Da’awa: Wani mai amfani da shafin X na da’awar wai Najeriya ta kashe kusan biliyan 61 na dalar Amurka wajen taimakawa Afirka ta Kudu da gwagwarmayar da ta yi da mulkin wariyar launin fata.

Hukunci: Yawanci gaskiya ne! Majiyoyin tarihi da na ilimi sun goyi bayan wannan hasashen da ya kintata yawan kudin da Najeriya ta kashe kan gwagwarmaya da mulkin wariyar launin fata a Afirka ta Kudu kan biliyan 61 na dalar Amurka.
Cikakken bayani
Yayin da aka fara kai sabbin hare-hare kan ‘yan Najeriyan da ke Afirka ta Kudu har ya kai ga dawo da ‘yan Najeriya sama 250 gida, akwai da’awowi da dama suka bulla a kafofin sada zumunta na soshiyal mediya dangane da rawar da Najeriya ta taka wajen taimakawa Afirka ta Kudu da gwagwarmayar da ta yi da mulkin wariyar launin fata.
Ranar 23 ga watan Yuni wani mai amfani da shafin X @MrJamesKe, ya wallafa da’awar cewa Najeriya ta kashe kusan biliyan 61 na dalar Amurka wajen tallafawa Afirka ta Kudu sadda ta ke kokarin yaki da mulkin wariyar luanin fata a kasar.
Ya bayyana hakan ne ya na jaddada cewa “dalilin da ya sa tarihi ke da mahimmanci ke nan” . Labarin, a ranar 26 ga watan Yuni, mutane sama da 400, 000 sun kalla sun kuma yi ma’amala da shi, yayin da ya sami alamar like 150 wasu 200 kuma suka sake rabawa.
Wannan batun ya janyo ra’ayoyi mabanbanta, inda wasu ma tambaya suke yi ko a wancan lokacin Najeriya na da irin wannan karfin har da za ta iya bai wa wata kasa tallafi na irin wannan kudin.
Wani, @MaMhizzy, rubutawa ya yi, “Manyan makaryatan kasar ‘yan kwayar Najeriya ya kamata a karance su. Ke nan Najeriya ta baiwa Mandela biliyan 61 na dala a shekarun 1960 sadda jimilar abin da Najeriya ke samu kowace shekara ke zaman dala biliyan hudu kacal?
“Abin da Najeriya kan samu kowace shekara wato GDP dala biliyan 56.7 ne a shekarar 1993. A ina suka sami dala biliyan 61?” a cewar @Tygerzs.
DUBAWA ta kuma sake gano wani bidiyo a shafin Facebook daga kundin tattaunawa na Podcast na The MERC Podcast. Daga 26 ga watan Yunin 2026, mutane sama da dubu dari takwas da hamsin suka kalla. Wasu dubu 35 suka yi ma’amala da labarin yayin da ya sami tsokaci sama da 5,000.
Haka nan kuma DUBAWA ta lura cewa wannan da’awar ya na yawan bulla ne a duk sadda aka fara kai hare-hare kan ‘yan Najeriya a Afirka ta Kudu ko kuma dai duk sadda aka sami tashin hankali a tsakanin al’ummomin buyu. Ganin yadda batun ya sake zagayowa ne a wannan karon ma ya sa DUBAWA ta gudanar da binciken tantance gaskiyar lamarin.
Tantancewa
DUBAWA ta fara da bin diddigin mafarin wannan batu na dala biliyan 61 wanda kasida ce da Cibiyar Kula da Harkokin Kasa da Kasa ta Afirka ta Kudu (SAIIA) ta wallafa da taken “Giwayen Afirka na tafe hannu da hannu – Afirka ta Kudu da Najeriya.
