Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook yayi da’awa cewa wata mata an kasheta a baya-bayan nan a Niger saboda batanci ga Annabi S.A.W.

Hukunci: Karya ce. Binciken DUBAWA ya tabbatar da cewa wannan hoto a wata kwalejin ilimi ne sai dai bashi da alaka da abin da ake fadi. Ko da yake an taba samun yanayi na batancin a jihar Niger amma ya faru ne a watan Agusta,2025, babu wani da aka kashe a baya-bayan nan.
Cikakken Sako
A ranar 23 ga watan Agusta,2026 wani mai amfani da shafin Facebook Mustapha Muhammad, ya yada wannan hoto kamar yadda aka (alkinta a nan) dandazon jama’a ne ke kallon yadda tayar mota ke konewa a gefen hanya kamar an kashe mutum an sanya masa wuta. An makala hoton wata mata a gefen hoton daga damansa.
Mai amfani da shafin na Facebook yayi da’awar cewa wata mata ce aka kashe a jihar Niger bayan samunta da laifin yin batanci ga Annabi S.A.W.
Taken labarin a harshen Hausa na cewa,” A jihar Niger yanzu haka sun ce wannan mata ta tsallaka iyaka don haka abin da ya rage mata shine zuwa lahira, Allah Ya tsare mana imaninmu, Amin.”
DUBAWA ta kuma gano wasu da’awowin da aka yada a wasu wuraren kamar nan da nan da nan.
Ya zuwa ranar 27 ga watan Satumba,2026, wannan wallafa a shafin na Facebook ta samu martani 254 da tsokaci 42 da yadawa 2.
Tsokaci da dama da aka rika yi ya nuna cewa “An tsallaka iyaka” kasancewar an yi kalaman batanci ga janibin Ma’aiki.
“Tace wani abu ga Annabinmu,” Habibu Musa Dan Gayarie ya rubuta.
Wani ma mai amfani da shafin Kawomi Kolo, ya fadi ga wani mai tsokacin cewa tsallaka “iyaka” na nufin yin batanci ga Annabi S.A.W.
Abdull Sanee Muhammad ya amince cewa wannan mata “ta tsallaka iyaka” don haka ta cancanci kisa yace abin da aka yi mata shine daidai.”
Duba da yadda ake ta samun masu goyon bayan abin da aka yi a sashin tsokaci dama ganin cewa wannan zai iya jawo rikici na addini da rashin zaman lafiya, DUBAWA ta ga dacewar tantance labarin.
Tantancewa
DUBAWA ta gudanar da bincike ta hanyar amfani da wasu muhimman kalmomi don gano bayanan ‘yansanda ko wata kafar yada labarai sahihiya da tayi rahoto kan yadda matasa suka aikata kisan a jihar ta Niger, sai dai babu wata kafar yada labarai sahihiya da ta ba da rahoton a baya-bayan nan.
Sai dai bayanan sun nunar da cewa an samu batun na labarin batanci ga ma’aiki da ya faru sama da shekara guda abin da ya faru a ranar 30 ga watan Agusta,2025 a Kasuwan Garba, karamar hukumar Mariga da ke jihar.
A cewar rahoton da BBC da Channels TV da The Sun, sun bayyana cewa matasa sun halaka wata mata mai siyar da abinci mai suna Amaye.
Mun gudanar da bincike kan wannan hoto da aka makala don kafa hujja kan da’awar amma sai muka lura cewa bashi da alaka da abin da ya faru a jihar ta Niger.
DUBAWA ta hanyar amfani da Google ta binciki asalin hoton inda ta gano cewa matar da ke jikin hoton sunanta Hauwa Liman mai aikin agaji ce kuma unguwar zoma da ke aiki tare da International Committee of the Red Cross (ICRC) wacce aka yi garkuwa da kasheta a hannun masu ikirarin Jihadi na bangaren Boko Haram a jihar Bornoa watan Oktoba,2018. Ba ta da wata alaka da abin da ya faru a jihar Niger a 2025.
Binciken gano asalin hoton ta Google ya nuna cewa hoton a Facebook an wallafa shi a shafin Ezeigbo Ojukwu a ranar 25 ga Satumba, 2025. Wannan hoto an nuna yadda aka kashe mutum a bainar jama’a a a garin Agbarho, a karamar hukumar Ughelli North a jihar Delta bisa zargin kokari na yin garkuwa da yaro.
Kafafan yada labaran Daily Trust da Independent sun ba da labarin abin da ya faru.
Domin kara bincikar wannan da’awa, DUBAWA ta tuntubi mai magana da yawun jami’an ‘yansanda a Niger SP Wasiu Abiodun wanda ya tabbatar da cewa wannan tsohon labari ne da ya faru sama da shekara guda a Kasuwan-Garba, a jihar Niger.
“Wannan lamarin ya faru sama da shekara guda a Kasuwan-Garba, a jihar Niger,” a cewarsa.
DUBAWA ta kalli dukkanin hotunan guda biyu a lokaci guda dana jihar ta Delta. Dukkanin hotunan guda biyu wuri guda suka nuna, ga bakin hayaki ga gini da bakin rufi daga gefe ga dandazon jama’a da turakun wutar lantarki.
Hoto da ya nuna zargin kisan gilla a jihar Niger da aka yada a shafin Facebook da kuma yadda aka aikata kisan gilla ga wata mata a da aka yi garkuwa da ita a karamar hukumar Ughelli da ke jihar Delta.
Idan ka kalli hotunan a tsanaki za a ga banbance-banbance da suka bayyana a jikin hoton, an rage masa fadi da tsayi an sanya yayi duhu an kuma sauya kayan da ke jikin wasu mutanen a jikin hoton, an sanya hoton Hauwa don sake jan hankali buri na mai da’awar.
DUBAWA ta kuma tura wannan hoto a manhajar da ke tantance ko an hada hoton da kirkirarriyar basira ta AI ta hanyar amfani da manhajar Hive Detect ya kuma nuna cewa kaso 67.9% cewa an hada hoton da kirkirarriyar basira ta AI.

Sakamakon hoto daga Hive AI
Wata hanyar ma ta gano asalin yadda aka samar da hoton ko da AI ita ce, OsintNet, sakamakon da aka samu ya nuna cewa an samu kaso 88/100, da ke nuna cewa an hada wannan hoto da AI ne, tsohon hoto ne aka sake yadawa.

Hoto na sakamako da aka samu daga OSINTnet
A Karshe
Mun gano cewa hoton da aka nuna cewa an kashe wata mata a jihar Niger karya ce, hoto ne da aka gyara shi daga wani hari a 2025 a jihar Delta, sai kuma hoton ma’aikaciyar agaji ta ICRC da ta rasu a 2018.
An gudanar da wannan aiki karkashin Cibiyar koyon Aikin Jarida da Kirkire-kirkire da Ci-gaba (CJID) bisa daukar nauyin Kungiyar Tarayyar Turai.