Site icon Dubawa

Nipah Virus: Wace cuta ce, ya take bazuwa. shin me yasa ta dauki hankali

Nipah Virus: What it is, how it spreads, and why it matters

Hoton Jemage. Asalin hoton: UKHSA Blog

Kasar Indiya ta tabbatar da bullar sabuwar cutar Nipah virus a jihar Gabashi ta West Bengal. Kasar ta bayyana rahoto na bullar wannan cuta sau biyu a wannan  kasa da ta himmatu wajen fadada batu na lafiya a yankunan na Asiya.

Wannan lamari ya ja hankali kan sabon halin da ake ciki a dangane da cutar a fadin duniya. Lamarin da ya sanya kasashe da dama suka kara tsaurara bincike a tasoshin jiragen samansu, hukumomin lafiya ciki har da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ta sanya cutar ta Nipah a matsayin aba ta farko da za a mayar da hankali a kanta kasancewar tana jawo mummunar cuta hadi da mutuwa tana kuma bazuwa tsakanin al’umma.

Duba da kallon batu na hakki da ya rataya a wuyan  DUBAWA na ilimantarwa  kan abin da ya shafi yada labarai. ta shirya gudanar da bincike da ilimantar da jama’a kan abubuwan da ya kamata su sani a game da wannan cuta da hanyoyi da al’umma ya kamata su bi don kare kai.

Me ake nufi da cutar ta Nipah Virus? 

Nipah virus (NiV) cuta ce da ake samu da daga dabbobi ma’ana ana yada ta daga dabbobi zuwa dan’Adam. An gano wannan cuta a tsakanin shekarun  1998–1999 lokacin da aka samu cutar ta barke tsakanin manoma da ke kiwon aladu a Malesiya, tun daga wancan lokaci a ke ci gaba da samun bullar cutar nan da can daga yankin Kudu maso Gabashi da kudancin yankin na Asiya musamman a yankin Bangaladash da Indiya.

Wannan cuta dai an fi samunta a jikin jemage mai shan kayan marmari musamman jinsin Pteropus. Akwai tarin shedu da suka nunar da cewa cutar ta Nipah virus na kama wasu dabbobi kamar aladu da karnuka da kyanwa ko mage da akuya da tunkiya da doki.

Wannan cuta ana mata kallo na mai hadarin gaske saboda tana jawo cutittika tana kuma jawo rasa rayuka wanda ya kan kai kaso 40–75%, ya danganta da yadda cutar ta barke da kuma yadda aka kaiwa masu cutar dauki.

Najeriya dai bata taba ba da rahoto na bullar wannan cuta ba ta Nipah virus, amma fahimtar yadda wannan cuta take da yadda take bazuwa abu ne mai muhimmanci.

Daga ina ne aka fara samun cutar ta  Nipah virus?

Jemagu da suka fito daga iyalan Pteropodidae, musamman samfurin Pteropus sune suke dauke da wannan cuta  Nipah virus suna dauke da cutar duk kuwa da cewa basa nuna alama ta rashin lafiya, mutum kuwa na daukar cutar ne idan ya hadu da tsuntsun da ke dauke da cutar ta hanyar abincin da ya sanyawa yawunsa ko kuma yayi masa fitsari kamar ruwan zaki da ake fitarwa daga bishiyar dabino ko mutum ya taba dabbar da ke dauke da wannan cuta kamar aladu.

Ta yaya cutara ke bazuwa?

Nipah na bazuwa ta hanyar taba abun da ke zama mai ruwa-ruwa kamar miyau na baki ko yawu ko jini ko fitsari ko danshin da ke fita daga hanci na mutum ko dabbar da ta kamu da wannan cuta. A wasu lokutan ana samuwar bazuwar cutar a asibiti idan ba a daukar matakan kariyar da suka wajaba.

A baya-baya da aka samu barkewar wannan cuta a Bangaladash da Indiya wannan kwayar cuta ta Nipah virus ta yadu tsakanin mutum da mutum ta hanyar haduwa da abin da ya fitar ta baki ko ta fitsari da bayan gida.

