Site icon Dubawa

Da’awar cewa ‘yan bindiga sun kai hari a Lambar Charanchi a jihar Katsina, karya ce

Claim bandit attacked Lambar Charanci, Katsina State, false

Jihar Katsina. Asalin hoton: Sahara Reporters

Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook yayi da’awa cewa an kai hari a Lambar Chiranci a kan hanyar Kano zuwa Katsina inda aka kashe mutane biyu a garin.

Da’awar cewa ‘yan bindiga sun kai hari a Lambar Charanchi a jihar Katsina, karya ce

Hukunci: Karya ce. Babban jami’i mai kula da shiya (DPO) na Rimi ya bayyana cewa babu wani hari da aka kai a Lambar Chiranci a ranar da aka bayyana a rahoton.

Cikakken bayani

Wani mai amfani da shafin Facebook Kwamared Yarima Bk, yayi da’awa cewa wasu ‘yanbindiga sun kai farmaki a lambar Chiranci, a garin lambar Rimi a kan hanyar Katsina zuwa Kano, inda suka halaka mutane biyu a wannan yanki. 

Wannan wallafa kamar yadda ake iya gani an killace ta a nan, an wallafa ne a ranar 28 ga watan Yuni,2026, inda aka yi zargin cewa lamarin ya faru a daren ranar Lahadi, lamarin da ya haifar da rudani ga al’umma da ke zaune a wannan yanki dama matafiya da ke bin wannan hanya.

Duk da cewa wannan wallafa bata da wata hujja da za a dogara da ita , abin ya ja hankalin al’umma duba da irin kalubalen tsaro da ake fama da shi a jihar ta Katsina.

Ya zuwa ranar 29 ga watan Yuni,2026, wannan wallafa ta samu martani 1,300 da masu tsokaci 179 da wadanda suka sake yadawa 53 inda da dama masu amfani da shafin suka rika nuna alhini da fargaba kan abin da ya faru. 

Wani mai amfani da shafin na Facebook Ahmed Abubakar Sadiq, da yake alhininsa yace “Tabbas daga Allah muke gare shi kuma za mu koma.”

Sai wani kuma mai suna Sharhabi Sani, yace “wani abin takaici kuma shine sai ka gansu suna yawo da ababen hawansu. Allah dai Ya kawo mana zaman lafiya a kasarmu.”

Martanin da ake gani ya nuna cewa mutane da dama sun amince da da’awar ba tare da yin bincike ba a tabbatar da cewa abin da ake fada da gaske ne.

Duba da yanayin tsaro da ake fama da shi da kuma yadda labaran karya ke haddasa fargaba da tsoro, DUBAWA ta mayar da hankali wajen bincike don tabbatar da da’awar. 

Tantancewa

Domin tantance wannan da’awa, DUBAWA ta tuntubi al’umma mazauna Lambar Chiranci.

Abubakar Badamasi, da ke tuka babur na haya ko Okada da ke zaune a wannan yanki yayi watsi da wannan da’awar inda yace babu harin ‘yanta’adda da aka kai a wannan yanki da aka fitar da rahoton a wannan dare.

Haka shima Khalid Abdurrahman, manomi kuma mazaunin wannan yanki ya bayyana cewa wannan rahoto karya ne kuma mutane da ke zaune a yankin basu sheda ganin wani hari ba, ko kai harin bindiga kamar yadda mai da’awar a shafin Facebook ke cewa.

Domin kara bincikawa DUBAWA ta tuntubi CSP Gambo Isah babban jami’in ‘yansanda DPO na yankin na Rimi wanda ya karyata da’awar.

Wannan jami’in ‘yansanda yayi watsi da da’awar inda ya tabbatar da cewa ‘yansanda basu karbi wani rahoto ba na harin ‘yanbindiga ko harbe-harbe a Lambar Chiranci a wannan rana da aka bayyana.

Har ila yau DUBAWA bata samu wani jawabi ba daga rundunar ‘yansanda ta jihar Katsina babu kuma wata kafar yada labarai sahihiya da ta yi labari a kan lamarin. 

A Karshe

Mazauna wannan gari da babban jami’in shiya na wajen wato DPO sun yi watsi da da’awar cewa an kai hari a Lambar Chiranci da ke a hanyar Kano zuwa Katsina inda aka kashe mutane biyu. Wannan da’awa dai ta tabbata cewa karya aka zabga.

Wannan aiki an aiwatar da shi karkashin cibiyar koyon Aikin Jarida da Kirkire-kirkire da Ci gaba (CJID) tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai.  

Exit mobile version