar kan tattalin arziki da Shugaba Tinubu yayi a jawabinsa

Hukunci: Gaskiya ce. 

Da’awa ta 4:  Wannan gwamnati ta ware naira miliyan dubu 3 don yin kwaskwarima ga gidan Aguda House

Binciken wasu da’awa biyar kan tattalin arziki da Shugaba Tinubu yayi a jawabinsa

Hukunci: GASKIYA CE. Kasafin kari ne cikin na 2023 wanda shuagaban kasa ya bayyana 2.17 trillion.  Naira miliyan dubu 3 za a yi amfani da ita ne don gyara gidan mataimakin shugaban kasa da ke Aso Rock Villa Abuja.

Da’awa ta 5: Wannan gwamnati ta ware miliyan dubu 5 don siyan motoci ga Shugaba Tinubu.

Kudi naira miliyan dubu 2.9 an ware (allocated) don siyan manyan motoci kirar SUV na shugaban kasa da wasu kudaden naira miliyan dubu 2.9 don wasu motoci da za a sake a fadar shugaban.

Sai dai abin lura a nan shine shi fa shugaban kasa guda daya ne tilo (individual member) a cikin tsarin shugabancin gwamnati. Wannan tsari ya hadar da ofishin shugaban kasa da mataimakinsa da shugaban ma’aiakata da sakataren gwamnati da mashawarci ga shugaban kasa kan harkokin tsaro  da sauran mambobi na majalisar zartarwa.

Binciken wasu da’awa biyar kan tattalin arziki da Shugaba Tinubu yayi a jawabinsa

Hukunci: YAUDARA CE. Kudaden da aka ware na fadar shugaban kasa ne, wanda shi shugaban kasa mamba ne a tsarin jagoranci na fadar.

A Karshe

Yayin da ‘yan Najeriya ke tsaka da ji a jika kan matsin tattalin arziki, gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na kashe makudan kudade kan wasu ayyuka da suke da alamun tambayoyi a tattare da su. Sai dai duk da haka wasu daga cikin da’awar da ake fadi kuma suke yaduwa kamar wutar daji ba gaskiya ba ne.

Exit mobile version