Kasidar ta kwatanta Najeriya a matsayin daya daga cikin jagororin kasashen Afirkan da suka taimaka a gwagwarmayar yaki da mulkin wariyar launin fata, inda ta bayyana rawar da ta taka wajen kafa kwamiti na musamman na yaki da mulkin wariyar launin fatar ta Aparthied a Majalisar Dinkin Duniya, da ma kudaden da ‘yan Najeriya suka rika tarawa a matsayin gudunmawar dafawa wadanda suka kasance a bakin daaga a lokacin.
Bisa kiyasin da aka yi, lokacin da aka kammala mulkin a shekarar 1994, Najeriya ta bayar da dalar Amurka kusan biliyan 61
Wannan kiyasin bai ambaci wani kudin da aka tura kai tsaye ba, illa dai yadda aka kimanta wannan jimilar a matsayin kudi, tattalin arziki da goyon baya na diflomasiyya a shekarun da suka gabata.
Tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Nelson Mandela shi ma tabbatar da gudunmawar da Najeriya ta bayar. CIkin wani bidiyo na ziyarar da ya kai Najeriya a shekarar 1990 wanda aka wallafa a shafin YouTube na gwamnatin jihar Legas, Mandela ya mika godiyarsa ga gwamnatin Najeriya da mutanenta saboda tallafin kudi da goyon bayan da suka basu a gwagwarmayar da suka yi.
Ya ce Najeriya “ta kasance cikin wadanda suka fi kowa bayar da tallafi” ga masu gwagwarmayar nuna adawa ga mulkin wariyar launin gata da ma tallafin da aka rika baiwa daliban Afirka ta Kudu dan zuwa makaranta da ma tura likitoci, malamai da duk ire-iren manyan jami’an da suka bukata a wancan lokacin.
Ana iya samun karin bayani dangane da irin wanann gudunmawar cikin wani binciken da aka yi a shekarar 2020 wanda aka wallafa cikin wata kasida a shafin Taylor & Francis Online.
Kasidar ta ce Najeriya ta fara dafawa jam’iyyar ANC da ta PAC na masu rajin girka hadaddiyar kasar Afirka a shekarar 1961 sadda ta ke baiwa jam’iyyun biyu dala miliyan biyar kowace shekara har zuwa 1970.
Har wa yau, kasidar ta ce Najeriya ce ta girka gidauniyar samarwa Afirka ta Kudu kudi, mai suna Southern Africa Relief Fund (SARF) a shekarar 1976, Abin da daga baya aka zo aka fi sani da “Mandela Tax.”
Cikin watanni shidda, gidauniyar ta hada dala milyan 10 da rabi daga gudunmawar da dalibai, ma’aikatan gwamnati da duk sauran bangarorin al’umma suka bayar. Ya kuma kara da cewa takunkumin da aka sanya ya jawo mata rashin kusan dala biliyan 41, na kudin da ya kamata a ce ta samu daga man fetur.
A shekarar 2012, tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo ya tabbatar cewa ma’aikatan gwamnatin Najeria sun bayar da wani kaso na albashinsu ga gidauniyar ta SARF.
A Karshe
Majiyoyin tarihi sun bayar da hujjojin da suka goyi bayan kiyasin kudin da ake hasashe Najeriya ta baiwa Afirka ta Kudu dan taimaka mata da gwagwarmayar da ta yi da mulkin wariyar launin fata wato dala biliyan 61. Sai dai ya kamata a fayyace cewa wannan adadin ya hada da gudunmawar kudi da na tattalin arziki da ma na diflomasiyya a tsukin shekarun da suka gabata ba wai kudi ni aka dauka aka tura mata sau daya ba.
An hada wannan rahoton ne a karkashin tallafin horaswa na musammanna na tantance gaskiyar bayanai na Kwame Karikari da OSINT, tare da hadin gwiwar DUBAWA da Cibiyar nazarin fasahar da ke kwaikwayon dabi’un dan adam na AI da bayanan da ba daidai ba (DAIDAC) tare da tallafin Cibiyar Habbakawa da Koyon Sabbin Dabarun Aikin Jarida (CJID)