Da’awa: Wani mai amfani da shafin X na da’awar wai wasu Filani ‘yan jihadi sun hallaka kiristoci sama da 350 a Tegina, karamar jukumar Rafi da ke jihar Neja.

Hukunci: Karya ce. DUBAWA ba ta sami wata hujjar cewa wasu kiristoci sama da 350 sun hallaka a hannun wasu filani ‘yan jihadi a Tegina ba. Duk hujjojin da aka gani sun nuna cewa an sami rikici ne tsakanin al’ummomin Filani da Kamuku, sa’annan ba riga an tantance yawan wadanda suka hallaka a sakamakon wannan rikicin ba.
Cikakken bayani
Wani mai amfani da shafin X, @corefrontline, ya wallafa bidiyo (kamar yadda zaku za ku iya gani a nan) ya na da’awar cewa wasi filani ‘yan jihadi sun kashe kiristoci sama da 350 a al’ummar Tegina da ke karamar hukumar Rafi a jihar Neja.
Ga taken da aka yi wa labarin, “…Filani ‘yan jihadi sun yanka kiristoci fiye da 350, maza, mata da kananan yara, yayin da aka kona wasu da dama da ransu a Tegina da ke jihar Neja tsakanin ranakun biyar da shida ga watan Yuli…”
Bidiyon da aka wallafa kuma ya nuna gawawwakin da suka kone cikin wani ginin da shi ma ya kone tare da wani sauti mai tayarda hankali.
Ranar 12 ga watan Yuli 2026, mutane sama da 4,228 sun kalla ko kuma sun yi ma’amala da wannan bidiyon. Akwai kwament hudu, alamar like 16 an kuma sake rabawa sau 11.
Mai amfani da shafin X, @Blow_coin, wanda ya yarda da da’awar ya ce, “tsaro ya shafi kowa da kowa ko da wani irin addini suke bi.
Wani kuma, @VictoriousXots, ya rubuta, “Ba shakka kungiyar kawancen tsaron NATO ke ba su kudi. NATO ba ta kaunar yankin Sahel kuma ta yi kokarin kashe Ibrahim Traore sau 20. Wata kila ma sun yi bukin murnar mutuwar Charlie Kirk.”
Ganin yadda wannan labarin zai iya yin sanadin rikicin addini ya kuma yaudari jama’a ne ya sa DUBAWA tantance gaskiyar labarin.
Tantancewa
DUBAWA ta fara da binciken mahimman kalmomi dan ganin ko akwai labarin da ke da alaka da hallakar kirirstoci fiye da 350 a hannun filani ‘yan jihadi a Tegina. To sai dai babu wani rahoton da ya bulla dangane da wannan batun a cikin kafofin yada labarai masu nagarta, da ma shafukan da hukumomin tsaro ke amfani da su a hukumance.
Mun gudanar da bincike na wasu hotunan da muka dauka a cikin bidiyon. Daga nan ne muka bi diddigin bidiyon muka gano cewa ya bulla ne a karon farko a shafin Facebook, kuma an wallafa bidiyon ne ranar 6 ga watan Yulin 2026 a shafin wani sanannan mai sharhi kan harkokin yau da kullun @DEnglish88.
Yayin da wanda ya wallafa labarin ke ikirarin cewa filani ‘yan jihadi ne suka hallaka kiristoci sama da 350, bidiyon da aka fara dorawa a shafin @DEnglish88 bai kwatanta bidiyon a matsayin wani hari na addini ko ma cewa an kai harin ne a kan kiristoci musamman ba.
DEnglish ya ce ba rikici ne na Boko Haram ko ma ‘yan bindiga ba, rikici ne tsakanin mazauna al’ummar Kamuku da na Fulani wanda ya afku a Tegina.
Domin samun tabbacin cewa haka ne wannan rikicin ya faru, DUBAWA ta tuntubi mazauna al’ummar da shugabanninsu a can a Tegina. Zion Danladi wani manomi ya fada mana cewa “rikici ne tsakanin kabilun Filani da Kamuku ba rikicin addini ba.”
Haka nan kuma, shugaban kungiyar Kamuku ta kasa, Elijah Buzaije Yusuf, ya ce lamarin ya afku ne sakamakon wani abun da ke da nasaba da yanayin zamantakewar al’ummar a maimakon tashin hankalin da ke da nasaba da addini kamar yadda aka nuna.
A cewar Yusuf, Musulmin da suka hallaka a sakamakon rikicin ma sun fi kiristoci yawa. Ya kuma kara da cewa ba’a ma kai ga tantance yawan mutanen da suka hallaka ba, kuma hakan ya kasance har zuwa lokacin da muka hada wannan rahoton wanda ya nuna cewa da’awar wai adadin kiristocin da aka kashe ya wuce 350 ba daidai ba ne.
“Musulmin da suka hallaka lokacin rikicin sun fi kiristoci yawa. Gaskiya a yanzu haka fai ba za mu iya cewa ga adadin mutanen da suka hallaka ba ko daga mutane na na Kamuku, bare a ce a hada adadin kabilun biyu,” Yusuf ya bayyana.
DUBAWA ta yi kokarin tuntubar ofishin ‘yan sand na Tegina sai dai lambar ba ta tafi ba.
Daga nan mun yi ta kokarin jin ta bakin Jami’in Hulda da Jama’a na ofishin ‘yan sandan jihar Neja SP Wasiu Abiodun, wanda ya rika gaya mana cewa ya na jiran karin bayani dangane da batun, amma ba mu ji komai daga wurinsa ba har zuwa lokacin da muka hada wannan labarin
Yunkudin da muka yi na samun karin bayani daga bakin tsohon Jami’in Hulda da Jama’a na NSCDC rundunar jihar Neja, SC Nasir Abdullahi shi ma ya ci tura domin bai amsa duk kiran da muka yi masa ba bare ya maida man.
Bisa la’akar da duka wadannan hujjojin, DUBAWA ba ta sami wata majiya mai nagarta da ta goyi bayan wannan da’awar ta kisar kiristoci sama da 350 a Tegina ba.
A Karshe
Hujjojin da muka gani sun nuna cewa tashin hankalin da aya afku aTegina na jihar Neja, rikici ne tsakanin kabilun Filani da Kamuku ba rikicin addini ba. Haka nan kuma ba’a kai ga tantance yawan wadanda suka hallaka ba dan haka babu hujjar cewa mutanen da suka hallaka sun wuce 350.
Wannan aiki an aiwatar da shi karkashin cibiyar koyon Aikin Jarida da Kirkire-kirkire da Ci gaba (CJID) tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai.