Da’awa: Wani mai amfani da X ya yi ikirarin cewa babu wani gwamna Bahaushe da ke kan mulki a Najeriya, yana mai cewa duk gwamnonin Arewa Fulani ne, sannan kuma Northern nigerian governors suna daga cikin wannan batu.

Hukunci: Yaudara ce. DUBAWA ta gano cewa akwai gwamnonin Arewa da dama da ba Fulani ba ne. Haka kuma, ikirarin cewa babu gwamna Bahaushe a kan mulki yana da sarkakiya saboda asalin Hausawa batu ne da masana tarihi da ilimi ke kallonsa ta hanyoyi daban-daban, ba kawai ta fuskar ƙabila ba.
Cikakken bayani
Tattaunawa kan zargin wasu ƙabilu da mamaye muƙaman siyasa a Najeriya na yawan bayyana a kafafen sada zumunta, musamman a lokacin da ake muhawara kan wakilci, tsarin rabon muƙamai da haɗin kan ƙasa.
A wannan yanayi ne wani mai amfani da shafin X, Dr Kalu, OON (@DrKalu_), ya yi ikirarin cewa babu wani gwamna Bahaushe da ke kan mulki a Najeriya, kuma duk gwamnonin Arewa Fulani ne.
Sakon da aka adana a nan yana cewa: “ Shin kun san cewa babu wani gwamna Bahaushe da ke kan mulki a Najeriya? Eh, duk gwamnonin Arewa Fulani ne.”
Zuwa ranar 10 ga Yuni, 2026, an kalli sakon sama da 334,000, an sake wallafawa sau 2,100 da kuma alamar so sama da 9,800.
Ikirarin ya haifar da muhawara tsakanin masu amfani da shafin, inda wasu suka ƙalubalanci maganar yayin da wasu suka goyi bayanta.
Wata mai amfani da shafin mai suna Felicity (@Fizzyalexa06) ta kalubalanci ikirarin, tana cewa “Muftwang na Plateau ba Fulani ba ne. Ka yi bincike sosai kuma ka daina yaɗa ƙarya da wata manufa.”
Sai kuma wani mai amfani da shafin, Shina (@ShinaToluoni117), wanda ya goyi bayan ikirarin, “ba wai kawai su ne mafi rinjaye ba, har ma ƙasar tasu ce. Fulani ba ‘yan asalin Najeriya ba ne.”
Arewacin Najeriya yanki ne mai ƙabilu masu yawa, kuma maudu’in kan ƙabila, wakilcin siyasa da asali kan jawo muhawara mai zafi a kafafen sada zumunta.
Saboda yadda sakon ya samu karɓuwa da kuma yiwuwar yaudarar jama’a, DUBAWA ta binciki ikirarin.
Tantancewa
DUBAWA ta duba asalin ƙabilun gwamnonin jihohin Arewacin Najeriya da ke kan mulki a halin yanzu. Binciken ya gano cewa akwai gwamnonin Arewa da dama da ba Fulani ba ne.
Misali, Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno da Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe dukkansu Kanuri ne.
Haka kuma, Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na Jihar Adamawa daga ƙabilar Margi yake, yayin da Gwamna Mohammed Umaru Bago na Jihar Neja ɗan ƙabilar Nupe ne.
Wadannan misalan sun yi hannun riga da ikirarin cewa duk gwamnonin Arewa Fulani ne.
Batun ko wane ne Bahaushe
DUBAWA ta gano cewa bangare na biyu na ikirarin yana bukatar ƙarin bayani, domin nazarin tarihi ya nuna cewa asalin Hausawafayyace ba abu ne mai sauƙi kamar yadda ake yi wa wasu ƙabilu.
Binciken masana ya nuna cewa al’ummar Hausawa sun samo asali ne daga cudanya da haɗewar al’ummomi daban-daban waɗanda daga baya suka rungumi harshe da al’ada iri ɗaya.
Wasu masana tarihi suna kallon Hausawa a matsayin haɗuwar al’ummomi daban-daban maimakon wata ƙabila guda mai asali ɗaya.
DUBAWA ta kuma tattauna da Salisu Ahmed, Farfesa a Sashen Harsunan Najeriya na Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato.
Ya bayyana cewa har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike da muhawara a tsakanin masana kan batun wanene Bahaushe, musamman dangane da ma’aunin da ya kamata a yi amfani da shi wajen tantance hakan.
A cewarsa, wasu ƙabilu kan narke cikin wasu al’ummomi sakamakon doguwar mu’amala da cudanya, har su rungumi harshe, al’ada da tsarin rayuwar al’ummar.
Salisu ya yi nuni da littafin “The Hausa Factor in West African History,” wani bincike kan tarihi da marigayi Farfesa Mahdi Adamu ya wallafa, wanda ya tattauna batun asalin Hausawa cewa ya wuce a danganta shi da jini ko zuriya kawai.
Ya ce littafin ya bayyana Hausa ta hanyar abubuwa kamar harshe, sutura, abinci, zamantakewa da sauran al’adun da al’umma ke tarayya a kansu.
“Akwai mutane da yawa da ba Hausawa ba ne ta fuskar asali, amma rayuwarsu gaba ɗaya ta Hausa ce saboda harshe da al’ada,” in ji Farfesa Salisu.
A Karshe
Ikirarin cewa duk gwamnonin Arewa Fulani ne ba daidai ba ne, domin akwai gwamnonin da suka fito daga ƙabilu kamar Kanuri, Margi da Nupe. Haka kuma, ikirarin cewa babu gwamna Bahaushe a kan mulki yana da sarkakiya kuma ya danganta da yadda ake fassara ma’anar Bahaushe. Saboda haka, ikirarin yaudara ce.