Ranar da na fara haduwa da Bella mai shekaru 26 na haihuwa, yamma ta riga ta yi, kuma Bella ta isa otel din da aka fi sani da Tuco’s Palace Hotel, ke nan, wanda wani bene mai launin ruwan ganye a Ogba, daya daga cikin kananan garuruwan da ke wajen Legas, dan yin karuwanci. Dandalin Telegram ne mafarin karuwancinta a shekarar 2023, sadda wata kawarta ta hada ta da wani shafin karuwanci a kan dandalin, kuma ya zuwa watan Afrilun 2025, Bella ta zama cikakkiyar karuwa. Karuwanci ko kuma ‘hookup’ yadda ake mi shi lakabi da turanci a Najeriya musaya tsakanin mutane biyu ta jima’i da kudi. A cikin wannan yanayi, ana samun karuwanci bisa dandalin da aka fi sani da prostitution on telegram.
Otel din mai suna Tuco’s Palace Hotel ya na barin karuwai su aikin su cikin walwala a cikin benensu na kasa da kuma wani gidan kulob din da suke mallaka. Dabarun kasuwancinsu masu sauki ne. Mazjen za su kashe kudi kan karuwan su sayi giya da sauran ababen sha a gidan kulob din daga nan sai su kama daki a otel din su sami biyan bukata ta jima’i. Ke nan riba biyu suke ci. Ana kiyasin cewa masana’antar jima’i ta duniya na samun biliyan 186 na dalar Amurka kowace shekara, kuma kusan kashi shida da rabi (wato about 6.45%) na wannan adadin daga Najeriya ya ke fitowa.

Hoton ciki da wajen Tuco’s palace hotel. Hakkin mallakar hoton: DUBAWA.
Bisa dukkan alamu Bella sananniya ce a Tuco’s palace hotel. Daga zuwa kowa ya fara kiranta, su na jira su yi magana da ita. Mintoci kalilan da shigarta Bella ta sami kwantoma ko kuma abokin ciniki. Nan da nan ta zauna kusa da shi cikin kulob din ba tare da sun ce wa juna uffan ba, sai dai kwalaben giyar da ke gabansu yayin da kowannensu ke rike da karar taba sigari, sai kuma karar sautin wakokin ke ya cike ko’ina
Na nemi wuri na zauna daga nesa, sai dai ban yi nisa sosai da Bella ba, a cikin kulob din. Da ma a wannan ranan ne wata kawa ta ta hada ni da ita har muka yi musayar lambobi. Dan haka sai muka fara hira ta WhatsApp dangane da abin da ta ke fiskanta a karuwanci a dandalin Telegram yayin da take zaune kusa da abokin cinikin na ta. Haka muka cigaba da hirar har mu ka kai ga fara tattaunawa ta kai tsaye a wasu lokutan.
A yanzu, prostitution on telegram na kara tasiri a cikin al’umma, yana ba da dama ga karuwai da kwastamominsu su hadu cikin sauki.
Yawanci Bella kan sami kwastamominta ne ta wani shafin sirri na karuwai a Telegram wanda ake kira “Obawole, Ogba, da Iju Ishaga,” an sanya ayoyi ta kowani gefe da hotannin furanni. Ba kamar yadda yawancin shafuka irin na karuwancin su ke rubuta kalmar “hookup” dan fayyacewa masu bukatar sani cewa suna taimakawa wajen samar da karuwai ba, shi wannan shafin ba shi da wannan inkiyar.

Bella ta na tallata sana’arta a cikin shafin. Hakkin mallakar hoton: DUBAWA.
Sunan wannan shafin daidai ne da sunan wani yanki a cikin The Ifako-Ijaiye da ke karamar hukumar Ikeja a jihar Legas. Babu tazara tsakanin wuraren sosai, kuma burin wannan shafin shi na hada karuwai da kwastamominsu da ke wannan yankin.

