Da’awa: Tsohon Sanatan Nijeriya, Dino Melaye, ya wallafa wani hoto yana ikirarin cewa ƴan bindiga dauke da makamai sun dawo da gawar Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya ga iyalansa a Katsina sannan suka tafi ba tare da wani ya tare su ba.

Hukunci: Yaudara ce. DUBAWA ta gano babu wata shaida da ke nuna cewa an yi irin wannan mika gawar. Haka kuma, hoton da aka yi amfani da shi wajen goyon bayan ikirarin an kirkire shi ne da fasahar AI.
Cikakken Bayani
Rasuwar Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya, tsohon Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro, ta ci gaba da jan hankalin jama’a bayan rahotanni sun nuna cewa ya rasu ne yayin da yake hannun masu garkuwa da mutane. An sace Janar Rabe tare da matarsa a Jihar Katsina ranar 30 ga Mayu, 2026. Wannan lamari na general rabe ya jawo hankalin jama’a, musamman yadda ya shafi harkokin tsaro a kasar. Bugu da ƙari, labaran da suka shafi general rabe na daga cikin manyan batutuwan da jama’a ke tattaunawa a yanzu.
A wannan yanayi ne tsohon Sanatan Nijeriya, Dino Melaye, ya wallafa wani hoto a Facebook yana ikirarin cewa ƴan bindiga dauke da manyan makamai sun kawo gawar marigayin ga iyalansa kafin su koma daji ba tare da wata matsala ba.
Sakon da ya wallafa ranar 14 ga Yuni, 2026, na cewa, “Ƴan bindiga dauke da manyan makamai sun mika gawar Janar Rabe jiya da safe a Katsina sannan suka nufi dajin Matazu da ke makwabtaka ba tare da an tare su ba! Wace irin ƙasa ce wannan???”
Hoton (an adana a nan) da aka wallafa tare da sakon ya kuma kunshi wani rubutu da Hausa wanda ke ikirarin cewa masu garkuwar sun saki matar Janar Rabe tare da mika gawarsa ga iyalansa.
Zuwa ranar 14 ga Yuni, 2026, sakon ya samu martani sama da 14,900, sharhi 4,300, da kuma yaɗa shi sama da 2,000.
Ikirarin ya jawo martani mai karfi daga masu amfani da shafukan sada zumunta.
Wata mai amfani da shafin, A-Sani Charity Hja, ta rubuta cewa “Allah Ya kawo karshen wannan gwamnatin Tinubu mai zalunci.”
Sai kuma Ozoms Ikewete da ya ce, “Sojoji kullum suna nuna karfinsu a Kudu maso Gabas inda babu matsala.”
Duk da haka, wasu sun yi shakku kan sahihancin hoton.
Kamar Luke de Young, wanda ya rubuta, “Ina ganin AI ne ya kirkiri wannan hoton.”
Saboda muhimmancin ikirarin da kuma yiwuwar tasirinsa ga yadda jama’a ke kallon matakan tsaro a ƙasar, DUBAWA ta binciki gaskiyarsa.
Tantancewa
DUBAWA ta yi nazari da ido kan hoton. Bincike kuma ya gano wasu kura-kurai da aka saba gani a hotunan da aka kirkira da AI.
Misali, mutane da dama da ke cikin hoton kamar ba su da wata alaka da juna. Yadda suke kallon juna yana nuna rashin daidaito, kuma babu wata alamar mu’amala tsakanin mutanen da ake zargin suna cikin wani yanayi na jimami da karbar gawar mamaci.
DUBAWA ta kuma lura cewa bakin bindigar daya daga cikin wadanda ake zargin ƴan bindiga ne kamar ya ratsa cikin akwatin gawar, wani kuskure da ake yawan samu a hotuna ko bidiyon da AI ta kirkira ko aka yi wa kwaskwarima ta hanyar fasahar zamani.

Hoton da ke nuna bindigar ta ratsa cikin akwatin gawa.
Bugu da kari, matar da aka nuna a matsayin matar marigayi Janar Rabe ba ta yi kama da matar Janar din da aka gani a bidiyoyin da suka rika yawo lokacin da suke hannun masu garkuwa ba.

Hoton matar Janar Rabe daga bidiyoyin da aka saki da kuma matar da ke cikin hoton da ake ikirari.
Domin kara tantance sahihancin hoton, DUBAWA ta sanya shi a manhajar gano hotunan da aka ƙirƙira da AI mai suna Hive AI.
Sakamakon binciken ya nuna yiwuwar kashi 68.2 cikin 100 cewa hoton ya kunshi abubuwan da AI ta kirkira ko aka yi wa kwaskwarima.

Sakamakon binciken Hive AI.
Haka kuma, wata manhajar gano AI mai suna ImageWhisperer ta nuna cewa akwai yiwuwar AI ce ta kirkiri hoton, lamarin da ya kara haifar da shakku kan sahihancinsa.

Sakamakon ImageWhisperer.
DUBAWA ta kuma duba rahotannin da suka shafi mutuwar Janar din.
A ranar 13 ga Yuni, 2026, Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da rasuwar Janar Rabe a hukumance.
A cikin sanarwar da Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Nasiru Mu’azu, ya sanya wa hannu, an bayyana cewa tsohon jami’in ya rasu ne sakamakon ciwon sukari da hawan jini yayin da yake tsare a hannun ƴan bindiga.
Sanarwar ta tabbatar da mutuwarsa, amma ba ta ambaci cewa ƴan bindigar sun fito sun mika gawarsa ga iyalansa ba.
Haka kuma, Hedikwatar Tsaro ta bayyana a wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labaran Tsaro, Manjo Janar Samaila Uba, ya sanya wa hannu cewa an yi kokari sosai wajen ceto Janar din tare da alkawarin kara matsa kaimi wajen yaki da masu aikata laifuka.
Sai dai sanarwar ba ta nuna cewa ƴan bindigar sun kawo gawar ga iyalansa sannan suka tafi ba tare da wata matsala ba.
DUBAWA ta kuma nazarci rahotannin da aka wallafa bayan sanar da mutuwar Janar din. Zuwa ranar 14 ga Yuni, 2026, rahotannin sun nuna cewa matar marigayin tana ci gaba da zama a hannun masu garkuwa da mutane, sabanin ikirarin da ke cikin hoton.
Yayin da hukumomi suka tabbatar da cewa Manjo Janar Rabe Abubakar ya rasu a hannun masu garkuwa da mutane, DUBAWA ba ta samu wani sahihin rahoto daga Hedikwatar Tsaro, Gwamnatin Jihar Katsina, hukumomin tsaro ko kafafen yada labarai masu inganci da ke tabbatar da cewa ƴan bindiga sun fito fili sun mika gawarsa sannan suka tafi ba tare da an tare su ba.
A wata hira da DW Hausa ta yi da Ishak Rabe, daya daga cikin ‘ya’yan marigayin, ya ce iyalan ba su da wani bayani kan yadda aka samu gawar.
“Gwamnatin jiha ce kadai za ta iya bayyana yadda aka samu gawar,” in ji shi.
A Ƙarshe
DUBAWA ta gano cewa hoton da aka yi amfani da shi wajen yada labarin cewa ƴan bindiga sun mika gawar Janar Rabe an kirkire shi ne da AI. Haka kuma, babu wata majiya ta hukuma da ta bayyana yadda aka samu gawar zuwa yanzu. Saboda haka, da’awar yaudara ce.