Site icon Dubawa

Da’awar wai gwamna Bago ya dauki daliban da suka kammala karatu kusan dubu 10 su yi aiki a ma’aikatun gwamnatin jihar Neja yaudara ce 

Claim Governor Bago employed nearly 10,000 graduates into Niger civil service, misleading

Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook user, Adamu Idris Manarakis, na da’awar ce gwamnan jihar Neja, Mohammed Bago, ta dauki wadanda suka kammala karatu su kusan dubu 10 su yi aiki a ma’aikatun jihar.

Da’awar wai gwamna Bago ya dauki daliban da suka kammala karatu kusan dubu 10 su yi aiki a ma’aikatun gwamnatin jihar Neja yaudara ce 

Hukunci: Yaudara ce! Takardun da suka daganci batun a hukumance wadanda DUBAWA ta gani sun nuna cewa gwamnatin Bago ta dauki mutane dubu biyar ne kadai ba dubu 10 kamar yadda ake da’awa ba.

Cikakken Bayani

Yawanci akan yi amfani da yawan mutanen da gwamnati ta baiwa aiki a ma’aikatunta a matsayin wani mizani na kwatanta irin hobbasar da gwamnatin ke yi wajen aiwatar da ayyukan da suka shafi al’umma kai tsaye ko kuma dai suka yi tasiri wajen inganta rayuwarsu musamman a jihohin da matasa ke fama da rashin aikin yi.

Ranar Asabar 4 ga watan Yulin 2026 wani mai amfani da shafin Facebook Adamu Idris Manarakis, ya wallafa wani batun da ke da’awar cewa gwamnatin gwamna Mohammed Bago ya dauki kusan mutane dubu 10 aiki a ma’aikatun gwamnatun jihar Neja.

Daga ranar Litinin 20 ga watan Yuli mutane sama da 210 sun yi ma’amala da shafin wasu 90 sun yi tsokaci kuma an sake raba labarin sau 35.

Wannan da’awar ta dauki hankali sosai a Facebook, inda yawancin wadanda suka yi ma’amala da shafin suka dauki labarin a matsayin gaskiya har ma suna mi shi kallon shaidar irin aikin da gwamna Bago ke yi a jihar, suna yaba masa da samar da ayyukan yi ga matasa da inganta ababen more rayuwa, ba tare da wani/wata daga cikin masu tsokacin sun yi tambaya kan sahihancin adadin ma’akatan da ake da’awa ya dauka ba.

Mohammed Naibicewa ya yi “Ya kamata mutane Neja su bayyana amincewarsu da gwamna saboda yunkurinsa.” ya kuma kara da cewa gwamna Bago ya “rage rashin aikin yi bayan da ya dauki matasa 10,000,” su yi aiki a ma’aikatun higar. Wani shi ma mai amfani da shafin Eedrees Zakaree, cewa ya yi, “ba za mu ki yabonsa ba,” Yayin da shi kuma Abdulkadir Ibn Yeruwa ya ce, “Kudos ga manomi, gwamna Muhammad Umar Bago.”

Ganin yadda wannan adadin abu ne da za’a iya tantancewa daga takardun gwamnati, amma kuma mutane sun dauki da’awar a matsayin gaskiya har ana yadawa a shafukan sada zumunta ne ya sa DUBAWA tantance gaskiyar lamarin.

Tantancewa

DUBAWA ta yi bitar kasidar da ake kira “Diary of Activities New Niger” a turance, Volume 2 (May 29, 2023 – May 29, 2025). Wadda kasida ce da gwamnatin jihar Nejar ke wallafawa a hukumace na duka nasarorin da gwamnatin Bago ta yi cikin shekaru biyun da ya ke mulki a jihar.

A nan ne muka ga cewa kawo yanzu mutane 5,000 ne kadai gwamnatin ta bai wa aikin yi.

A shafi na 369, a karkashin sashen da aka yi wa taken “Civil Service Reforms,” wato sauye-sauyen gwamnati, ya yi bayanin cewa, “An dauki daliban da suka kammala karatu 5,000 su yi aiki a ma’aikatun gwamnatin jihar Neja dan samun sabbin dabaru da kwarwwa a fannin ta yadda zai inganta ayyuka da tasirinsu.”

Da’awar wai gwamna Bago ya dauki daliban da suka kammala karatu kusan dubu 10 su yi aiki a ma’aikatun gwamnatin jihar Neja yaudara ce 

Hoton kasidar inda ta ke bayyana ainihin adadin mutanen da gwamnatin Bagon ta bai wa aiki a ma’aikatun gwamnatin jihar Nejar.

Wannan rahoton wadda ita ce ta gwamanti a hukumance ta ce mutane 5,000 aka bai wa aiki ba 10,000 kamar yadda ake da’awa ba. Haka nan kuma DUBAWA ta gano cewa wannan adadin ne ma’aikata a gwamnatin Bagon suke cigaba da maimaitawa.

Ranar 14 ga watan Satumban 2025, mai bayar da shawara na musamman ga gwamnan jihar Nejar kan kan harkokin da suka shafi kafofin yada labaran da ke amfani da yanar gizo-gizo, Abdullberqy Ebbo, ya wallafa haka cikin shafin Facebook wanda ya danganta da gwamnan a wata hirar da ya yi da TVC.

Abin da ya wallafa na cewa: “A jihar Neja mun dauki mutane sama da dubu biyar aiki a ma’aikatun jihar, abin da ba’a taba gani ba. Muna gina hanyoyi, da asibitoci kuma mutanenmu suna farin ciki da mu.”

Haka nan kuma, ranar 4 watan Yulin 2026, babban mai kula da huldodin gwamnatin da manema labarai na gwamnan, El-Hajj Alfa Bago, ya sake wallafa wani bayanin a shafinsa na Facebook daga Abdullahi Abubakar Abdullahi inda ya ce ta hanyar Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnati mutane 5,000 sun sami ayyuka na dindindin wadanda har kudin fenshow za su samu.

Mun kuma ga wani bayani a shafin Instagram wanda aka wallafa a shafin @zayyan01__ wanda bidiyo ne na gwamnan ya na cewa ya baiwa mutane 5,000 aiki, shi ma wannan mawallafin ya danganta labarin da tashar TVC.

Mun yi amfani da mahimman kalmomin dan bin diddigi labarin ko zai  kai mu ga ainihin hirar da aka yi da tashar TVCn da mawallafan suke bayani a kai amma ba mu ga komai ba.

DUBAWA ba ta ga wani abu da ya tabbatar mata a hukumance cewa daliban da suka kammala makaranta kusan 10,000 sun sami a a ma’aikatun jihar Neja ba.

A Karshe

Da’awar wai gwamna Bago na jihar Neja ya dauki ma’aikata kusan 10,000 yaudara ce. Duka bayanai da takardu da ma sanarwar da aka yi dangane da batun sun nuna cewa mutane 5,000 ne kadai aka bai wa aiki a ma’aikatun gwamnatin jihar Nejar.

Wannan aiki an aiwatar da shi karkashin cibiyar koyon Aikin Jarida da Kirkire-kirkire da Ci gaba (CJID) tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai.

Exit mobile version