DA’AWA: Wani a Shafin sa na Facebook ya saka bidiyo dake nuna cewa gwamnan jihar Neja Umaru Bago ya sanar da tisge duk Fulani hakimai a jihar.

HUKUNCI: Karya ce! DUBAWA ta gano cewa gwamnan jihar Neja Bago bai bada umari haka ba. Bidiyon ya yi kokarin nuna bayanan da gwamnan ya yi da ya ziyarci sarkin Kontagora inda ya yi magana kan rashin tsaro da rikicin fili.
Cikakken Bayani
A Ranar 19 ga Yuli 2026 Otache Ib Gideon a Shafinsa na Facebook ya saka wani bidiyo (Da aka saka a nan) daya nuna cewa gwamnan jihar Neja Mohammed Bago ya bada umarnin tsige duk hakimai Fulani a jihar.
Da’awar da aka rubuta a karkashin bidiyon ya nuna cewa gwamnan ya tsige duk hakimai Fulani daga matsayinsu na sarakunan gargajiyya.
“Umar Bago ya ce duk wadanda aka yi garkuwa da su kuma aka sako su bayan an biya kudaden fansansu na cewa Fulani ne suka yi garkuwa da su inda hakan ya say a bada wannan umarni. Kalla ka gani. Addu’a na shine jihohin Benuwe, Filato da Taraba da dai sauran jihohi su yi koyi da haka. Da’awar bidiyon kenan.
Zuwa ranar 21 ga Yuli 2026 mutum 165 suka nuna alamun duba bidiyon, 71 sun mayar da martani da 345 sun sake wallafa bidiyon.
Kings Okolo a shafinsa na Facebook wanda ya amince da wannan da’awar ya jinjina wa gwamnan inda ya rubuta cewa ‘Ran ka shi dade ka cancanci ka shugabaci kasar nan. Mun gode maka saboda gaskiyan da ka fada. Fata na shine sauran gwamnoni za su yi koyi da irin shugabancin ka.
Shima Abubakar Umar a shafinsa na Facebook ya ki amincewa da bidiyon inda yake cewa abin da gwamnan ya fada ba daidai bane ake fada da turanci ba.
“Babu basaraken da ya tsige. Kamata ya yi kunemi kwararren tafintan Hausa.
Ganin hakan ya sa DUBAWA ta gudanar da bincike domin tattance bidiyon.
Tantancewa
DUBAWA ta gudanar da bincike inda ta gano cewa babu gidan jaridar da ta dauki wannan labari.
DUBAWA domin tabbatar da ingancin bidiyon wanda ya kareda shafukkan mutane a Facebook inda ta gano wasu bidiyon da suka fi wannan tsawo dake nuna cikakken abin da gwamnan ya fada. Da farko dai bidiyoin ya yi kama da wanda aka dauk yayin da gwamna Bago ya ziyarci fadan sarkin Kontagora Mu’azu Barau II.
Bayanan da gwamnan ya yi da harshen Hausa ya nuna cewa bai tsige Fulani hakimai ba ko wani basarake a jihar Neja ba.
Sai dai gwamnan ya gargaddi wasu sarakunan gargajiyya da su nisantan kansu da kwacewa mutane filayen su inda yake cewa gwamnatinsa ba za ta amince da haka ba.
Gwamnan da yake bayanin ya ce “duk mutanen da aka yi garkuwa da su bayan an biya kudaden fansan su an sakosu sun dawo gida sukan bayyana cewa Fulani ne suka yi garkuwa da su. A dalilin haka ya sa nake kira ga duk shugabanin Fulani da su kwabi ‘ya’yan su kan kauce wa aikata muggan aiyukka irin haka domin ganin an samu zaman lafiya”.
Gwamnan ya yi kira ga manoma da su daina noma kusa da bakin hanya domin gujewa rikici tsakanin su da makiyaya.
Domin tabbatar da ko gwamnan ya yi sanarwa kan tsige hakimai Fulani DUBAWA ta duba da’awar da gwamnan ya yi a shafinsa na Facebook inda babu wani sanarwa irin haka.
DUBAWA ta tattauna da shugaban masu yada labarai na gwamnan Bolagi Ibrahim wanda shima ya karyata bidiyon tare da cewa yaudarace kawai na mutane.
“Wannan ba gaskiya bane; gwamnan mu gwamna ne dake shugabanci na karkato da hankalin mutune kan aiyukkansa.
A Karshe
Da’awar dake nuna cewa gwamnan jihar Niger ya tsige hakimai Fulani karya ne.
Wannan aiki an aiwatar da shi karkashin Cibiyar koyon Aikin Jarida da Kirkire-kirkire da Ci gaba (CJID) tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai.