Site icon Dubawa

Karya ce! Bidiyon da ya shuhura na Cristiano Ronaldo da Georgina Rodriguez a Kaaba, an kirkiro ne da fasahar AI dan yaudarar jama’a

False! Viral video of Cristiano Ronaldo, Georgina Rodriguez at Kaaba, deepfake

Da’awa: Wani bidiyon da ya shuhura wanda aka wallafa a shafin Threads ta Facebook na shahararren dan kwallon Portugal Cristiano Ronaldo da Georgina Rodríguez a Kaaba can a Makka da’awar cewa taurarin biyu sun rungumi addinin Islama.

Karya ce! Bidiyon da ya shuhura na Cristiano Ronaldo da Georgina Rodriguez a Kaaba, an kirkiro ne da fasahar AI dan yaudarar jama'a

Hukunci: Karya ce. Binciken mu ya nuna cewa fasahar da ke da kwaikwayon dabi’un dan adam na AI ne aka yi amfani da shi wajen kirkiro wannan hoton. Cristiano Ronaldo da Georgina Rodriguez ba su koma addinin musulunci ba. Bugu da kari, dokoki sun haramta wa wadanda ba musulmi ba shiga birnin Makka

Cikakken bayani

Wani bidiyo ya shuhura a shafin  Threads (Dandali mallakar kamfanin Meta wanda ke da hade da shafin Facebook),  ya na nuna tauraron na kungiyar kwallon kafar Al-Nassr football Cristiano Ronaldo da abokiyar zaman sa Georgina Rodríguez su na tsaye kuda da Ka’aba a birnin Makka, Saudiyya.

A cikin bidiyon ana iya ganin su tare sun jingina a jikin juna yayin da suke sanye da fararen kayan da mahajata suka saba sanyawa wanda aka fi sani da Ihram. Bacin haka akwai wata murya da ke magana a kan hoton ta na kwaikwayon su ta na cewa:

“As-salamu alaykum, guys. Yau mu na ka’aba, Ma sha Allah, wuri mai kyau, godiya ta tabbata ga Allah. In sha Allah, ku ma za ku zo nan ba da dadewa ba. Allahu Akbar.”

Sadda muka fara gudanar da wannan binciken mutane da dama sun yi ma’amala da labarin inda sama da 38,000 suka danna alamar like, an yi tsokaci 842 yayin da wasu 386 suka sake raba labarin wasu 1,100 kuma suka wallafa batun a shafukansu.

Bidiyon ya bulla ne mako daya bayan da aka kammala ziyarar da aka saba shekara-shekara.

Ganin yadda ya yadu ya kuma dauki hankalin jama’a aka rika neman sanin ko lallai taurari sun zama musulmi ne ya sa DUBAWA daukar nauyin gudanar da bincike dan gano gaskiyar lamarin.

Ka’abar wadda ke tsakiyar  Masjid al-Haram (Babban masallaci/The Grand Mosque) a maka, ita ce wuri mafi tsarki a Islam.

Tantancewa

DUBAWA ta fara da tantance ainihin addinan taurarin biyu inda ta binciki ko akwai wata sanarwa a hukumance dangane da addininsu ko kuma wanda ke cewa sun sauya addini. 

Matsayin addini da abin da suka bayyana cikin rajistar bayanan addinin jama’a

Cristiano Ronaldo mabiyi darikar katolika ne. Ya na yawan bayyana ibadarsa da alakarsa da cocin katolika, musamman yadda ya kan yi alamar giciyye da hannunsa a duk sadda zai shiga filin wasa.

Tun bayan da ya fara wasa a kungiyar kwallon kafar Al-Nassr aka fara rade-radin cewa mai yiwuwa zai musulunta kuma da yawa sun yada jita-jitar a yanar gizo-gizo.

Yayin ‘yan wasa, abokansa da sauran na kusa da shi sun nuna cewa ya na matukar mutunta al’adun Islama da al’adun gargajiya na yankin da ma abokan aikinsa musulmi, babu wani bayani daga Ronaldon kansa ko wani mai 

DUBAWA ta kuma sanya bidiyon cikin manhajar da ke tantance hotunan da aka kirkira da fasahar AI. Binciken ya nuna cewa akwai matsaloli da dama. Na farko akwai rashin jituwa tsakanin motsin fatar bakin su da sautin maganar bidiyon da ma yadda fuskokinsu ke motsi.

Yadda fuskokin ke motsi bai yi kama da yadda dan adam ke motsa jiki ko fuskarsa wanda kuma babbar shaida ce da ke nuna hotunan da aka kirkiro da fasahar AI wanda aka fi sani da deepfake a turance.

Bisa tanadin doka, gwamnatin Saudiyya ta haramata ma wadanda ba musulmi ba shiga birnin Makka da wuraren da kewaye da babban masallacin.

A matsayin su na wadanda ba musulmi bam Ronaldo da Georgina ba za su taba samun iziznin kusantar Ka’abar ba kamar yadda aka gani a cikin bidiyon.

Bitar da muka yi na kafofin yada labaran wasanni masu nagarta bai nuna mana wani rahoto kan musuluntarsu ba bare ma wata ziyarar da suka kai Makka.

Idan da sun musulunta da gaske, labari ne da zai dauki hankali sosai musamman a kafofin yada labarai na kasa da kasa.

A Karshe

Bidiyon da ya nuna Cristiano Ronaldo da Georgina Rodríguez ya na da’awar cewa jaruman sun rungumi musulunci karya ne. Hujjojin da muka samu sun nuna mana cewa an kirkiro hoyon ne. Bacin haka da’awar ta saba da addinin da jaruman biyu suke bi a hukumance da ma tanadin dokokin musulunci kan ai ziyara zuwa birnin mai tsarki.

Exit mobile version