Daidai inda yankunan Obawole, Iju Ishaga da Ogba suka hadu a Legas. Hakkin mallakar hoton: Google Earth.
Shafin na sirri ne dan haka idan ba wai wanda ke amfani da shafin ne ya fada maka ba, ba za ka taba sanin ya na nan ba. Telegram na barin mutane su kirkiro shafukan sirri da mambobi kusan 200,000 kuma kowannensu zai iya wallafa hotuna da bidiyoyi da sauran abubuwa yadda suke so ba tare da an kayyade ba. ‘Yan uwa Pavel da Nikolai Durov suka kirkieo wannan manhajar suka kaddamar da ita a watn Disemban shekarar 2013. Yanzu a shekarar 2025 masu amfani da ita sun wuce biliyan daya kowani wata. Dandalin na kare sakonni gaba daya daga mai aikawa zuwa mai karba, abin da aka fi sani da end to end encryption da turanci, sa’annan ya na iya boye lambobin waya ya kuma hada tsarin na’ura mai sarrafa kai (ko kuma bot kamar yadda aka fi sanin shi da turanci) dan ya yi aiki a shafin kai tsaye. Wadannan fasalolin masu inganta bayanan sirri ne suka kara ba shi damar samar da shafuka irin na karuwanci kamar su Obawole Ogba da Iju Ishaga.
Bella ta taimaka mun na shiga shafin sa’annan ta nuna mun yadda zan iya samun kwastamomi kamar dai yadda ta ke yi. Ta karbi waya na ne ta na rubutu a cikin shafin ta na kuma fadin abin da take fadawa cikin shafin a madadi na:
“A halin yanzu, ina da lokacin saduwa na gajeren lokaci ko kwana da BJ (wato tsotson alzakari),” da rubuta ta kalle ni da girarta a sama tana so ta san ko na amince ni kuma na nuna amincewa na. Nan da nan ta tura sakon a madadi na tana gaya mun cewa zan sami kwastamomi ba da dadewa ba. Haka kuma aka yi. Nan da nan kwatamomi suka fara tura mun sakonni wasu ma don wutar ciki har kira na suka rika ui kai tsaye.
Kafin mu kammala tattaunawarmu, Bella ta yi mun gargadin cewa in yi hankali da masu kula da shafin ko kuma ‘yan admin masu kwadayi wadanda ke son karbar kudi wajen mata. Sunansa Cattea

Cattea ya na barazanar cire Bella daga shafin karuwancin na Telegram. Asalin hoton: DUBAWA.
Amfani da karuwai dan samun riba da kirkirar sabbin dabaru
Wata karuwar wadda na hadu da ita a Tuco’s Palace Hotel da ma can ta yi mun magana kan Cattea. Ita kanta sunarta na farko kadai ta fada ta shiga karuwanci ta shafin kafin Cattea ya hana ta shiga saboda ba ta biya shi abin da ya kira “zakka” ba. Sunarta Bibire: Ta karanto mun bakaken dan in rubuta sunar daidai a cikin wayata. Bibire ta fada mun yadda ta biyr N2,000 dan ta shige shafin da aka tantance. Ta kuma nuna mun resit dinta domin ta kagu ta fada mun gaskiya.
Ta ce abun ya zama matsala ne bayan da Cattea ya cigaba da tambayarta kudi a kai – a kai, har ma ya fara barazanar cire ta daga sahfin. Idan ya yi haka ba za ta iya tallata kanta ba bare ta sami kwastamomi. Ta ce ta biya shi N1,000 har sau biyu kafin ta ga cewa ya ishe ta ba za ta iya ba. Daga nan sai Cattea ya haramta mata shiga shafin, ta na magana ta na fusata muryarta na tashi yayin da take bayanin abun da ya faru da ita.
Kamar Bibire, Ella Johnson ita ma mamba ce ta shafin Obawole, Ogba, Iju Ishaga wadda ita ma aka rika ci da guminta, amma wannan karon sauran ma’aikatan admin din banda Cattea. Ella na cikin wasu shafukan na daban wadanda su ma suke hada karuwai da kwastamomi a wasu yankunan na Legas. Wadannan shafukan na sada karuwan da kwastamomi a unguwannin masu hannu da shuni ne. Ella ta biya N10,000 dan ta samu ta shiga wadannan shafukan: @lekkibeach, @ibejuLekki, da @ajahconnect; Sai dai nan da nan aka fara mata zamba anan karbar kudi daga wajenta. Cikin wata daya suka haramta mata shiga shafin suka ce sai ta biya N70,000 idan har ta na so ta cigaba da kasancewa a shafin.

