.
|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: A wani bidiyo da ya bazu kamar wutar daji yayi da’awa cewa shan tsimi na jikon hanyen gwaiba da lemongrass da leman tsami na maganin ciwon sanyi da ake samu ta sanadin jima’i, wanda ke amfani da Guava and lemon grass.

Hukunci:Karya ce. Ko da yake watakila a samu cewa ganyen gwaiba da lemongrass suna samar da magani da wasu abubuwa masu amfani ga jiki, babu wata sheda a likitance da ta nunar da cewa yana maganin cutar sanyin mara.
Cikakken Sako
Cutuka da ake samu ta dalilin jima’i (STIs) har yanzu na ci gaba da zama babbar barazana ga lafiyar al’umma a fadin duniya. Suna bazuwa ne ta hanyar jima’i, abin da ke kawo su kuma sune bacteria da birus da ‘ya’yan halittar da ke cutar da jama’a na parasites.
A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya fiye da cutukan na jima’i miliyan daya ne da ake iya magance su (STIs) suke faruwa a kowace rana, sau tari a cikin mutane da ke tsakanin shekaru 15-49.
Wata mai amafani da shafin Facebook ta yi da’awa cewa idan aka hada ganyen gwaiba da lemongrass kamar yadda yake a nan abin na maganin cutuka da ake yadawa ta sanadin jima’i abin da kan sahfi mafitsara.
Wannan mata ta yi bayani kan yadda ake hada wannan magani da kayan da ake sawa da suke taimakawa wajen magance cutar.
Tace, “Idan kana da duk wani nau’i na cuta a jiki, kaje ka hada wannan magani wanda ke warkar da ciwon sanyi kamar Gonorrhoea (Goloriya) ko Syphilis, ka je ka tafasa ganyan gwaiba da lemon grass da lemon tsami guda biyu a hada a rika sha sau biyu a rana, da safe da dare.
Bayan aikata hakan sai kuma a sanya ruwan a cikin bokiti a zauna a ciki a bari turirin ya shiga dubura, ka aikata hakan za ka ba da labari bayan kwanaki bakwai.”
Ya zuwa ranar 7 ga watan Mayu,2026 wannan wallafa ta samu wadanda suka nuna sha’awarsu 59,000 (likes) da masu tsokaci 1,600 (comments) da wadanda suka yada 6,000 (shares), wadanda suka gani kuwa sun haure 200,000 (views).
DUBAWA ta yi nazari na tsokacin don fahimtar inda suka karkata a dangane da wannan da’awa.
@Ogechi Udochukwu Ta gaskata amfanin wannan maganin inda tace “bayan shan wannan magani na je asibiti don a yi min gwaji, sai likitan yace madam baki da wata matsala da ta shafi sanyi a jikinki. Duk yanayin jikinki ya nuna baki da wata matsala.”
@Kwetun Shalote, da alamu suka nuna cewa yana neman karin bayani a dangane da wannan magani yayi tambaya ne da cewa “Shin ana dafawa ne kowace rana ko sau daya za a dimama ayi amfani da shi a tsawon makon.?”
@Ijeoma Nkwor ita ma ta yi tambaya ne da cewa, “Shin dan shekaru 17 zai iya shan wannan magani?”
Ganin cewa wannan lamari ya shafi batu na lafiya sannan wasu da dama sun yarda da abin da ake fadi, hakan ya sanya DUBAWA ta ga dacewar gudanar da bincike kan batun.
Tantancewa
DUBAWA ta fara da bincike don gano amfani da ke tattare da ganyen gwaiba da lemongrass don alakarsu da wannan da’awa da ake yi.
A cewar wani rahoto da aka gabatar a mujallar Healthline ya nunar da cewa ganyen na gwaiba da ita kanta gwaibar suna dauke da sinadarin vitamin C da potassium da fibre wadanda ke taimakawa wajen nika abinci da kara garkuwar jiki da kula da yawan sukari a jiki da makamantansu, sai dai makalar bata ce yana maganin cutar sanyin mara ba.
WebMD ita ma ta wallafa makala inda tayi magana kan yadda a gargajiyance lemongrass ke taimakawa wajen narkar da abinci da maganin ciwon jiki da rage zazzabi. A makalar an nunar da cewa binciken ya nuna ana iya samun wannan lemongrass ya taimaka wajen yakar kwayoyin cuta na bacteria da fungi.
Bayan duba ga nazarce-nazarce da ake yi da majiyar likitoci kan wadannan shuke-shuke DUBAWA ta lura cewa a duk wadannan tsirrai biyu babu wata sheda a kimiya da ta nunar da cewa lemongrass na maganin cutar sanyi ko da kuwa an gano cewa dukkaninsu suna da wasu abubuwa da ake amfana da su, babu shedar da ta nunar da cewa suna maganin cutar sanyin mara.
