Site icon Dubawa

Bidiyon kubucewar fursunoni a Sokoto na karya ne

Viral video Sokoto prison break, false

Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook na da’awar twai wasu ‘yan ta’adda sun kubuce daga kurkuku bayan da wasu ‘yan uwansu suka yi amfani da abubuwa masu fashewa suka rusa bangon

Bidiyon kubucewar fursunoni a Sokoto na karya ne

Hukunci: Karya ce. DUBAWA ta gano cewa an yi amfani da fasahar AI ne wajen kirkiro bidiyon kuma babu kafofin yada labarai masu nagarta wadanda suka dauki labarin kubucewar fursononi ko mai dai hari a kan gidan yarin da ya kunshi ‘yan ta’adda.

Cikakken bayani

Wani mai amfani da shafin Facebook, @Southern Piller, na da’awar wai wasu ‘yan ta’adda sun kufuce da wani gidan kasso a Sokoto tare da tallafin wasu ‘yan ta’addan ‘yan uwansu wadanda ake zargi sun fasa bangon da ya ba su damar tserewa.

Wannan batun (wanda aka adana a nan) An yi shi ne cikin bidiyo mai taken “‘Yan ta’adda sun kubuce daga gidan yarin Sokoto da yawan su.”

Mun kalli bidiyon mai tsawon minti daya inda mu ka ga wani mutumi ya na tsokaci yayin da ya ke nuna wani bidiyon da aka dora a kan wanda ke bayar da labarin. Wannan bidiyon na biyun na nuna dandazon mutane suna tserewa daga wani ramin da aka huda a jikin bango.

Mai da’awar a cikin bidiyon ya yi bayani kamar haka, “Jama’a na, ya sake faruwa. Jiya ‘yan ta’adda sun tsere daha gidan yarin Sokoto. Bidiyon da ku ke gani a sama bidiyon da ya dauki abun ne sadda ya ke faruwa. Wadannan ‘yan ta’addan da daman su ne suka tsere. Kuma kun san yadda suka yi nasara? Wasu ‘yan ta’addan ne suka zo suka tayar da abubuwa masu fashewa suka huda bangon da ya kasance musu hanya. A lokacin da suka kai wannan harin babu wani ma’aikacin tsaron gidan yari a wurin.”

Mutumin ya cigaba da kwatanta abin da ya faru a matsayin misali na yadda ake tafiyar da abubuwa a Najeriya, inda ma ya kara da cewa kasar na barin ‘yan ta’adda su ci karensu ba babbaka, wato su cizarafin al’umma su kuma bar kurkuku cikin walwala.

Ranar shida ga watan Yunin 2026, mutane sama da 41,000 suka sanya alamar like, wasu 2,400 suka yi tsokaci, an sake raba shi sau 10,000 yayin da alkaluma ke nuna cewa an kalla bidiyon sau 500,000.

Mun yi nazarin wasu daga cikin tsokacin da aka yi dan gane abin da masu ma’amala da shafin ke tunani. Da yawa daga cikin su sun yi shakkar sahihancin bidiyon da ma inda ya fito.

@Tedman Golden tambaya ya yi, “Wa ya nadi bidiyon? Ina nufin wa ke daukan bidiyonsu yayin da suke kokarin tserewar?”

@Evelyn Nwaogu ita ma tambaya ta yi, “ta yaya aka yi suka kubuce ta bangon haka ba tare da an gan su ba?”

@ Jack Joseph shi kuma rubutawa ya yi cewa, “Me ya sa kafofin yada labarai na gargajiya ba su dauki wannan labarin ba? Ta yaya za mu tabbatar cewa wannan labarin gaskiya ne ba wai kawai abin da wani ya yi dan nishadi ba?”

Sauran masu amfani da shafukan sada zumuntan sun sa labarin a shafukan Facebook da na Instagram a  nan da nan.

DUBAWA ta yanke shawarar tantance wannan batun saboda sarkakiyar da ke tattare da shi da ma yadda jama’a su ke ma’amala da labarin ganin yawan mutanen da suka kalli bidiyon.

Tantancewa

DUBAWA ta fara da sanya makalar labarin cikin manhajar  InVID, manhajar da ke tantance sahihancin labarai a yanar gizo. Wannan manhajar ta cire wasu daga cikin hoton dan gudanar da bincike kan asalinsu. Sakamakon yin hakan ya fitar da labarai da dama inda aka yi amfani da wannan bidiyon amma kuma aka yi masa take daban-daban.