A garin Siliguri, a Indiya a 2001, a samu yaduwar wannan cuta sosai a cibiyar kula da lafiya inda aka samu kaso 75% na wadanda suka kamu da cutar ko maa’ikatan lafiyar ko masu zuwa ziyara. Daga shekarar 2001 zuwa 2008, kimanin rabi na mutanen da suka kamu da wannan cuta sun sameta ne a  jikin ‘yanuwansu mutane lokacin da suke kokarin ba da  kulawa ga ,marasa lafiya.

Sabanin  COVID-19, Nipah ba a daukarta ta hamyar iska, ana bazata ne tsakanin mutane wanda kuma babar barazana ce ta fuskar lafiya.

Wadane alamu ake ji ake gani a matsayin na cutar?

Yadda cutar ke shigar mutum na farawa da yadda ba a ganin alamu, sannu a hankali sai  akai matakin yin numfashi da kyar har kuma a kai matakin da mutum zai zama bai ma san a inda yake ba.

Da fari mutum da ya samu cutar na nuna alamu da suka hadar da zazzabi da ciwon kai da ciwon gabobi da yin amai da bushewar makogwaro, wanda kuma sannu a hankali sai jin lalaci da jin jiri da fita daga hayyaci har ma abin ya kai da shafar kwakwalwa, wasu mutanen kan samu cutar yin numfashi da kyar ko a shiga hali na rai kwa-kwai mutu kwa-kwai cikin saoi 24 zuwa 48.

Lokacin da cutar ke dauka daga lokacin da mutum ya harbu da kwayoyin cutar na farawa daga kwanaki 4 zuwa 14. Ana kuma iya samu lokacin ya kai har kwanaki 45 kamar yadda rahotanni suka nunar. 

Wadanda cutar ta kama su sama-sama suna iya warkewa, sai dai akan dauki lokaci ana ganin kwakwalwarsu da matsala. Kaso 20 cikin dari na wadanda suka taba yin cutar suna tafiya da cutar da ta shafi kwakwalwa, kama daga wadanda suke sarkewa ko mutum ya sauya halayya. Wasu kadan da suka tsira daga wannan cuta sukan samu matsalar da kan shafi kwakwalwa inda za ka ga suna shiga yanayi na dimuwa.

Wadane hanyoyi ake bi don samar da kariya?

Ya zuwa yanzu babu magani ko allurar wannan cuta ta Nipah virus ko da yake Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bawa wannan cuta kulawa ta musamman a matsayin cuta da ake gudanar da bincike a kanta. Ana ba da shawarar ba da kulawa ta musamman ga wanda ya samu kai a wannan cuta ta yadda za a tabbatar da ya samu kulawa kan abin da ya shafi yin numfashi.

Babu wasu alamu na farko da za a iya cewa na mutum ya harbu da kwayoyin cutar ta Nipah, wani lokacin ma ba a iya gano wanda ya kamu da cutar wannan ke zama kalubale  yayin daukar matakai na kare bazuwar cutar da dakile bazuwarta a kan lokaci.

Kari kan wannan, akwai kuma duba yawa da inganci na samfur na cutar da lokacin da aka kai dakin gwaji wannan na iya shafar sakamakon.

Duba da abin da aka fahimta bayan barkewar cutar ta Nipah a 1999  a wani gidan gona da ake kiwon aladu, an rika tsaftace wajen da fesa maganin kashe kwayoyin cuta da wanke gonar wannan na iya taimakawa wajen dakile bazuwar cutar.

Idan aka samu labarin bullar cutar, ayi kokari a killace dabbobin da ke a wajen, ba tare da bata lokaci ba, a yanka dabbobin da ake ganin suna da cutar a kone a kuma binne su, wannan zai taimaka wajen dakile bazuwar cutittikan zuwa ga mutum.

Killace dabbobin da hana su motsi daga wata gona zuwa wata na taimakawa wajen rage bazuwar cutar.

Dauki da mutane ke kaiwa shine abu na farko, a mayar da kai wajen sa idanu ga alamun cutar da duk sarkaikiya da ke tattare da ita. 

Akwai allurai da dama da matakan yaki da kwayoyin cuta abubuwa ne da har yanzu ba a kammala aikinsu ba.

Me ya kamata mu yi yanzu? 

Kammalawa

Nipah virus cuta ce da ba kasafai ake ganin masu ita ba, Amma tana daga cikin manyan cutika da ke zama barazana a duniya saboda yadda take kashe mutane. gashi kuma babu maganinta ko allurar cutar. 

Exit mobile version