Site icon Dubawa

Karya ce! Majalisar Dinkin Duniya bata kada kuri’ar yankan kauna kan mulkin Shugaba Tinubu ba 

False! UN did not pass vote of no confidence on Tinubu administration

Tinubu da Guterres. Asalin hoton: Premium Times

Da’awa: wasu masu amfani da shafin Facebook sun yi da’awa cewa Majalisar Dinkin Duniya ta kada kuri’ar yankan kauna kan mulkin da Shugaba Tinubu ke yi a Najeriya gabanin zaben da za a yi a kasar na shugaban kasa a 2027.

Karya ce! Majalisar Dinkin Duniya bata kada kuri’ar yankan kauna kan mulkin Shugaba Tinubu ba 

Hukunci: Karya ce. Kada kuri’ar yankan kauna na wata kasa mai cin gashin kanta baya cikin hurumin Majalisar Dinkin Duniya, mutanen da ke cikin kasa ne kawai ke iya sauya harkokin shugabancinsu bisa tanadin dokarsu da tsarinsu na mulkin dimukuradiyya, abin da ya samu kariya a dokar majalisar kamar yadda yake a tsarin dokar MDD mai lamba ta  2(7).

Cikakken Labarin

Wani shafin Facebook mai suna National Media Frontiers, yayi da’awa cewa Majalisar Dinkin Duniya cikin ‘Hikima’ ta kada kuri’ar yankan kauna kan mulkin Shugaba Tinubu gabanin zaben 2027.

A cewar wallafar Majalisar Dinkin Duniya ta yi wannan gargadi ne ganin yadda halin tabarbarewar rayuwa ke ci gaba da samuwa a kasar ga kuma wasu tarin kalubale a kasar, ganin yadda ake ci gaba da samun karuwar yunwa, wannan na sake nuna cewa mutane na iya sauya ra’ayinsu a dangane da zaben kasar a 2027. Shugaba Tinubu dai na neman karin wa’adi na biyu karkashin inuwar jam’iyyar APC. 

“LABARI DA !!! Majalisar Dinkin Duniya ta kada kuri’ar yankan kauna kan gwamnatin shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu gabanin zaben 2027; lamarin ya haifar da fargaba  da ke nuna cewa mutanen da ke arewacin kasar sama da miliyan 17 ana tura su kusa da samun kai a yanayi na yunwa karkashin wannan gwamnati mai ci ta APC; matsayi mafi muni a tarihin dimukuradiyyar Najeriya,” kamar yadda wani bangare na abin da aka wallafa ya nunar. 

Ya zuwa ranar 7 ga watan Yuli,2026, wannan wallafa ta shafin Facebook kamar yadda aka (alikinta a nan) ta samu martani sama da 1,100 da masu tsokaci 414 da wadanda suka sake yadawa 561. 

DUBAWA ta kuma samu wannan wallafa a shafukan na Facebook da dama kamar yadda za a gani a wadannan wurare nan da nan da nan da nan da nan da nan da nan.

Umar Yahaya, wani mai amfani da shafin na Facebook ya yi martani da cewa “To [Reno] Omokri, kun dai ji daga bakin masu abin, kun yarda cewa akwai yunwa a Najeriya?”

Attahir Abubakar yace, “Ina godiya Majalisar Dinkin Duniya na tona asiri na wasu bangarorin abubuwan da ke faruwa a wannan gwamnati.”

Hamdil Al-amin yace, “Ga wani sabo fil  daga wata duniyar, wannan babban labari ne da yake shigowa, don haka wadanda ke ganin cewa wannan gwamnati na yin wani abu, ya kamata su kuma saurari wani bangaren, saboda wanann na fitowa daga Majalisar Dinkin Duniya ne ba daga majalisar dokokin Najeriya ba.”  

Ganin irin tasirin da wannan da’awa ka iya yi ga wannan gwamnati ga kuma cewa wasu da dama sun aminta da abin da ake fada DUBAWA ya zama wajibi ta gudanar da bincike.

Kuri’ar yankan kauna ta Majalisar Dinkin Duniya 

A matsayinta na jigo a tsarin diflomasiya na kasa da kasa a wannan zamani tun daga shekarar 1945 Majalisar Dinkin Duniya tana kan bakanta na ganin dorewar zaman lafiya a duniya da samun fahimtar juna tsakanin kasashe da ke zama mambobi na MDD, duk da cewa tana kokarin ganin an yi daidai tana kuma tasiri kan tsare-tsare na duniya, sai dai batun kuri’ar yankan kauna kan wata kasa da ke zama mai cin gashin kanta wannan wani abu ne na daban da ke zama bako cikin tsare-tsare da ayyukan wannan majalisa.

Ita kuri’ar yankan kauna tsari ne a kundin tsarin mulki da ‘yankasa ke amfani da shi a majalisa da ke kafa gwamnati, kamar yadda ake gani a tsarin gwamnatin Burtaniya da Indiya, karkashin wannan tsari ‘yanmajalisar na da karfin fada aji suna iya sauke firaminista da gwamnati idan majalisar zartarwa ta gaza samun rinjaye na masu goyon bayanta.