Hirar Ella da jami’an shafin, resit dinta da yadda jami’an shafin ke bukatar karin kudi daga wajenta. Asalin hoton: Ella.
Ella na hasashen cewa masu kula da shafin mata da miji ne kuma suna karbar kudi yadda suke so ne dan sun san cewa ba za’a taba kama su ba.
“Abun na taba mun hankali, ‘yan kwanakin nan,” ta ce.
Baya ga karbar kudin da jami’an shafin suka yi mata, Ella ta kuma fiskanci wulakanci wajen wasu daga cikin kwastamomin da ta samu a Telegram. An taba zagin siffarta da kamaninta, an taba barinta a kan hanya, an kuma taba barazanar mata duka, abubuwan da duk su ka kara mata damuwa. Ta yi labarin yadda ta taba shiga motar hayar da aka caje ta N30,000 dan zuwa ganin wani daga cikin kwastamominta wanda kuma bayan da ta biya ta isa wurin, mutumin ya ki zuwa. Bacin haka, akwai kuma sadda ta ke ciniki da wani kwastoma wanda ya bukaci yin amfani da ita ta wurin bayan gida, ita kuma ta ce ya biya 250,000. Mutumin sai ya kwatanta ta da buhun kasusuwa ya ma ce idan da ido da ido suka hadu da ya kwade ta.
To amma yayin da mata irinsu Ella ke fama da irin wannan kalubalen na karuwanci a shafukan Telegram, jami’an da ke kirkiro shafukan suna kula da su kazamin riba suke ci. Baya ga karbar kudin da suke tilastawa jama’a, sukan kuma bukaci biyan kudaden kasancewa mambobi wanda kuma sukan bushi iska kawai su kara ba tare da wani dalili mai kwari ba. Duk da cewa Ella ta biya N10,000 kafin ta shiga shafin @ajahconnect, ni da na yi kokarin shiga N35,000 aka ce in biya. A halin da ake ciki kuma shafin na Ajah Connect mambobi 16,000 ya ke da su.
Shafin karuwancin da aka kora daga WhatsApp ya sami gindin zama a Telegram
Da yake akwai hanyoyin samun kudi daga budewa da ma kula da shafukan karuwanci a Telegram, akwai sauran kungiyoyin da ke taimakawa wajen tabbatar da hada-hada a irin wadannan shafukan a Najeriya bai daya, har da jami’o’i. Na irga kungiyoyi 86 masu yin irin wannan aikin.

Makulun duka shafukan da muka binciko tare da yankunan da su ke aiki a Najeriya. Hakkin mallakar hoton: DUBAWA.
Wasu daga cikin shafukan kuma sun tashi ne daga WhatsApp suka koma Telegram bayan da aka kore su. Daya daga cikin irin wadannan shafukan shi ne Olosho Connect Naija, inda maza suke zuwa su roki cewa a mayar da su kamar bayin jima’i yayin da su kuma mata suke zuwa su tallata bidiyon jima’i dan samun kudi. Wasu mambobin sukan tallata damammakin shiga fina-finan jima’i da ma jima’i da wadanda suka sauya jinsinsu.

Wasu daga cikin tallace-tallacen da aka yi a shafin Olosho Connect bayan an goge lambobin. Hakkin mallakar hoto: DUBAWA.
Manajan shafin, Henry Okimonye Otareh, ya bayyana mana cewa kungiyar ta fara aiki ne WhatsApp, amma bayan da aka kore su ne suka dawo nan kuma yanzu a shirye su ke su zama kungiya ko kuma shafin karuwancin da ya fi kowanne a Najeriya a kan dandalin na Telegram.
“Muna son mutane daga akalla kowani babban birni a Najeriya: Abuja, Legas, Fatakwal, Asaba, Owerri, Enugu, Umuahia, Uyo, Calabar,” a cewar Henry, inda ya ke kira ga mambobi da su taya shi cika burinsa ta hanyar raba makalar shafin da kowa, “hatta wadanda ke rayuwa a kananan garuruwa da kauyuka.”
Olosho Connect Naija yanzu ya sauya sunaye daban-daban kafin ya zabi wanda ya ga cewa ya fi dai-dai da burin da jami’an shafin suke so su cimma.