Baya ga wannan mun kuma duba ka’idoji da aka shimfida wajen kula da cutar da ta shafi ciwon na sanyi kamar yadda mahukunta a fannin suka nunar, Cibiyar Kula da Kare Bazauwar Cutuka ta (CDC) Hanyar yaki da cutar Sanyi ko gonoriya akwai hanyoyi da masana kiwon lafiya suka zayyana inda ake ba da magunguna masu yaki da kwayoyin cuta kamar ceftriaxone idan ciwon bai yi tsamari ba ga kuma wasu hanyoyin ko matakan kula da ciwon sifilis CDC Syphilis wanda ake iya magani da penicillin, sai dai yawan magungunan da za a yi amfani da su ya danganta da matakin cutar.Duk wadanan magunguna babu wanda aka bayyana amfani da ganyen gwaiba da lemongrass.
Matsayar Kwararru
DUBAWA ta tuntubi Bala Yunusa, kwararren masani kan cutuka masu saurin bazuwa a Asibitin Koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa wanda yayi watsi da da’awar sannan yayi karin bayani da cewa cututtuka na sanyi da suka hadar da goloriya da Sipilis suna samuwa ne ta dalilin wani nau’in bacteria ko dangoginta wadanda ake maganinsu ta hanyar gudanar da gwaje-gwaje.
“Cutar goloriya da chlamydia cuta ce da ke kama mutane ta hanyar bacteria wanda ana maganinta ta hanyar amfani da magunguna samfurin antibiotics,
Yayin da cutar sifilis ake maganinta ta hanyar nau’in wata hanyar, duk wadannan ana maganinsu ta hanyar daukar matakan kula da lafiya masu karfi da amfani da gwajin cutukan da aka yi, da wahala a ce akwai wani magani na jikon wasu ganyayyaki da ake amfani da shi don magance cutar da ke yaduwa ta hanayar jima’i,” a cewar Bala..
Yayi gargadin cewa da’awar za ta haifar da matsala gagaruma musamman ga cutuka irinsu HIV, wanda shine an kasafta shi cikin cutuka da ke bazuwa, wanda kuma ke daukar lokaci ana amfani da magunguna ana dakile cutar, kada ta karya garkuwar jiki.
“HIV cuta ce da ake samunta ita ma ta hanyar saduwa wacce ke karya garkuwar jikin dan’Adam, tana iya gawurta ta zama cutar AIDs mai barzana ga rayuwa. Jin cewa ma amfani da maganin gargajiya zai magance cutuka irin wadannan abune mai hadari, kamata yayi a dauki matakai na kula da lafiya nagartattu, rashin yin hakan babbar barazana ce,” a cewarsa.
DUBAWA ta kuma tattauna da Fatima Abdullahi, masaniya kan harkokin kula da mafitsara kuma mai bincike a Jami’ar Ahmadu Bello tace da’awa irin wannan sai an mata taka tsantsan kasancewar mutane da dama na jin fargaba suna saboda dalilai na jin kunya su je suna yin magani da kansu.
Fatima tace kalubale irin wannan idan aka ga alamu akwai bukatar a je ayi gwaji.
“Kalubalan shine alamun cutar na iya buya, wani na iya ganin fitar ruwa a gabansa ko jin ciwo lokacin yin fitsari sai ya dauka karamin ciwo ne wanda kuma ta yiwu cutar ce ta Goloriya.
Idan ba a yi gwaji ba yadda ya kamata akwai barazana ta cewa azo ana maganin cutar da ba ita ce ba, sai a bar cuta ba tare da yi magani ba.” a cewarta.
Ta yi gargadin cewa samun tsaiko wajen maganin cutar na iya haifar da babbar barazana musamman ga wadanda suke gwammacewa za su yi amfani da magani a gida ba tare da jin shawarar masana ba.
“Abun da ake iya maganinsa na iya zama babbar barazana idan ba a dauki mataki ba yadda ya dace ko kuma idan aka je ana wani magani na daban.
Rashin zuwa da wuri ma na iya zama babbar barazana, tace mutum na iya farawa da ko da fadawa ma’aikacin jinya ne ko wani likita ko masani kan harkar kula da lafiya mafi kusa dsa shi.,” a cewarta.
A Karshe
Duk da cewa ganyen goba da lemongrass suna da abubuwan da za a amfana da su ko da a mangaren lafiya, amma babu wata sheda ta kimiya da ta nunar da cewa suna maganin ciwon sanyi.