Mun sami nau’in bidiyon da ya fi nuna hotunan da kyau a shafin TikTok. Da DUBAWA ta yi bitan bidiyon mun lura da cewa akwai wani shafi a wajen Najeriya da shi ma ya wallafa bidiyon. Wannan ya kuma bayyana a yadda aka yi amfani da harshen larabci wajen dora bayanan bidiyon da kuma makalun da aka yo amfani da su kamar haka (“#dhiifama #arafa #mecca #ethiopian_tik_tok”).

Mun kuma kwafi bayanin da aka yi a shafin gabatarwar wanda ke cewa:

“Beeksisa garaa garaa viidi’oonis ta’u sagaleedhaan haala bareedaa ta’een isiniif hojjenna,”

Tun da ba harshe ne da muka sani ba sai muka sanya shi cikin shafin fassarar google wato Google Translate. Shafin ya bayyana harshen a matsayin harshen Oromo. Ga kuma fassarar bayanin: “Muna kirkiro tallace-tallace iri-iri ko da kuwa wani iri kuke so cikin kwarewa, mu na iya yin su ko da kuna so a bidiyo ne ko kuma sauti kadai.”

Mun kuma yi amfani da wajen fassara a shafin TikTok wanda shi ma ya bamu fassara daidai da wanda muka riga muka samu. Oromo daya daga cikin harsunan da ake amfani da su ne a kasar Ethiopia da wasu yankunan Kenya. Bacin haka wannan bidiyon ya sake bulla kan dandaloli da dama kuma dukkansu ba wanda ke da alaka da Najeriya kamar yadda za ku iya gani a wadannan shafukan, nan, nan, nan, nan da nan.

Bayan mun sake yin bita mun lura da cewa akwai wani rubutun da aka sa a bangon wurin da ake da’awar wai kurkukun ne. Abin da aka rubuta shi ne “PENITENCIARIA,” kuma kalma ce da nufin kurkuku a harshen Spanianci”

Ganin haka sai muka gudanar da bincike dan gano ko fursunoni sun tsere daga wani kurkuku a wata kasar da ke amfani da harshen Spanianci kawanan nan dan ganin ko watakila daga cikin ne bidiyon ya fito a maimakon Najeriyar da ake da’awa. Sai dai a nan ma binciken ya ci tura, ba mu ga komai kamar haka ba.

DUBAWA ta gano abubuwa da dama wadanda ba daidai ba a bidiyon da ya fita kyau. Alal misali, yadda mutanen ke motsi bai yi daidai da yadda dan adam ke motsi ba, kuma babu ramuka ko gibi sosai a jikin bangon da mutanen suka rika fitowa.

Bisa la’akari da wadannan abubuwan ne muka sanya hoton cikin manhajar da ke tantance ko an kirkiro hotuna da fasahar AI ne dan yin nazari. Mun fara da sa bidiyon cikin manhajar Hive AI, wanda ya bamu maki 95.6 wanda ke cewa ba mamaki an yi amfani da AI wajen kirkiro wannan bidiyon.

Bidiyon kubucewar fursunoni a Sokoto na karya ne

Sakamakon da muka samu daga manhajar  Hive .ai

DUBAWA ta kuma tantance bidiyon da manhajar da ake kira  Deepfake Detection da turanci, wato manhajar da ta ke iya gano duk hotuna da bidiyon da aka yi amfani da fasahar AI wajen kirkirowa. Nazarin ya nuna mana cewa akwai yiwuwar an hada bidiyon da irin wannan fasahar ne da kashi 80 cikin 100.

Bayanan da muka samu daga nazarin da aka yi dan gano ko an yi amfani da fasahar AI ne wajen kirkirowa.

Daga karshe, mun gudanar binciken gano ko akwai wasu rahotannin da ke labarin ‘yan ta’adda sun fasa kurkuku a Sokoto sun fito amma ba mu ga wani labari mai kamar haka ba.

A Karshe

DUBAWA ta gano cewa batun kubucewar fursunoni daga kurkukun Sokoto bayan da aka kai wani hari karya ce kawai. Bidiyon da aka yi amfani da shi wajen bayyana wannan da’awar an yi amfani da fasahar AI ne wajen kirkiro shi kuma kafofin yada labarai na gargajiya masu nagarta duk ba wanda ya dauki labarin wai an kai wani hari Sokoto.

Exit mobile version