Site icon Dubawa

Hotunan rabon ɗan kamfai mai tambarin hoton Gwamnan Kano, ƙarya ce!

Mata dauke da ‘yan kamfai. Mallakar hoto: FB/Gistreel.

Mata dauke da ‘yan kamfai. Mallakar hoto: FB/Gistreel.

Da’awa: An yaɗa hotuna da ke ikirarin cewa Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, ya raba ‘yan kamfai na mata masu dauke da hotonsa a matsayin tallafi.

Hotunan rabon ɗan kamfai mai tambarin hoton Gwamnan Kano, ƙarya ce!

Hukunci: Karya ce. DUBAWA ta gano cewa an sauya hoton, inda aka dora hoton gwamnan a jikin ‘yan kamfan ta hanyar fasahar gyaran hoto.

Cikakken Bayani

Wani hoto da ke yawo a Facebook, Instagram da X ya janyo ce-ce-ku-ce bayan masu amfani da kafafen sada zumunta sun yi ikirarin cewa Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, ya raba ‘yan kamfai  gana mata masu dauke da hotonsa a matsayin wani shirin tallafi mata.

Hoton ya nuna wasu mata suna daga ‘yan kamfai da ake zargin an saka hoton gwamnan a jikinsu.

Hotunan sun jawo martani daga mutane da dama, inda wasu suka yi wa gwamnan ba’a, yayin da wasu suka bayyana lamarin a matsayin amfani da mukamin gwamnati wajen yada farfaganda ta siyasa.

Wani mai amfani da Facebook kuma tsohon ɗan jarida, Ojudu Babafemi, ya wallafa hoton tare da bayyana cewa lamarin na nuna yadda siyasa ke kara lalacewa.

“Lokacin da aikin gwamnati ya koma wasan kwaikwayo, aka mayar da mutunci tamkar kayan talla, sannan shugabanci ya koma abin neman suna kawai, hakan yana tayar da tambayoyi masu muhimmanci kan abubuwan da muka fi bai wa muhimmanci,” in ji shi,

Wani mai suna Adebiyi Fashoyin kuwa ya yi sharhi da cewa, “wasannin kwaikwayo na ban-dariya da hauka”.

Ganin yadda hoton ya yaɗu da kuma tasirin siyasar da ke tattare da shi, DUBAWA ta gudanar da bincike kan sahihancin ikirarin.

Tantancewa

DUBAWA ta gudanar da binciken ta manhajar neman hoto ta Google da kuma nazarin fasahar hoto domin gano asalin hoton.

Binciken ya gano cewa an cire hoton ne daga wani bidiyo da Fatima Nasir, wadda aka fi sani da Teemah Cool, ta wallafa. Fatima fitacciyar mai amfani da TikTok ce kuma mai goyon bayan Gwamna Yusuf, wadda aka fi dangantawa da tafiyar siyasar “Gida-Gida” a Kano.

Asalin bidiyon ya nuna wasu mata suna daga ‘yan kamfai yayin wani taron siyasa a Kano. Sai dai binciken ya nuna cewa babu hoton gwamnan da ake gani a cikin hotunan da suka yadu a cikin asalin bidiyon ba.

Hotunan rabon ɗan kamfai mai tambarin hoton Gwamnan Kano, ƙarya ce!

Hoton da aka zaƙulo daga asalin bidiyon.

Wani bincike da aka gudanar ta manhajar SynthID Verifier ya tabbatar da cewa an yi wa wani bangare na hoton gyara ko kuma an samar da shi da fasahar Google AI.

Wannan ya nuna cewa an maƙala hoton Gwamna Yusuf a ‘yan kamfan ta hanyar amfani da manhajojin gyaran hoto.

Karkatar da Gaskiya

DUBAWA ta gano cewa ikirarin ya samo asali ne daga labarin da aka karkatar da gaskiyar abin da ya faru a wani taron siyasa.

An dauki asalin bidiyon ne a ranar 23 ga Afrilu, 2026 lokacin da magoya bayan Gwamna Yusuf suka taru domin tarbar Oluremi Tinubu yayin ziyararta Kano domin kaddamar da shirin Energise Commercialisation Now.

A yayin taron, an ji wasu magoya bayan suna waka ta siyasa suna yi wa Rabiu Kwankwaso ba’a. Ana kallon Kwankwaso a matsayin jagoran siyasa kuma tsohon ubangidan siyasar Gwamna Yusuf.

‘Yan kamfan da aka nuna a bidiyon wani bangare ne na ba’ar siyasa tsakanin bangarorin siyasa a Kano.

Sai dai daga baya an maƙala hoton gwamnan a jikin ‘yan kamfan, wanda hakan ya sauya ma’anar bidiyon zuwa wani ikirari na cewa gwamnati ce ta raba su a matsayin tallafi.

Abin da Teemah Cool ta ce

DUBAWA ta yi kokarin tuntubar Teemah Cool domin jin karin bayani, amma ba ta samu amsa ba zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Sai dai a wata hira da wasu shafukan yada labarai suka wallafa, fitacciyar mai TikTok din ta ce ita ce ta sayi ‘yan kamfan daga kasuwa da kanta.

Ta bayyana cewa hakan martani ne ga masu adawa da gwamnatin Kano, wadanda suka yi amfani da kalmar “falle daya” wajen nuna cewa Gwamna Yusuf zai yi wa’adi daya ne kacal.

A Ƙarshe

Hoton da ake yadawa da ke ikirarin cewa Gwamnan Jihar Kano ya raba ‘yan kamfai masu dauke da hotonsa ga mata karya ne.

Exit mobile version