Site icon Dubawa

Da’awar wai ana cigaba da tabka rikicin kabilancin tsakanin Fulani da Kambari a jihar Neja yaudara ce

Old Niger abduction video recycled to depict mass Christian kidnapping
,

Da’awa: Hausaland Magazine a shafinta na Facebook ta bayyana cewa a jihar Naje kabilun Fulani da na Kambari na rikici inda ana fargaban cewa an kashe mutane da dama a dalilin rikicin.

Hukunci: Yaudara ce. Rahotani sun tabbatar da rikicin kabilancin da ya shafi wasu kauyukan Fulani, Kambari da Bargawa da wasu bangarorin jihar Neja. To sai dai da ma can an dade ana fama da da ire-iren wadannan rikice-rikicen ba kwanan nan ne aka fara ba kamar yadda Hausaland Magazine ke fada ba sa’annan rikicin kabillancin ya shafi kabilu uku ne ba biyu ba.

Cikakken Labari

Hausaland Magazine a shafinta na Facebook a ranar 21 ga Agusta 2026 ta wallafa da’awar cewa kabilun Fulani da Kambari na rikici a jihar Naje inda ana fargaban cewa an kashe mutane da dama.

Da’awar da (aka saka a nan) ya nuna cewa “Yanzu : Rikici tsakanin kabilun Fulani da Kambari a jihar Neja. Ana fargaban an kashe mutane da dama”.

Zuwa ranar Laraba 26 ga Agusta 2026 mutum 212 sun nuna suna son da’awar, 119 sun mai da martani, 42 sun sake wallafa da’awar,.

Da’awar yt jawo ce-ce-ku-ce wajen mutane inda da’awar ke nuna kamar Fulani ne ke kai wa mutane hari a jihar.

Sani Karofin Arewa ya rubuta a shafin sa cewa “Fulani sun zama annoba a Najeriya da kuma ‘yan Najeriya. Kabilar Kambari na da ikon kare kansu. Fulani sun zama annoba ga Najeriya musamman a Afrika gaba daya”.

James J Fakayode a shafinsa na Facebook ya ce “Fulani kabila ce dake yi wa Najeriya barazana”.

Sam Okirigwe ya ce “kowace kabila na da ikon kare kansu daga kisan kiyashin da Fulini ke yi”.

A dalilin wannan da’awa ya sa DUBAWA ta gudanar da bincike domin tabbatar da gaskiyar lamarin.

Tantancewa 

DUBAWA ta gudanar da bincike domin gano rahotanin da aka fitar game da wannan rikicin kabilancin da ake yi a jihar Neja inda ta gano labaran da aka yi kan rikicin kabilancin da ake yi a kananan hukumomin Borgu da Agwara a jihar Neja.

Rahotan da gidan jaridar Vanguard ta wallafa ranar 15 ga Agusta 2026 ya nuna cewa mutum sama da 20 ne suka mutu a kauyen Kokoli dake karamar hukumar Borgu a dalilin rikicin da ya barke tsakanin wasu kabilu. Gidan jaridar ta rawaito cewa rikicin ya shafi kabilun Fulani, Hausa, Kambari da Bargawa.

Rahotan ya nuna cewa a dalilin rikicin mutum sama da 300 sun gudu sun bar gidajen su inda suke samun mafaka cikin dazuka wasu kuwa sun gudu zuwa Yauri da Ngaski dake jihar Kebbi.

Jaridun Sun newspaper, THISDAY da The Guardian a ranar 19 ga Agusta sun rawaito cewa rikicin kabilanci da ya barke tsakanin kabilun Kambari, Fulani da Bargawa dake kauyukan kananan hukumonin Agwara da Borgu sannan rikicin ya fara ne saboda fili. Rahotani sun nuna cewa rikicin ya yi ajalin mutum kusan 30 tare da lalata dukiyoyi da dama.

Rahotanin sun nuna yadda shugaban cocin darikan Katolika na dayoyisis din Kontagora kuma shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya rashen jihar Neja Bulus Yohanna ya yi kira ga kauyukan dake fama da rikicin kabilanci da mai da takobi su zauna lafiya da junan su.

Rahotani sun nuna cewa rikicin kabilancin da aka saka a Facebook rikici ne da ya dade ba rikici ne da ya barke a kwanannan ba kamar yadda Hausaland Magazine ta wallafa ba a shafinta ranar 21 ga Agusta 2026.

Babbancin rahotanin da aka samu shine yadda da’awar da aka saka a Facebook ya nuna cewa rikicin da ake yi a jihar Neja tsakanin kabilu biyu ne sannan rikicin ya auku a cikin kwanakin nan ne.

An samu tabbacin cewa rikicin ba tsakanin kabilu biyu ne ba kadai amma rikici ne tsakanin Fulani, Kambari da Bargawa.

A Karshe

Da’awar da Hausaland Magazine ta saka yaudara ce. Akwai tabbacin cewa ana rikicin kabilanci a jihar Neja tsakanin kabilun Fulani, Kambari da Bargawa a kananan hukumomin Agwara da Borgu dake jihar sannan rikicin an dade ana fama da shi ba kwanan nan aka fara ba.

Wannan bincike an gudanar da shi ne a karkashin shirin Cibiyar Bunkasa Aikin Jarida da Kirkire-kirkire (CJID) tare da tallafin Tarayyar Turai (European Union).

Exit mobile version