A ranar Talata 9 ga watan Disamban 2025, Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ya aika dakarun sojan Najeriya zuwa makociyar kasar wato Jamhuriyar Bene, bayan da aka samu jita-jita cewa an yi juyin mulki a kasar.
Manyan kanun labarai a jaridu sune yunkurin juyin mulki ya gagara a wannan kasa da ke a Afurka, inda aka rika nuna bidiyo na dakarun soja na bayyana shirin juyin mulki kamar yadda aka nuna cewa an watsa labarin a kafar talabijin ta kasar.
Bayan fitar da sanarwar kasashe makota kamar su Ghana da Côte d’Ivoire da Najeriya sun aika dakaru don kwantar da hankulan al’umma. Sai dai kuma wasu rahotanni sun tabbatar da cewa sai bayan da Najeriya ta tura jiragen yakinta ne da dakaru don su kori sojojin da suka yi juyin mulki daga sansanin soja da shelkwatar gidan talabijin na kasar sannan ne aka samu zaman lafiya ya dawo.
An dai samu mabanbantan ra’ayoyi, ‘yan Najeriya da dama suna fitar da ra’ayoyinsu a shafukan sada zumunta a dangane da kai sojojin. Yayin da wasu ke magana kan batun matsalar tsaro ta cikin gida, wasu kuma na muhawara ne a dangane da batun cewa Shugaba Tinubu yayi gaban kansa ne ya tura sojojin ba tare da jiran amincewar majalisa ba.
A dangane da wannan shirin DUBAWA ya fitar da wannan bayani don fayyacewa ko shugaban Najeriya na iya tura dakarun soja wata kasa ba tare da jiran amincewar majalisar dattawa ba.
Matsaya a dokar Najeriya
Binciken da muka gudanar a DUBAWA an gano cewa a sake nazari na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya nunar da cewa shugaban kasa na da dama a hukumance ya tura dakaru zuwa wasu ayyuka na musamman a wajen Najeriya.
Duk da haka kafin fadar shugaban kasa ta ba da umarni sai ta tuntubi cibiyar tsaro ta kasa. Wannan shine tanadi da yake a Sashi na biyar na kundin tsarin mulkin Najeriya abin lura daga bangaren masu iko.
Duk da cewa amincewar majalisar dattawan ita ce babbar magana, shugaban kasa na iya ba da umarni a aiwatar idan aka tabbatar zaa samu amincewar majalisar dattawan cikin kwanaki bakwai.
Shin aika sojan na kan doka? Kwararru sun yi magana
A tattaunawa da AbdulHaqq Mutairu, lauya mai zaman kansa a Legas yace shugaban kasa na da damar ya aika dakaru zuwa kasa da ke zama makociyar Najeriyar ba tare da jiran amincewar majalisar dattawa ba, muddin ya tabbatar da cewa an tuntubi cibiyar harkokin tsaro ta kasa kafin amincewar majalisar dattawa.
Ya kara da cewa idan shugaban kasa ya gaza samun amincewar majalisar cikin kwanaki bakwai, wannan na iya bayuwa ya zuwa yin karan tsaye ga kundin tsarin mulkin Najeriya.
AbdulHaqq ya kara da cewa bawa shugaban kasa karfin iko da ya wuce kima ta damar aika sojoji ba tare da taka tsantsan ba, wannan zai bude kofa ta mulkin kama karya a tsarin mulkin dimukuradiyya.
“A nawa ra’ayin idan mutum ya aikata hakan na iya bayiwa a cire shi,,” a cewarsa.
Lauyan ya kara da cewa karkashin yarjejeniya mai lamba 2(4) ta Majalisar Dinkin Duniya ta ba da dama akai dauki na soja a wata kasa makociya idan aka sanar da kasar inda ake tsammni shugaban kasa ya fito yayi bayani.
Lauyan ya kara da cewa dukkanin kasashen biyu Najeriya da Jamhuriyar Bene sun rattaba hannu a yarjejeniya ta kasa da kasa kamar ta Kungiyar Gamayyar Afurka ta AU da Kungiyar Kawancen Kasuwanci ta Kasashen Afurka ta Yamma (ECOWAS) inda suka yi hadaka a harkoki da dama.
A cikin jawabin ya nunar da cewa fadar shugaban kasa tayi da’awar cewa abin ta yi na cikin hurumin hakkin da ya rataya a wuyanta karkashin sharudan kungiyar kawancen kasuwanci ta ECOWAS kafin daukar wannan mataki.
Wani lauyan, Moshood Ibrahim, ya fadawa DUBAWA cewa Najeriya har yanzu tana da karfin fada aji a tsakanin kasashen na ECOWAS inda take daukar nauyi kan abubuwan da suka shafi tsaro da shugabanci.
Haka kuma kungiyar ta ECOWAS na aiki ne kan tsarika na doka kamar yarjejeniyar da aka kulla a 2001 wacce ta mayar da kai kan dimukuradiyya da shugabanci nagari, abin da ke karfafa kungiyar ta yi martani kan duk abin da ya sabawa kundin tsarin mulki na shugabanci wanda ya hadar da juyin mulki na soja.
Yace “ECOWAS ta yi wani taro a baya-bayan nan a Abuja inda aka tattauna abubuwa irin wadannan inda kungiyar ta dauki alkawari na cewa ba za ta sake bari irin wannan abu na barazanar tsaro na faruwa ba a yankin.”
Moshood ya kara da cewa shiga yarjejeniya da ECOWAS ya hadar da ba da dama ga daukar mataki na bai daya ba tare ma da sanin kasar da abin ya shafa ba, don a maido da bin doka da oda karkashin kundin tsarin mulkin kasar da kaucewa duk wani hargitsi na siyasa.
Sai ya ba da misali kan yadda ECOWAS ta shiga kan lamuran da suka biyo bayan zabe a Côte d’Ivoire lokacin da shugaban kasar a wancan lokaci Laurent Gbagbo yaki amincewa da sakamakon zabe.
“Najeriya ta taka muhimmiyar rawa inda ta tabbatar da cewa an kawar da soja tare da maido da zababben shugaban kasa, a duniyar yau babu wata kasa da za ta zauna ita kadai don haka shigarmu kan abin da ya shafi kasashen yanki, kan abin da ya shafi tsaro na kan turba,” a cewar lauyan.
A Karshe
Binciken DUBAWA ya nunar da cewa kasancewar Najeriya cikin kungiyar kasashen yanki kamar Kungiyar Kasashen Afurka ta AU da ECOWAS, shugaban Najeriya na da damar daukar nauyi na tura dakarun soja zuwa kasa makociya don su maido da bin doka da oda kuma wannan mataki da zai dauka dole ya zama karkashin doka tare da samun amincewar majalisar dattawa.
Idan aka samu kuma umarnin aka fara bayarwa sai an sanar da cibiyar shari’a ta kasa kuma sai an sanar da majalisar dattawa cikin kwanaki bakwai, idan ba haka ba kuma matakin shugaban na iya zama yin karan tsaye ga doka.