Da’awa: A kwai shafukan sada zumunta da dama da suka yi da’awa cewa kungiyar masu tada kayar baya Kirista sun tare hanya tare da farwa matafiya Musulmi a yankin Mangu a plateau state nigeria.

Hukunci: YAUDARA CE. Bincike da aka gudanar ya bayyana cewa an kai hari ga matafiya Musulmi inda aka halaka 8 daga cikinsu, lamarin da ya faru a ranar 20 ga Yuni,2025, sai dai babu sheda da ta nuna cewa kungiyar masu tada kayar baya ce ta mabiya addunin Kirista, sabanin abin da ake wallafawa.
Plateau state nigeria has been a focal point for various discussions and events in recent years.
Cikakken Labarin
Wani mai amfani da shafin na Facebook, Northern Nigeria Hub, yayi da’awa a wata wallafa kamar yadda za a iya gani (nan) cewa wani shedar gani da ido a Jos ya fadi cewa masu tada kayar bayan Kirista a Mangu sun tare hanyar zuwa Sabon Gari a karamar hukumar Mangu a ranar 2 ga Mayu,2026, ya kara da cewa Musulmai matafiya an fito da su daga motar da suke tafiya aka kashe su , yayin da a hannu guda jami’an tsaro suna kallo ba tare da daukar wani mataki ba.
Mai da’awar ya nunar da cewa shedun gani da ido su biyu ne suka ba da labarin, cewa Musulmai bakwai da sojoji biyu an halaka su kafin daga bisani da misali karfe shida na yamma aka kawo jami’an tsaro.
Wallafar ta kara da cewa babu wata magana daga bangaren gwamnati ko ‘yansanda da sojoji a dangane da wannan farmaki, ko me wallafar bai iya fayyace cewa ko farmakin na da alaka da kabilanci ba.
Tun bayan da aka wallafa labarin a ranar 4 ga Mayu,2026, an samu masu martani sama da 2,100 da masu tsokaci 1,400 da wadanda suka sake yadawa 1,100, an sanya bidiyon a sashen tsokaci a matsayin sheda kan da’awar da ake yi kamar yadda muka nuna su a nan da nan da nan da nan da nan da nan
Adam Abdullahi, wani mai amfani da shafin Facebook da yayi tsokaci a shafin na Northern Nigeria Hub yace “Daukar fansa ta zama dole.”
Mubarak Usman, wani mai amfani da shafin na Facebook yayi amfani ne da kalamai masu kaushi kan wadanda suke goyon bayan farmakin, ya rubuta cewa “Yayin da nake duba sashin tsokaci na lura da cewa wasu na goyon bayan kisan mutane da basu ji ba basu gani ba don haka, ina addu’a Allah ya sa haka ta faru a kanku ko wadanda kuke kauna idan haka ta faru sai ku dandana ku ji abin da ake ji.”
Sai dai duk da haka DUBAWA ta kuma gano wani tsokaci da ke nuna tantama kan abin da ya faru, yana kuma sanya alamar tambaya kan sahihancin da’awar.
Bulus Iliya yace, “Me yasa kuke tura labarai da ke iya tada hankulan al’umma da ka iya kawo tashin hankali, wannan farfaganda ce mai hadari, lamarin bai da kyau.”
Mike Goman, wani mai amfani da shafin na Facebook yace wannan an tsara ne don farfaganda da sanya tsana a tsakanin al’umma. A cewarsa.
“Mai yada labarin ya kamata ya rika tantance bayanai kafin sakinsu.Wannan kasa na cikin halin tashin hankali da fargaba ana taka tsantsan, da Allah a bamu zaman lafiya, mu rungumi juna ba tare da banbanci na addini ko kabila ba.”
Ganin yadda wannan wallafa ta dauki hankali da mabanbantan tsokaci hakan na iya jawo rikicin kabilanci da addini wannan ya sanya DUBAWA ganin wajibci na gudanar da bincike da tantance labarin.
