Site icon Dubawa

Hoton bidiyon mutane na wawashe shinkafa a mota  ba a bayan nan aka yi shi ba

Footage of people looting vehicle with bags of rice, not recent

Image of Nigerians looting warehouses for government palliatives. Photo Source: Daily Post.

    Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook ya yada wani bidiyo (video) na mutane sun sa wawason buhunhunan shinkafa tare da da’awar cewa lamarin ya faru ne a baya-bayan nan a jihar Kwara.

    Hoton bidiyon mutane na wawashe shinkafa a mota  ba a bayan nan aka yi shi ba

    Hukunci: Yaudara ce! Wannan bidiyon tsohon bidiyo ne da aka yi shi 2023, kuma rahotanni na kafafan yada labarai sun nunar da cewa wannan lamari ya faru ne a Iwo Road Ibadan, ba a jihar Kwara ba kamar yadda mai da’awa ya bayyana.

    Cikakken Sako

    Tun bayan hawan mulkin Shugaba Bola Tinubu Najeriya ke fama da tarin matsaloli na tattalin arziki da suka hadar da hauhawar farashin kayayyaki a kasuwanni da ragewa naira daraja. Da zuwansa kan mulkin Najeriya shugaban ya cire tallafin manfetir (removed the fuel subsidy) abin da yayi babban tasiri a rayuwar ‘yan Najeriya  inda suka ga hauhawar farashin kayayyaki da ba a taba gani ba a sama da tsawon shekaru 18 (highest inflation rate in over 18 years.)

    ‘Yan Najeriya na ji a jika a dangane da wannan tsari, abin da ke barazana ga rayuwarsu, wannan shi ya janyo aka rika zanga-zangar kungiyoyin kwadago (labour unions) da koke-koke a fadin kasa (nationwide outcry).

    A ranar Laraba 30 ga watan Oktoba, 2024 wani mai amfani da shafin Facebook,  mai suna Mazi Ikegod, ya yada wani bidiyo da yayi zargin cewa wasu mutane ne a jihar Kwara suka sa wawa ta kwasar buhunhunan shinkafa a jihar Kwara.

    A wannan bidiyo an ga yadda mutane ke kokawa kowa na son ya dauki buhun shinkafar daga motar kirar bas ta dakon kaya  wacce kawai ta tsaya a kasuwa, an ga wasu mazauna yankin na fada kan mallakar buhun shinkafar , nan kuma sai aka hango direban motar cikin rudani bayan da ya ankara an yi masa fashi na kayan da ya dauko dako a motarsa kirar bas.

    Wannan wallafar an sa mata take labarin da cewa, “Tsadar rayuwa: Idan ba a yi wani abu cikin gaggawa ba Najeriya ta dauki hanyar shiga yanayi na rudani.”

    “A wannan karo ma al’umma a Kwara sun sace buhunhunan shinkafa a lokacin da aka kaita kasuwa za ka ga mutane biyar na kokawa a kokari na kwatar buhun shinkafa guda daya.”

    Wannan wallafa ta samu kimanin mutane uku da suka yi sharhi, wasu biyu kuma suka sake wallafawa, ya zuwa ranar Alhamis 31 ga watan Oktoba,2024.

    Wannan da’awa kuma an ganta an wallafa a shafin X kamar a wadannan wurare (here, here, da here) da shafin Facebook.

    Wannan wallafa ta jawo bazuwar yaduwar labaran karya, don haka DUBAWA ta ga dacewar tantance wannan da’awa.

    Tantancewa

    Mun gudanar da nazari kan wannan bidiyo don gano asalin bidiyo ta (Google Reverse Image) sakamakon ne ya kaimu ga wadannan shafuka na Facebook (here da here) wanda aka wallafa a ranar 12 ga watan Satumba,2023. A wannan bidiyon an bayyana cewa lamarin ya faru ne a Ibadan..

    Domin kara bincikawa DUBAWA ta ga wani irin wannan bidiyo a shafin Instagram a irin wannan rana a shekarar 2023 kamar yadda yake a shafin na Facebook.

    Hanyar tantance hoto ma ta (Reverse Image Search) ta kaimu ga wannan bidiyo a shafin TikTok duk da cewa babu rana da aka nada, akwai sharhi da aka yi a kansa a tsakanin ranakun 14 ga Satumba da 16 shekarar 2023, abin da ya ci karo da cewa bidiyon sabo ne.

    DUBAWA ta kuma gudanar da bincike ta hanyar amfani da wasu muhimman kalmomi a google kan batun, inda ta gano rahoto da kafar yada labarai ta The Spectacles ta wallafa, a cewar kafar yada labarin lamarin ya faru ne a Iwo Road a birnin Idaban a ranar 10 ga watan Satumba, 2023 a lokacin da wata mota dauke da buhunhunan shinkafa ta tsaya, sai dai mazauna yankin sun dauka wannan shinkafa wani bangare ne na irin shinkafar da gwamnati ke rabawa don ragewa al’umma radadi, don haka sai suka daka mata wawa suna kwasar kayan abincin da ke zama shinkafa a cikin motar kirar bas.

    Har ila yau ita ma kafar yada labarai ta Blueprint ta ba da wannan labari a ranar 12 ga Satumba, 2023. Haka kuma DUBAWA ta ga wani labarin a shafin bidiyo na YouTube wanda ke zama wallafar (Gist Hub Plus) a ranar 13 ga watan Satumba, 2023.

    Ga ma yadda taken labarin yake “Mota kirar bas makare da shinkafa an daka mata wawa a Iwo Road bayan da mutane suka dauka shinkafa ce ta rage radadi da gwamnati ta kawo wa al’umma.”

    A ranar 12 ga watan Satumba, 2023 ita ma kafar yada labaran VideoWheelsTV ta wallafa wannan bidiyo da ita ma nata taken labari.

    “Mota kirar bas makare da shinkafa ta tsaya a Ibadan mutane suka afka mata tare da satar kayan ciki.”

    Karshe

    Bincikenmu ya gano cewa bidiyon da aka wallafa ba sabon bidiyo ba ne, yana nan a shafin intanet tun a 2023, kuma ma wurin da aka dauki bidiyon a birnin Ibadan ne ba jihar Kwara ba kamar yadda me da’awa ke fadi.

    Exit mobile version