Da’awa: wani mai amfani da shafin X ya wallafa wani bidiyon da ke da’awar wai yara ne ‘yan makaranta ke tserewa daga wata makaranta a Kano bayan wani harin bindiga. Wannan ya sa aka yi zargin cewa akwai alaka da school abduction.

Hukunci: Yaudara ce. Yayin da ba mu iya tantance daidai wurin da abun ya faru ba, hujjojin da muke da su sun nuna cewa ba Kano ba ne. Bacin haka kafofin yada labarai masu nagarta ba su yi wani labari makamancin wannan ba.
Wannan al’amari na school abduction yana bukatar a yi cikakken bincike don tabbatar da gaskiyar lamarin.
Cikakken bayani
Ranar 15 ga watan Mayun 2026 wau ‘yan ta’adda masu dammarar makamai sun afkawa makarantu uku a karamar hukumar Orire da ke jihar Oyo inda suka hallaka mataimakin shugaban makarantar suka yi awan gaba da wasu dalibai da mallamai yayin da suka bar al’ummar cikin wani yanayi na jimami da rudani.
Wannan lamarin ya yi sanadin koke-koke daga al’umma yayin da suke kira ga gwamnati da ta ceto duk wadanda abun ya shafa. Yayin da hakan ke faruwa, a waje guda kuma tsoro da fargaba na cigaba da kasancewa a sauran al’ummomin kasar, inda jami’an tsaro da ‘yan banga su kuma su ke kokarin kama duk wadanda ake zargi da kasancewa ‘yan bindiga ko ta’addan da ke boyewa a cikin daji.
Bayan harin ne wani mai amfani da shafin X @AJSMILE911, ya wallafa bidiyo (Wanda aka adana a nan) na wadansu daliban makarantar sakandare wai suna tserewa daga wata makaranta a Kano bayan da ‘yan bindiga suka kwashi wasu daliban tare da shugabana makaranta.
“Abin da ke faruwa yanzu-yanzun nan a jihar Kano. Wasu ‘yan bindigan da ba’a san ko su wane ne ba sun shiga wata makarantar gwamnati sun dauki shugaban makaranta tare da wasu daliban da ba’a san adadinsu ba,” mai amfani da shafin na X ya rubuta.
An sake yin wata da’awar irin wannan a shafin Facebook kamar yadda aka wallafa a nan. Daga 5 ga watan Yunin 2026, an kalli labarin sau 331,000, tsokacin ya kai 601 sa’annan mutane, 2,700 sun sake rabawa, an kuma sami alamar like 3,700 likes, kafin wasu 373 kuma suka adana.
Da suke mayar da martani dangane da da’awar, wasu masu amfani da shafin na X sun bayyana fargabarsu dangane da matsalar rashin tsaron kasar, yayin da wasu kuma su ki shakkar faruwar abin a jihar Kano.
“Allah sa dai wannan ba gaskiya ba ne. Lallai Najeriya na fama da mamaya,” in ji @Kingstonpk.
“Yarubanci suke yi sa’annan kuna cewa Kano,” In ji @s_a_ashraf argued.
“Wannan bogi ne fa,” thatgirloyin321 ya rubuta.
Domin takaita yaduwar irin wannan jita-jitar ne DUBAWA ta dauki nauyin tantance gaskiyar wannan lamarin.
Tantancewa
DUBAWA ta sanya bidiyon cikin manhajar tantance hotunan Google Reverse Image Search. Wannan manhajar ta hada mu da wasu hotunan da suka yi kama da wadannan a cikin wani bidiyon Facebook inda dalibai ke gudu yayin da wasu mata ke ihu cikin harshen yarubanci ta na cewa mutane ne ke yada bayanan karya suna cewa ‘yan ta’adda na mamayar ungwanni.
Duk da cewa ba mu iya tantance daidai inda wannan hargitsin ya afku ba, binciken da muka gudanar da mahimman kalmomi sun nuna cewa wasu makarantu a cikin garin Akure na jihar Ondo sun rufe sakamakon irin wadannan hare-haren. Ana iya ganin wadannan labaran a wadannan makalun na shafin Facebook, wato a nan, nan, da nan.
A waje guda kuma, jaridar Punch ta rwaito cewa rundunar ‘yan sandan jihar Ondo ta tabbatarwa mazauna karamar hukumar Odigbo da sauran al’umma cewa babu wani dan ta’addar da ke zaman wata barazana ga tsaron inda su ke.
DUBAWA ta kuma gano cewa, sabanin yanayin yadda al’adun yankin arewacin Najeriya ke kasancewa musamman wajen sanya kaya, babu macen da ke sanye da hijabi a cikin bidiyon.

Hotunan wasu mata wadanda ba su sanya hijabi ba
Haka nan kuma, mun sake gudanar da bincike na mahimman kalmomi dangane da harin da ake da’awar an kai jihar Kanon amma ba mu sami wani abu da ke da irin wannan dangantakar ba.
A Karshe
Wannan da’awar yaudara ce. Duk da cewa ba mu iya tantance takamaimai ko ina ne wannan harin ya faru ba, duk hujjojin da muka samu daga binciken ya nuna cewa ba Kano ba ne bacin haka babu ma kafofin yada labaran da suka yi batun cewa wani abu makamancin wannan ya faru.