Bayanin da ke nuna lokacin da aka dauka ana sauya sunan shafin kafin aka kai ga Olosho Connect Naija. Hakkin mallakar hoton: DUBAWA.
Sai dai bayan da aka amince kan sunan, sai jami’an shafin suka bukaci mambobi maza su biya N5,000 zuwa asusunsu mai lamba Opay account: 9159563993, yayin da su kuma karuwai matan kudin da aka ce su biya ya danganta dan ya na iya kasancewa wani abu tsakanin N3,000 zuwa N20,000.

Hoton da ke nuna kudaden da ake amfani da su wajen gudanar da shafin na Olosho Connect Naija. Hakkin mallakar hoton: DUBAWA.
Matan dai dole sai an tantance su a matsayin karuwai. Kafin a tantance ni sai da na ba su hoton kai na, irin wanda da zarar an gani zai dushe. Wata mai suna June Din wadda ke mallakar shafin ce ta duba hoton. Mintoci biyat bayan nan, June ta yi amfani da tambarin tantance mai amfani da shafin Telegram ta tantance ni. Ta tantance ni a matsayin abin da ta kira “verified escort” wato dai karuwa. Wannan na nufin cewa yanzu maza za su iya yarda da ni a matsayin karuwa su kuma tuntube ni dan samun biyan bukatunsu a farashin da zan karba.