Tantancewa
Ta hanyar lalubar wasu muhimman kalmomi a yayin bincike DUBAWA ta gano rahotanni daga ranar 20 ga Yuni,2025 wadanda suka yi kama da wannan da’awa da ta yadu yanzu.
A irin wancan lokaci ana zargin matasa a kauyen na Mangu sun farmaki wata mota dauke da fasinjoji Musulmai 32 daga Zaria a jihar Kaduna a hanyarsu ta zuwa Qua’an-Pan a jihar ta Plateau.
Musulmai takwas ne da fari aka kashe su amma rasa rayuka ya karu har zuwa mutane 13 ya zuwa ranar 23 ga watan Yuni,2025.
Gwamnati a wani sakon da Gyang Bere, daraktan yada labaran gwamnan ya fitar yayi Allah wadai da farmakin. Ya zuwa ranar 10 ga Yuli,2025 rundunar ‘yansanda a jihar ta Plateau ta kama mutane 22 da ake zargi kan wannan batu ciki kuwa har da wasu kananan yara biyu.Sai dai babu wata sheda da ta nunar da cewa wadanda suka kai farmakin wasu masu tada kayar baya ne Kirista kamar yadda aka nunar a wannan da’awa da aka yi a baya-bayan nan.
Ya zuwa ranar 5 ga watan Mayu,2026 babu wata kafar yada labarai sahihiya da ta yada wannan labari cewa an kai farmaki ga mabiya addinin Musulinci a wannan yanki. Babu kuma wata gwamnati ko kungiyoyin kare hakkin Musulmi da suka ba da bayanai cewa a baya-bayan nan an kai farmaki a kan wasu mutane nasu a yankin. Rashin maganar tasu kuma ta nuna cewa babu wani abu da ya faru da tuni sun yi raddi.
Ganin irin hadari na irin wannan da hadarin da irin wannan da’awa ke iya haifarwa DUBAWA ta tuntubi Panan Dapar, dan’asalin wannan yanki a jihar ta Plateau kuma shugaban kungiyar matasa wanda yayi watsi da da’awar, sai yayi kira ga mutane su yi watsi da jita-jitar wanda a cewarsa an tsara ta ne don “cimma wata manufa.”
Yace “babu wani farmaki a baya-bayan nan kan matafiya a jihar ta Plateau baya ga wanda ya faru a shekarar bara kan matafiya wadanda suka yada zango a garin a kan hanyarsu ta zuwa karamar hukumar Quanpan a jihar ta Plateau daga garin Zaria.”
Haka nan kuma DUBAWA ta tuntubi kwamishinan ‘yansanda a jihar ta Plateau Bassey Ewah, wanda yace da’awar karya ce, abin da aka yada ya yadu kamar wutar daji a shekarar bara ne.
Mai magana da yawun ‘yansanda a jihar Alfred Alabo, ya bayyana cewa babu farmaki kan Musulmi matafiya, kuma an kai jami’an tsaro a wannan yanki yayin da aka ga wata alama ta “‘yar hatsaniya.”
Alfred yace al’ummar basu da wata kungiya ta masu tada kayar baya mabiya addinin Kirista wadanda aka ce sun yi waccan aika-aika da da’awarta ta yadu kamar wutar daji.
Karin bincike na DUBAWA ya gano cewa an dan samu hatsaniya yayin da wani dauke da bindiga ya kai farmaki ga masu hakar ma’adanai wanda yayi sanadi na kisan wasu matasa biyu ‘yangarin a ranar 30 ga watan Afrilu,2026.
A Karshe
Da’awar cewa wata kungiyar masu tada kayar baya a Sabon Gari karamar hukumar Mangu sun kai farmaki da kashe mabiya addinin Islama karya ce. Lamari mai kama da haka ya faru ne a watan Yuni,2025, babu wata sheda da ta nuna cewa wannan bidiyo da aka yada a baya-bayan nan hakan ya faru kamar yadda mai da’awar ke ikirari.