Asalin hoton: THE WHISTLER.
|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wata da’awa da aka wallafa a kafafen sada zumunta na yanar gizo ya nuna hotuna da bidiyo da suka nuna cewa sojojin Najeriya sun kashe wasu ‘yan bindiga a karamar hukumar Gumi dake jihar Zamfara.

Hukunci: Karya ce. Yayin da rahotani ke tabbatar da yadda sojoji suka kashe ‘yan bindiga da dama a Gumi, DUBAWA ta gano cewa hotunan da aka yi amfani da su, an dauke su ne a kasar Afrika ta Kudu inda jami’an tsaro suka kama wasu masu hako ma’adanai ba tare da izini ba kuma tun a shekarar 2022 aka dauki bidiyon.
Cikakken Labari
A ranar tara ga Yuli 2026 Mallan Abdulsalam Ahmed a shafinsa na X (@Abdul_Ahmad_) ya wallafa wasu hotuna da suka nuna yadda sojoji suka kashe mahara da dama a karamar hukumar Gumi dake jihar Zamfara.
Da’awar na cewa “An kashe mahara da dama jiya a karamar hukumar Gumi. Ci gaba da kokari, Sojojin Najeriya.
Zuwa ranar 10 ga Yuli 2026 wannan wallafa ya samu wadanda suka duba 253,000, masu nuna shi’awarsu 28,000, masu tsokaci 576, wadanda suka sake yadawa 679, wadanda suka saka alama 174.
Wannan da’awar ya jawo tsokaci iri-iri.
Wani Fubara-D shima a shafinsa na X (@FubaraD1) ya rubuta cewa ” Hakan na nuni da cewa rundunar sojin Najeriya ba sune matsalar ba amma shugabani da masu daukan nauyin muggan aiyukkan kungiyoyi irin haka.
Wani masanin falsafa (@Aboosman46) ya ce “Idan da sojoji za su rika ganawa da mahara irin haka da ba za a rika samun Labaran aiyukkan mahara ba”.
Daga nan kuma, Logic (@Mrofficial_10) ya nuna rashin amincewar sa da haka inda ya ce “Sojoji na da masaniyar haka?
A haka Kuma I rahim Garkuwa Danchadi a shafinsa na Facebook ya saka bidiyo mai tsawon sakkan 30 dake nuna yadda sojojin Najeriya suka yi batakashi da mahara a Gumi.
Bidiyon ya nuna motocin yaki da dama na sojojin bindigogin su na sakin wuta.
A ranar 10 ga Yuli 2026 wannan bidiyo ya samu wadanda suka duba 5,700, masu nuna shi’awarsu 195, masu tsokaci 12 da wadanda suka sake yadawa 20.
DUBAWA ta kuma gano hotuna da bidiyo da aka saka a Facebook a nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan da nan da irin wannan da’awa.
Ganin yadda aka yada bidiyon da hotunnan da tsokacin da suka jawo DUBAWA ta gudanar da bincike kan da’awan.
Tantancewa
DUBAWA ta gudanar da bincike domin tattance inda ta gano hotunnan daga wurin hako ma’adanan dake Losberg Kloof ne dake Westonaria,Lardin Gauteng dake Afrika ta Kudu inda sojoji suka gudanar da bincike domin kama masu hako ma’adanai ba tare da izini ba.
A wani rahotan da gidan jaridar News24 ya wallafa ya nuna cewa ofreshan prosper wata hadaddiyar kungiyar jami’an tsaro sun kama mutum 217 masu hako ma’adanai ba tare da izini ba a ranar 7 ga Yuli 2026.
Rahotan ya nuna cewa wadannan mutane da jami’an tsaron suka kama baki ne da suka shigo kasan daga kasashen Mozambique, Zimbabwe da Lesotho sannan da wasu mutum biyu ‘yan kasan Afrika ta Kudu.
’Yan sanda sun kama wasu mutane biyu da suke zargin sun da ajiye makamai da tallafawa bakin mutanen da suka shigo kasan ba tare da izini ba.
DUBAWA ta kuma gano wadannan hotunnan a Labaran da gidan jaridar YFM Ekurhuleni ya wallafa da Zagazola wadanda duk suka nuna cewa hotunnan an dauke su ne a kasar Afrika ta Kudu yayin da sojoji ke gudanar da aiyukkansu a maimakon sojoji yayin da suke gudanar da aiyukkan su a Najeriya. Binciken DUBAWA ya gano asalin inda aka fara wallafa wadannan hotunnan a shafin X na rundunar ‘yan sandan kasar Afrika ta Kudu SAPS.
“Hadaddiyar kungiyar jami’an tsaro #ofreshan Prosper sun kama mutum 217 a wurin hako ma’adanai dake Losberg Kloof a Westonaria”.
Hakan ya tabbatar cewa wadannan hotuna daga Afrika ta Kudu suke sannan basu da alaka da aiyukkan sojoji a jihar Zamfara.
Tsofaffin Hotunan Horar da Sojoji
DUBAWA ta gudanar da bincike domin tattance bidiyon mai tsawon dakiku 31 ta hanyar amfani da ‘Reverse Image Search’.
Sakamakon binciken ya nuna cewa an fara saka wannan bidiyo a Facebook ranar 20 ga Janairu 2022.
Da’awar ta ce “Rundunar sojojin Najeriya CS/VP3 da Dongfeng CSK 131. Sojoji a shirye suke bana”.
Wanda ya wallafa bidiyon ya ce bidiyon ya nuna yadda ake horar da sojoji kan harba bindiga da motocin yaki.
DUBAWA ta kuma gano rashin alakar wannan bidiyo da aiyukkan sojoji a jihar Zamfara a watan Yuli 2026.
Sai dai kuma rahotani sun tabbatar cewa rundunar ofreshan FANSAN YAMMA ta kai wa mahara farmaki a mabuyar su dake tsaunin Dutsen Gidan dake da nisan 17km bayan garin Gumi dake karamar hukumar Gumi.
Bisa ga bayanan da gwamnatin jihar ta bada ya nuna cewa sojojin sun kashe mahara kusan 300 a farmakin da suka yi ranar 9 ga Yuli 2026.
A Karshe
Hotunnan da bidiyo dake nuni da kashe mahara ‘yan bindiga a karamar hukumar Gumi jihar Zamfara karya ne.
Bidiyon an fara saka shi a yanar gizo a 2022 sannan hotunnan daga kamen da jami’an tsaron kasar Afrika ta Kudu suka yi a wannan watan Yuli