Hoton yadda na shiga shafin da yadda aka tantance ni. Hakkin mallakar hoton: DUBAWA
Na tambayi June irin matakan kariyar da aka sa dan kare matan wadanda aka tantance su a matsayin karuwai kuma ta ce mun babu.
“Wannan wajen saduwa ne, ba wanda zai iya tabbatar da kariyarka. Za ka hadu a karon farko da wanda baka taba gani ba, hadarin ke nan,” ta fada mun cikin murya mai tsauri yayin da ni kuma nan da nan hawaye suka cika a idanu na.
Yayin da masu shafin ba su daukar wasu matakai na kirki ko ma masu kwari wajen kare mambobinsu, suna amfani da dokokin kariyar Telegram wajen kare kansu. Da kyar wanda ke shafin zai iya daukar hoto, ko nadar maganganu ko kuma bayanai da wayar tarho. Ya kan kuma yi amfani da fasahohin da ke kwakwaiyon dabi’un dan adam irin su ChatKeeperbot, wanda ke taimakawa wajen cire sakonnin da ba’a bukata, da Safeguard, wadda fasaha ce ta tsaro. Duk sadda ka ke hira da kwastoma idan ka yi kokarin daukar hoton hirar da kuke yi a rubuce, zai sanar da shi! Bacin haka babu inda za ka latsa ka kai karar shafin kamar yadda ake gani a sauran shafuka. Ka na iya barin shafin amma ba za ka iya kai karar shafukan ba.
Labaran bogi sun yi kamari, jami’an shafin na amfani da hotunan tsiraicin mata wajen tallata jima’i
Da Henry ke kokarin kare sahihancin shafinsa na Olosho Connect Naija, a cikin wani bayanin da ya turo mana ta voicenote, ya yi da’awar cewa “karuwanci ne sana’ar da ta fi dadewa a tarihin dan adam,” ya kuma jaddada cewa “an kirkiro shafin ne dan ya cigaba da zama na dindindin.”
Sabanin da’awar Henry, bayanan tarihi sun nuna cewa sana’ar kera kayayyakin aiki ne sana’ar da ta fi dadewa a duniya tunda an fara ta kusan shekaru milliyan biyu da digo shidan da suka gabata. Batun cewa “karuwanci na zaman sana’ar da ta fi dadewa a duniya” ya fito ne daga wani maurbuci mai suna Rudyard Kipling, wanda ya kasance a karni na 19 cikin shekarar 1988, sadda jama’a suka rika mahawara kan dokokin da aka so gindaya masa.
Henry ya kuma yi zargin cewa mata sukan fi son yin jima’i idan har maza za su biya, domin dangantaka ta kan zo da dokoki da yawa wadanda yawanci sukan sanya mata cikin wani yanayi na damuwa. Sai dai wata kwararriya a fannin kiwon lafiya Elizabeth Adewale ta karyata wannan zargin “idan har mace ta kwana da wani ba ta samun wani damuwa.”
Bacin da’awowin Henry masu yaudarar jama’a, ya kan kuma yi amfani da tsiraicin mata wajen tallar jima’i ya na amfani da abin da ake kira Telegram’s Story Albums. Henry na da bidiyoyi tara masu nuna tsiraicin mata a shafin shi. Wasu daga cikinsu na dauke da tallar da ke cikin launin baki da fari ya na cewa: “Ina da mata a shirye daga ko’ina a Najeriya.” Dan haka ne ma na yanke hukuncin gano tushen daya daga cikin bidiyoyin bayan da na ga kamar wata ‘yar yarinya ce tsirara tana jujjuya kanta. Komai a bayyane ya ke in banda wani hoton barkonon tsidibi da aka sa aka kare fiskarta da shi.
Na yi amfani da waya na na dauki hoton shafin sai na sanya hoton cikin manhajar tantance mafarin hotuna na Google Reverse Image Search. A nan ne na gano cewa bidiyon ya fito daga wani shafin fina-finan batsar Najeriya ne, inda ake wallafa hotunan mata da ‘yan mata a-kai – a kai. Ban bayyana makalar shafin ko abin da ake kiran shafin ba bisa dalilai na kariya. Sai dai hoton ita ‘yar yarinya na dauke da kwatance kamar haka: “Hotunan tsiraicin ‘Yar Akwa Ibom Video Leaks.”
Wani gajeren bidiyon da aka tsakura daga wannan bidiyon shi ma ya bulla a shafin Facebook ranar 3 ga watan Yunin 2024. Mai amfani da shafin da bidiyon ya bulla Kopala chimz ya yi amfani da emojis masu hawaye ya rufe wasu wuraren da ke jikinta. Na kai karar bidiyon zuwa ga Facebook amma ba su cire shi ba. Iyakaci dai suka dauki matakin kare kananan yara daga ganin hoton insa suka yi bayanin cewa bidiyon ya karya dokokin da suka tanadar dan kare “abubuwan da kananan yara za su iya gani.”

Hoton tsokacin da Facebook ya yi bayan da na kai karar bidiyon. Asalin hoton: DUBAWA.
Baya ga amfani da hotunan tsiraicin mata dan tallata karuwanci. Henry ya na kuma safarar mata dan jima’i ya na kai su wuraren da ke ciki da wajen kasar. Daya daga cikin sakonnin da ya wallafa a shafinsa na Olosho Connect Naija da safiyar 17 ga watan Fabrairun 2025 na cewa:
“Idan har akwai mai sha’awar zuwa Ghana dan aiki, tura mun sakon kai tsaye ta DM yanzu-yanzun nan!” Sa’o’i kadan bayan haka, Henryn ta kuma sake wallafa wata bukatar ta daban. “Idan har akwai mai lokaci yanzu wanda zai iya zuwa Calabar kuma za ku iya tsotson alzakari, tura mun sako ana bukatar ku cikin gaggawa.”
Na tuntuntubi Henry dangane da aikin da ya tallata na zuwa Ghana ya kuma yi alkawarin cewa “zai kira ni.”
Dandalin saduwa tamkar abu mai salon rayuwa iri-iri
Telegram, a cikin manufofinsa na tabbatar da ‘yancin sirrin masu amfani da shafin, ya hana haramta wa masu amfani da shafin “gudanar da ayyukan da suka karya doka a yawancin kasashen duniya. Wannan ya hada da azabtarwa ko cin zarafin kananan yara, da saye da sayar da abubuwan da aka haramta.”
Wannan ne ya ba ni karfin gwiwar kai karar Olosho Connect Naija zuwa kamfanin Telegram ta email din tura korafe-korafe ranar 18 ga watan Janairun 2026, ina tambayarsu ko ayyukan wadannan shafukan sun karya dokokin Telegram, kuma idan haka ne wadanne irin matakai za su dauka wajen shawo kan matsalar kasasncewar irin wadannan shafukan.
Duk da cewa dandalin bai amsa ni ba, nan da nan suka cire shafin na karuwanci ranar 22 ga watan Janairun 2026

Bayanin Telegram kan abin da ya sa suka sauke shafin. Hakkin mallakar hoton: DUBAWA.
To sai dai abun bai kare ba. Mako daya bayan nan Henry ya sake bude wani sabon shafin karuwancin a Telegram da suna mai kama da na tsohon shafin ya kuma raba dan mutane sh shiga. Ni ma na sami gayyatar shiga shafin saboda an riga an tantance ni a matsayin karuwa a tsohon shafin.

Henry ya yi imanin cewa karuwar da ba’a tantance ba ne ta yi sanadin rufe shafin da aka yi. Asalin hoton: DUBAWA.
Mai rajin kare hakkokin mata Oluwafunmbi Ogunsola ta shawarci cewa, baya ga rufe wadannan shafukan da ke dandalin, ya kamata Telegram ta yi gargadin cewa duk wanda ya cigaba da karya dokokin dandalin za su haramta mi shi amfani da shafin dindindin.
“Ya kamata su cigaba da sanya ido kan kungiyoyin dan su tabbatar cewa jami’an shafukan ba su sake bude wani bayan sun rufe shafukansu ba,” a cewar Oluwafunmbi. “Idan suka karya dokar, cire su kawai ya kamata a yi dindindin.”
Rashin aiwatar da dokoki yadda ya kamata ke kara ta’azzara matsalar
Dokar hukunta laifuka ta Najeriya wadda aka fi sani da Penal Code a turance ta hana gudanar da karuwanci a yankin arewacin kasar, yayin da a wasu yankunan kudancin kasar kuma sassan 223, 224, da 225 na dokar hukunta miyagun laifuka ta han gudanarwa da ma daukar karuwai.Wannan haramcin ya hada da samar da wurare ko kuma kayayyakin da za su taimakawa jama’a wajen daukar karuwai a duk sadda suke so ko kuma daukar mata da ‘yan mata a shigar da su cikin aikin na karuwanci. Christiana Longe, wata mai aikin shari’a kuma manaja a Cibiyar Koyar da Aikin Jarida da Sabbin Dabaru na Cigaba ta yi bayanin cewa dokokin da suka shafi hukunta miyagun laifuka masu lambobin 222, 223 da 224 su ne suka haramta ayyukan shafuka irin su Olosho Connect Naija “domin gidajen karuwanci ne a yanar gizo-gizo.”
Sauran dokokin cikin gida wadanda suka hada da Dokar da ta hana Safarar Mutane da kuma manufofin kasa da kasan da su kuma suka hada da Dokar da ta hana kowani irin cin zarafi a kan mata wanda aka fi sani da CEDAW, wanda Najeriya ma ke daga cikin kasashen da suka sanyawa yarjejeniyar hannu, shi ma ya haramta wa mutane yin riba da matan da ke karuwanci, har da masu shiga tsakani, da masu bude gidan karuwan da ma wadanda ke safarar matan.
Domin ganin an kama Henry da June sun fiskanci hukunci, Na kai karar duk abubuwan da shafin Olosho Connect Naija ke yi zuwa ga Godwin Eyake. Godwin shi ne Shugaban hukumar da ke yaki da safarar mutane wato NAPTIP a jihar Cross River. Na kuma ba shi makalar shafin da suke amfani da shi ta WhatsApp tare da wani jami’in tsaro dan su ga yadda ake gudanar da abubuwan a zahiri. Daga nan sai na tambaye su ko wani irin mataki za su dauka.
To sai dai shugaban NAPTIP din na Cross River ya ce kasancewar shafin ba laifi ba ne kuma ba su karya doka ba. A cewarsa hukumar ta na iya shiga ne kadai idan har akwai hujjojin da ke nuna cewa ana cin zarafi “misali kamar ana kwace kudin da suka samu daga wurin karuwancin” Ya kuma kara da cewa hukumar za ta kuma iya sa baki idan har shi wanda ke daukar karuwan ya fara cin zarafin karuwan ta hanyar karban kudi a wurinsu bayan ya yi barazanar cewa zai wallafa hotunan tsiraicinsu.
