Da’awa:Wani shafin Facebook, Mariam Ann TV, ya yada wasu hotunan bidiyo masu tada hankali na jikin mutane babu kai aka kuma nunar da cewa yana da alaka da dalibai da aka yi garkuwa da su a jihar Oyo.

Hukunci: Karya ce. Binciken DUBAWA ya gano cewa wannan hoto ba shi da alaka da garkuwa da daliban da aka yi a jihar ta Oyo a baya-bayan nan.
Cikakken Labarin
A ranar 2 ga watan Yuni, 2026 wani shafin Facebook mai suna Mariam Ann TV ya yada wani bidiyo da aka ajiye (link) nashi a nan wanda ta yi martani kan wasu hotuna da ta yi da’awar cewa suna da alaka da daliban makaranta a Oyo da aka yi garkuwa da su. Daya daga cikin hhotunan gawarwaki babu kai yayin da dayan ya nuna dalibai kwance a kasa.
A cikin bidiyon an ga yadda wata mata ke kokawa a turancin Pidgin tana cewa “yara ne da ba ruwansu sun kashe su.”
Wani mai amfani da shafin Facebook ya yada wannan bidiyo a martani da yayi kan wannan bidiyo.
Mun kuma lura cewa wannan bidiyo ya yadu a shafin WhatsApp, inda wasu suka rika yada shi a shafinsu.

Hoto na irin da’awar a shafin WhatsApp status.
Hoto na biyun na yara ne a cikin kayan makaranta wanda aka yada sosai a shafukan intanet wanda suna da alaka da garkuwa da aka yi da dalibai da malamansu a baya-bayan nan a karamar hukumar Orire ta jihar Oyo.
Ya zuwa ranar 3 ga watan Yuni, 2026 wannan wallafa ta samu sama da mutane 549,000 da suka kalla (views), shima bidiyon an kalla 3,100 (views), da yadawa (shares) 4,700 da wadanda suka nuna sha’awarsu (likes)15,100.
Wannan wallafa ta samu martani da dama.
Chinazo Reuben, yace “Lokacin da Nnamdi Kanu ke fada masu cewa za a zo wannan lokaci, shin sun yarda da abin da yake fada? Maimakon haka sai suka rika fada masa sunaye kala-kala. Yanzu ga abin da ke faruwa.”
Ita kuwa Queen Ijeoma Olu: tace shin hakan abu ne mai yiwuwa? Allah Ya kawo mana dauki.”
Wadeyiri A Dery, yace “A kalla yaran sun huta”
Shi kuwa Uche Chidiebere Kelvin: “idan har da gaske ne, mai zai hana a wallafa da cikakken bayani sai kawai a fadawa mai kallo cewa akwai hoto mai sosa zuciya?”
Oyinloye Segun, yace “Me nake gani, yara ne fa.”
DUBAWA ta gudanar da binciken gano gaskiyar wallafar da irin hadarin da ke tattare da ita da fargabar da hakan zai iya kawowa.
Tantancewa
Binciken hotunan ya nuna cewa hotunan basu da alaka da yara da aka yi garkuwa da su a Oyo.
DUBAWA ta bibiyi bidiyon mutanen da aka yanke masu kai sai ta ganshi tun a Nuwamba 2024 An dauki hoto daga bidiyon da aka gani a shafin Goresee.
Irin wannan bidiyo ne kuma aka wallafa a ranar 20 ga watan Mayu,2025 inda aka wallafa a shafin na intanet tare da taken labari da ke cewa, Yakin kabilanci mai muni a Congo inda aka halaka mutane.”
Hoto na biyun ya nuna dalibai a cikin kayan makaranta sai dai hotunan basu zama bai daya ba, abin da ya janyo zargi shin wannan na gaske ne. Ganin hakan ce ta sanya DUBAWA gudanar da bincike ko an yi amfani da kirkirarriyar basira ta AI wajen hada wannan hotuna.

Hoto daga manhajar da ke nuna hoto ne na AI
Da aka yi amfani da manhajar gano asalin bidiyo guda biyu sun nuna banbanci da ke akwai, Content at Scale ya bayyana hoton da cewa kaso 91% nasa an kirkira ne daga AI yayin da kaso 9% ke zama mutum ne ya dauka, abin da ke nuni da cewa an hada ne kawai.
Daya manhajar kuwa ta Illuminarty ta nuna cewa kaso 3.6% ya nuna cewar akwai yiwuwar hoton an hada shine da AI.
A Karshe
Wannan hoto bashi da wata alaka da yaran da aka kama a jihar Oyo. Bincikenmu ya nuna cewa daya daga cikin hotunan tsoho ne daga rikicin da ya faru a Jamhuruyar Dimukuradiyyar Kwango yayin da daya hoton kuma anyi amfani da manhajar kirkirarriyar basira ne ta AI wajen hada shi.
Don haka da’awar karya ce. Wannan tabbas ya nuna yadda mutane suke yada labaran da ba haka suke ba a yada abin da zai harzuka zukatan al’umma musamman a yanayin da aka yi garkuwa da daliban na Oyo.