Da’awa: Wasu masu amfani da shafukan sada zumunta da suka hadar da Sahara Reporters, sun yada wani bidiyo bisa da’awar cewa wani hari ne da aka kai kwana-kwananan a sansanonin soja guda biyu a Yobe, lamarin da ya jawo rasa rayukan sojoji da dama a jihar. Kamar yadda aka ruwaito a cikin Sahara Reporters news, wannan labarin ya jawo hankali daga masu bincike.

Hukunci: Yaudara ce. Duk da cewa akwai hari da aka kai a Buni Yadi da Buni Gari a karamar hukumar Gujiba ta jihar Yobe, bidiyon da aka yada na wani hari ne da ya faru shekaru biyu da suka gabata a jihar Zamfara.
Hukunci: Yaudara ce. Duk da cewa akwai hari da aka kai a Buni Yadi da Buni Gari a karamar hukumar Gujiba ta jihar Yobe, bidiyon da aka yada na wani hari ne da ya faru shekaru biyu da suka gabata a jihar Zamfara. Hakanan, Sahara Reporters news ta bayyana cewa rahoton ba daidai ba ne.
Cikakken Labarin
Kafar yada labaran ta Sahara Reporters ta yada wani bidiyo mai tsawon minti daya da dakika 35 a shafinsu na X kamar yadda aka (alkinta) a ranar 10 ga watan Mayu, 2026, inda aka nuna wasu mutane dauke da bindigogi suna tsalle da murna bayan lalata wata tankar yakin soja mallakar sojojin Najeriya.
A da’awar an rubuta cewa bidiyon ya nuna yadda mayakan Boko Haram suka kai farmaki sansanonin soja guda biyu a jihar Yobe, inda suka kashe ‘yansanda da dama da sojoji a garin da ke zama mahaifar gwamnan jihar ta Yobe Mai Mala Buni.
“DUBA: Boko Haram an kai farmaki a sansanonin soja biyu a jihar Yobe inda suka kashe sojoji da ‘yansanda a mahaifar Gwamna Buni,” kamar yadda wallafar ta nunar.
Wannan wallafa ya zuwa ranar 11 ga watan Mayu,2026 ya samu wadanda suka kalla 148,700 (views), da maratani 1,700 da sake yadawa a Tweeter 1,200 da tsokaci 360. A shafin Facebook kadai wannan wallafar ta yadu sosai kamar a wadannan wurare nan da nan da nan da nan da nan da nan da nan da nan da nan da nan da nan da nan.
A bangaren masu tsokaci a shafin Facebook wadanda ke ganin an yi nasara kan dakarun sojan a bidiyon, wani mai suna Rapar Sam yayi tambaya ne da cewa shin ba dakaru ne masu kai dauki na gaggawa daga bangaren soja da suka gaza yin abin da ya dace a irin wannan lamari?
“Ina jiragen sojan sama masu kai daukin gaggawa? Ina ganin gwamnatin Najeriya bata shirya yin nasara a kan ‘yanta’addar ba.”
Duk da haka DUBAWA ta ga wasu daga cikin tsokacin na cewa wannan bidiyo fa tsoho ne, kuma bashi da alaka da abin da ya faru a jihar Yobe.
Pan Shak ya rubuta cewa, “Wannan tsohon bidiyo ne daga 2024 kuma a garin Zurmi ne na jihar Zamfara.
Ko da yake an samu kai hari a sansanonin soja guda biyu, a karamar hukumar Gujiba jihar ta Yobe a Buni Yadi shelkwatar karamar hukumar da Buni Gari mahaifar gwamnan jihar ta Yobe, amma wannan bidiyo ai tsoho ne.”
Musa Yashi Babawo ya rubuta cewa, “bidiyon da [Sahara Reporters] suka wallafa alamu sun nuna cewa tsohon bidiyo ne kasancewar mayakan na sanye da hulunan sanyi wanda da wahala haka ta faru a lokacin zafi a jihar ta Yobe.”
Ganin irin tsokaci da mutane ke yi da irin matsalar da irin wannan da’awa ke iya haifarwa a wannan kasa da ke a cikin matsalar tsaro, wannan ya sanya DUBAWA gudanar da binciken gano gaskiya.
Tantancewa
Bincike ta hanyar amfani da wasu muhimman kalmomi ya tabbatar cewa dakarun soja sun wargaza tare da tarwatsa harin ta’addanci da aka nufi Birgediya ta 27 a Buni Gari da a wani shingen bincike a Yobe. Mayakan ISWAP da ke dabdala a kewayen Tafkin Chadi su suka tsara wadannan hare-hare a ranar 8 ga Mayu,2026.
Wannan ba shine karon farko ba da aka kai hari a wannan gari kasancewar ma wasu kafafan yada labarai sahihai sun ba da rahoto a wadannan shekaru 2017 da 2018 da 2019 da 2025.
A wani sakon manema labarai daga hadakar dakarun Operation Hadin Kai da mai magana da yawun rundunar Sani Uba ya fitar ya bayyana cewa an wargaza shirin kai farmaki na mayakan na ISWAP inda aka halaka ‘yanta’adda 50 sojoji biyu suka rasa rayukansu a farmakin da ya gaza nasara.
Mun yi kokarin ji daga bakin mai magana da yawun rundunar sojan Onyechi Anele, sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto babu amsa.
Wannan bidiyo da aka yada shi kamar wutar daji lokacin da DUBAWA ta bincika a kansa sai aka samu mabanbantan sakamako bayan amfani da manhajar Google Lens.
Mun gano cewa wannan bidiyo ya fara yaduwa a shafukan sada zumunta tun a watan Fabrairu na 2024, a wannan lokacin an bayyana cewa farmaki ne da ya faru a jihar Zamfara.
DUBAWA ta kuma gano wannan bidiyo tun a 7 ga Afrilu,2025 duka kuma suna magana kan harin ‘yanbindiga da ba a tabbatar ba a Zamfara, kamar yadda za a gani a wadannan wurare nan da nan da nan da nan da nan, ganin shi kansa yanayi na bidiyo za a iya cewa na harin ne na Zamfara.
An kuma sanya wannan bidiyo a manhajar InVid WeVerify. Mun gani a shafin Facebook bidiyo mai kyau da ya fita an wallafa a ranar 9 ga watan Fabrairu,2024, inda aka yi da’awar cewa lamarin ya faru a jihar Zamfara don haka akwai bukatar a hada hannu wuri guda don yakar matsalar ta tsaro.
Mun kuma samu wasu kafafan yada labarai sahihai da suka ba da rahoto
Cewa an farwa wasu al’umma a Zamfara a watan na Fabrairu,2024, sai dai ba za a iya tabbatarwa cewa wannan bidiyo ya fito ne daga wannan yanki ba, da aka kai hari a lokacin.
Wadannan abubuwa da aka binciko sun ci karo da abin da kafar yada labaran ta Sahara Reporters ta fitar inda ta nuna gazawar jami’an tsaro wajen dakile matsalar ta tsaro a yankin da ma yadda kafafan yada labarai ke yin rahotanni akai.
A Karshe
Yayin da kafafan yada labarai suka ba da rahoto na harin ‘yanta’addar da ya gaza nasara a garuruwan Buni Yadi da Buni Gari a jihar ta Yobe, bidiyon da ya yadu ya nuna cewa hari ne da aka kai a jihar Zamfara. Don haka da’awar yaudara ce.