Da’awa:Da dama labaru ne da aka wallafa a shafin Facebook sun yi da’awar cewa a baya-bayan nan dakarun sojan Najeriya sun kama kusan mayakan Boko Haram 488 a jihar Abia.

Hukunci: Karya ne.Bidiyon da ake kafa hujja da shi an same shi ne tun a 2014 bashi da wata alaka da abin da abin da ya faru a jihar Abia kan matsalar tsaro ko ayyukan mayakan Boko Haram a jihar Abia.
Cikakken Bayani
A shekarun baya-bayan nan matsalar tsaro da a baya a ke ganin ta mamaye arewacin Najeriya yanzu na bazuwa zuwa sauran sassa na kasar, ayyukan ’yanfashin daji da ta’addanci na faruwa a sassa daban-daban na kasar kawo yanzu.
Yayin da wannan matsala ke ci gaba da karuwa kafafan sadarwar zamani sun zama wajen yada labaran karya da yaudara inda ake yada labaran kai farmaki da matsalolin tsaro. Sau tarin irn wadannan labaran kan zama na karya kamar yadda DUBAWA ta gano.
A baya-bayan nan wani mai amfani da shafin Facebook yayi da’awa kamar yadda yake anan cewa dakarun sojan Najeriya sun kama mayakan Boko Haram 488 a cikin motoci kirar bas 35.
Ya zuwa ranar 28 ga watan Afrilu, 2026 a lokacin da aka wallafa da’awar an samu wadanda suka nuna sha’awa (likes) mutum 20 da masu tsokaci (comments)8 da wadanda suka sake yadawa (shares) 5.
DUBAWA ta kuma nazarci tsokacin da mutane ke yi kan wannan wallafa don ganin yadda suke kallon batun.
@Etim Akpan ya rubuta cewa “Allah Ya kawo mana dauki” Addinin Musulinci na son mamaye kasar nan, so suke yi ta zama kasa ta mabiya addinin Islama? Wannan shine burinsu?
@Murphy Osass ya rubuta cewa, To yanzu sun kama su, me kuma zai faru a gaba? Zaa shigar da su cikin dakarun sojan Najeriya ne kamar yadda aka saba?”
@Capa Odu yayi tambaya ne da cewa, “zuwa ga jami’an tsaro, da Allah me ke zama manufarsu, wa kuma ya aika su?”
DUBAWA ta samu irin wannan labari kamar a wadannan wurare, nan da nan da nan da nan da nan da nan da nan da nan da nan da nan da nan da nan da nan da nan and nan.
Duba da yadda wannan da’awa ta yadu da muhimmancinta ga jama’a da a batun tsaro na kasa DUBAWA ta ga dacewar gudanar da bincike kan wannan da’awa don gano gaskiyar labarin da kaucewa tada hankali na al’umma ba gaira ba dalili.
Tantancewa
DUBAWA ta lura cewa bidiyon da aka yada daga rahoton gidan talabijin ne, wannan ya sanya dole a tabbatar da tushen rahoton haka kuma ranar da aka fitar da rahoton.
Munyi amfani da manhajar InVID don gano asalin bidiyon, sai muka gano cewa asalin bidiyon ya fito ne daga Channels TV a shafin YouTube shekaru 11 da suka gabata a ranar 15 ga watan Yuni,2014.
Mun kuma gano cikakkun rahotanni da aka fitar wadanda suka nuna yadda dakarun sojan Najeriya suka kama motoci kirar bas da daruruwan matasa da ke kan babbar hanyar Enugu zuwa Fatakwal.Wadanda ake zargin na tsakanin shekaru 16 zuwa 24 ne kuma sun fito ne daga Arewacin Najeriya a kan hanyarsu ta neman aikin yi. Rerahoton da jaridar Vanguard ta fitar a wannan lokaci ya nunar da cewa mahukunta basu samu cikakkiyar sheda ba da za su alakanta matasa da kungiyar Boko Haram.
DUBAWA ta kuma tuntubi jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yansanda a jihar ta Abia Maureen Chinaka, wacce ita ma tayi watsi da wancan zargi tace wannan wani abu ne da ya faru a lokaci mai tsawo.
“Lamarin ya faru shekaru da dama da suka gabata kafin ma na shiga wannan ofishi, wannan kuma ba shine karon farko ba da muke samun ana yada irin wannan labari, ba gaskiya ba ne” a cewarta.
Tace ya kamata al’umma su zam masu lura a duk lokacin da ake yada irin wannan labari kasancewar wasu labarun basu da tushe wasu ma babu su a zahiri amma ana amfani da su wajen yaudarar al’umma.
Karshe
Da’awar cewa a baya-bayan nan dakarun sojan Najeriya sun kama mayakan Boko Haram 488 a jihar Abiya karya ne, bidiyon da aka yi amfani da shi a matsayin sheda, an zakulo shi daga wani abu da ya faru a 2014, bashi da alaka da jihar Abia ko wani abu da ya faru a baya-bayan nan.