A matsayinta na taron kasashe masu zaman kansu MDD ba ta da dama ta kada kuri’ar yankan kauna kan wata kasa ko shugaban wata kasa, haka kuma MDD bata iya sauke shugaban kasa ko rushe majalisa ko ta tilasta sauya gwamnati ta masu rinjaye.

Kuri’ar yankan kauna na iya faruwa ne idan a cikin majalisar ce, abin da ke iya shafar harkokin mulki na cikinta, irin wannan bata shafar wata kasa ko mulki na yankin wata kasa. 

A kwai misali na abin da ya faru a 2025 lokacin da. kungiyar ma’aikatan MDD ta kada kuri’ar yankan kauna ga Sakataren MDD António Guterres, saboda batutuwa da suka shafi rikici na kwadago da matsala da aka samu a harkar shugabanci.

Majalisar Dinkin Duniya kan mayar da hankali ne kan warware  rikici da sanya takunkumi da haduwa don samun mafita kan abin da ya shafi tsaro, sabanin daukar mataki da ya shafi ba da umarni na majalisa.

A babban Taron na Majalisar Dinkin Duniya taron da ke hada mambobi kasashe su zauna su tattauna kan abubuwa da suka shafi kasashen duniya, kuma abubuwan da suka cimma baya nufin a karkashin doka an tilasta wata kasa.

Wannan haduwar bata nufin a kada kuri’a ta yankan kauna kan wani tsari na shugabanci.

Dokar Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 2(7) ta ba da kariya ga iyakoki na gwamnatoci abin da ya haramta wa MDD tsoma baki kan abubuwan da suka shafi harkoki na cikin gidan wata kasa. Ka’idoji  na kasa mai cin gashin kanta ya ba da dama kowace kasa ta gudanar da harkokin mulkinta da fitar da tsarin dokokinta da zabar shugabanta ba tare da tsoma baki na wasu daga waje ba, 

Hakki ne da dama ta al’umma ta kasa wadanda za su yi duk abubuwan da suke muradi a cikin kasa da bin tsarin dimukuradiya ya tanadar idan suna muradi.

Fassara ta daban

Duk da amfani da wasu muhimman kalmomi wajen bincike DUBAWA ta gaza gano wata kafar yada labarai sahihiya da ta yi labarin cewa MDD ta kada kuri’a ta yankan kauna kan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu. 

Abin da muka gano shine akwai rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da sako kan Shirin Samar da Abinci na Duniya WFP. A jawabin da ta fitar tace sama da mutane miliyan 17 daga arewacin Najeriya da wasu miliyan 36 ‘yan Najeriya na fama da matsalar yunwa ko matsalar rashin abinci mai gina jiki kamar yadda nazari da hadakar bayanan cibiyar ya nunar a baya-bayan nan.

Jawabin da ya samu rattaba hannu na Kinday Samba, babbar darakta mai kula da Afurka ta Yamma da Afurka ta Tsakiya inda ta gano rikici da sauya matsugunai da raguwar kai tallafi ga al’umma lamuran da suka kara ta’azzara matsalar rashin abinci a kasar.

Bayan fitar wannan bayanai na shirin na MDD a ranar 2 ga watan Yuli,2026, Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta zargin mahukunta a Najeriya da ke mulki yanzu da nuna halin ko in kula kan batun na yunwa da rasa rayuka da ake yi a kasar.

A sakon da  ya  samu rattaba hannu na sakataren yada labarai na jam’iyyar Bolaji Abdullahi ya kafa hujja da bayanan da aka samu a matsayin abin dogaro ko shedu da suka nuna rashin iya gudanar da mulki na shugabannin da rashin bawa abubuwan da suka dace fifiko da tsare-tsare marasa kan gado.

DUBAWA ta tuntubi Oluseyi Soremekun, baban jami’in yada labarai na MDD na kasa ta hanyar tura masa da sakon email don neman karin bayani.

Oluseyi, a amsar da ya bayar yace an shirya wannan da’awa ce don kawai a yada labaran da ba haka suke ba a kawar hankalin al’umma kan ainihin abin da ke akwai “don haka abin da aka fada an tsara ne don kawar da hankali daga abin da ainihi muka fitar kan shirin abinci na duniya WFP a sakon manema labarai da muka fitar a ranar 2 ga watan Yuli,2026.”

Yace Majalisar Dinkin Duniya na hada kai da sauran abokan hulda da suka hadar da gwamnatoci da kafafan yada labarai da masu samar da bayanai ko sakonni a kafafan sada zumunta da kungiyoyi masu zaman kansu a kokari na dakile yada labarai da ba haka suke ba gabanin babban zabe da za a yi a 2027.

A karshe

Majalisar Dinkin Duniya bata kada kuri’ar yankan kauna ba a kan Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Da’awar ta ci karo da bayanan nazari da shirin samar da abinci na duniya WFP ya fitar a dangane da tabarbarewar matsalar samar da abinci da ake fama da ita a Najeriya. 

Majalisar Dinkin Duniya ba ta da hurumi a kundin tsarin mulkinta ta kada kuri’ar yankan kauna kan shugabancin wata kasa mai cin gashin kanta, don haka da’awar karya ce.

Exit mobile version