Da ta ke mayar da martani dangane da wannan, masanin shari’a Dogo Joy ta yi bayanin cewa dokar musamman sashe na 223 (2) da 225 (B) ya riga ya bayyana cewa an hana maza taimakawa mata su yi karuwanci ko da suna karbar kudin ko ba su yi.
“Dokar ba ta ma ce sai ya karbi kudbi ba, bude gidan karuwanci da ajiye karuwai kadai sun isa su janyo mi shi matsala,” kwararriyar ta bayyana hakan cikin haushi ta kuma kara da cewa, “ko a yanar gizo ko kuma a cikin al’umma laifi laifi ne.”
Sai dai Joy ta nuna cewa hukuncin ya tsufa saboda a shekarun 90 ne aka kirkiro da dokar. Duk wadanda aka kama da laifi za’a ci shi tara ne kadai “tara na naira dari ko kuma ya yi wata daya a gidan yari ko kuma duka biyun,” Shawarar ta ita ce Najeriya ta kwaskware dokokin amfani da mata dan karuwanci saboda a samar da hukunce-hukunce masu tsauri.
Daga baya NAPTIP ta yi alkawarin daukar mataki
Bayan martanin Godwin na cewa ba zai dauki wani mataki ba, na kai karar shafin zuwa ga hedikwatar NAPTIP ta adireshin imel din da ya ke karbar korafe-korafe. Hukumar ta bakin darektan sashen kula da shari’a Ijeoma Mary Amugo, Esq. ta tabbatar mana da cewa ayyukan da shafin ke yi sun karya doka. Cikin wata wasikar da ta turo mana, hukumar ta yi alkawarin cewa sashen yaki da miyagun laifuka a kan yanar gizo za su gudanar da bincike a kai.
Prisca Iwendi, wata mai rajin kare hakkin mata, ta shawarci cewa NAPTIP ya samar da wani kwamiti na mutane wadanda za su sanya ido kan matsalar su kuma kama duk wadanda ke da shafukan karuwanci su hukunta su. Ta ce su kansu Otel-otel din da ke taimakawa karuwancin ya kamata a kama su a sa musu takunkumi ko kuma a rufe su baki daya.
Anna Fisher, wadda ke daga cikin wadanda suka kirkiro kungiyar Nordic Model Now, wadda kungiyar kasa da kasa ce da ke aiki dan dakile karuwanci, ita ma ta shawarci Telegram da ya dauki matakai masu kwari wadanda za su kawo karshen shafukan da ke tallata karuwanci.
“Wadannan shafukan sun habbaka masana’antar karuwanci,” a cewar Anna. “Dan haka mun yi imanin cewa rufe shafuka irin wadannan ne zai taimaka wajen dakile wannan matsalar.”
A ranar 23 ga Maris, sabon Olosho Connect Naija ya haɗa wani na’urar basirar da kwaikwayon dabi’un dan Adam (AI) mai suna Ban Protector cikin dandalin domin gano da kuma cire ’yan jarida. Bayan kwana huɗu, a ranar 27 ga Maris, Telegram ta dakatar da sahfi na “saboda zargi na da aika saƙonnin banza (spam),” kuma kofar da nake da ita zuwa hanyoyin karuwanci na Telegram ta rufe gaba ɗaya.
Bincike da Editoci
- Kemi Busari—Lead Editor
- Lois Ugbede— Sub-Editor
- Ropo Sekoni— Copy Editor
Bayanin Edita: Kuna iya karanta wannan labarin cikin harshen Yarubanci da Turanci. Haka nan kuma ku na iya ganin bidiyon a nan