Site icon Dubawa

Karya! Hoton mutanen da ake da’awar an kashe yayin da ake garkuwa da su ba daga Sokoto ba ne

False! Image of kidnap victims killed not from Sokoto

Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook ya wallafa wani hoto na gawawwaki, ya na da’awar  wai mazauna garin Karuwa da ke karamar hukumar Sabon Birni a Sokoto ne wadanda masu satan mutane suka kashe a Sokoto.

Karya! Hoton mutanen da ake da'awar an kashe yayin da ake garkuwa da su ba daga Sokoto ba ne

Hukunci: Karya ce! DUBAWA ta gano cewa hoton ba shi da wata alaka da jihar Sokoto. Ya yi mafari ne daga rahotanni kan ayyukan sojoji kan kungiyoyi masu dammara a jamhuriyar.

Cikakken bayani

Sabon Birni karamar hukuma ce a jihar Sokoto, yankin Arewa maso yammacin Najeriya, kan iyakar jamhuriyar Nijar. Yankin na daya daga cikin al’ummomin da suka fi jin raunin ayyukan ‘yan bindiga da masu garkuwa da jama’a a jihar.

Wani mai amfani da shafin Facebook Garkuwan Danchadi, ya wallafa labarin da ke da’awar wai kwanan nan masu garkuwa da mutane sun hallaka da dama daga cikin mazauna kauyen Kurawa a karamar hukumar Sabon Birni na jihar Sokoto.

Tare da wannan da’awar akwai wani hoto (kuna iya gani a nan) da ke nuna gawawwaki a zube a wani fili haka. 

Da yake rubutu cikin harshen hausa tare da kananan hotuna masu nuna alamar kuka, mai amfani da shafin ya ce, “wadannan na daga cikin mutanen da ake labarin cewa masu garkuwa da jama’a sun hallaka a garin Kurawa da ke karamar hukumar Sabon Birni na jihar Sokoto yanzun nan …. Idan kun yarda ku taimaka ku yada wannan sakon dan ya kai ga mahukuntan da suka dace.”

Zuwa 8, ga watan Yulin  2026, mutane sama da 230 sun yi ma’amala da labarin, wasu 76 sun yi tsokaci, wasu 74 kuma sun sake raba labarin.

Yawancin masu amfani da shafin sun yarda da batun gaskiya ne, yayin da wasu kuma suka nuna shakkunsu.

Wani mai amfani da shafin, Aminu Bello ya ce “Wannan ne gaskiyar abin da ke faruwa da kasarmu. Bari Allah ya kare mu ya rage mana wannan masifar. Lallai Arewa na fuskantar matsanancin rikici.”

Wani shi ma mai amfani da shafin, Hon Nazifi Garba Gatawa, watsi da batun ya yi ya ce an kirkiro labarin ne ya kuma kira mawallafin “makaryaci”  

Ganin yadda ba mamaki akwai karya cikin labarin da ma yiwuwar da’awar ta haddasa fargaba da yaduwar labaran da ba daidai ba ne ya sa DUBAWA tantance batun.

Tantancewa

DUBAWA ta fara da gano ko an yi garkuwa da mutane kwanan nan kamar yadda da’awar harin da aka yi da garkuwa da jama’a a kauyen Kurawa ke bayani

Mun yi amfani da mahimman kalmomi wajen ganowa amma ba mu ga wani rahoton da ke bayanin satan jama’a a Kurawa na Sabon Birni ba.

Domin dada tantance da’awar, DUBAWA ta tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufa’i, wanda shi ma ya yi watsi da da’awar.

A cewarsa, babu wani harin da aka kai kauyen Kurawa kamar yadda aka fada a wannan labarin na Facebook.

“Babu wani harin da aka kai kauyen Kurawa kuma babu mazaunin kauyen da aka kashe, kamar yadda wannan shafin ke da’awa. Yayin da wasu kauyukan na Sabon Birni ke fuskantar ire-iren wadannan hare-haren, ba mu sami wani rahoton wannan harin da ku ke bayani a kai a wannan ranan ba.”

Daga nan DUBAWA ta tantance hoton da aka sa da da’awar cikin shafin binciken hotuna na Google reverse image search.

Wannan shafin ne ya bi diddigin gano asalin hoton a shafin X kuma ya danganta shi da wani aikin sojojin da dakarun tsaron FAN na yankin Tillabéri da ke jamhuriyar Nijar suka gudanar 

Daya daga cikin jaridun kasar Dépêche AES, ta wallafa bidiyoyi da hotunan da suka bayyana wannan harin da aka kai. Taken da aka yi labarin ya bayyana cewa an gudanar da harin ne ranar 30 ga watan Yunin 2026 dan daidaita wasu ‘yan bindigan da ke aiki a yankin Torodi da kewaye da ke yankin yammacin Nijar.

Haka nan kuma shi wannan hoton ya bayyana a wani shafin na X mai suna, Nation Mali @NationMali

Ba’a taba danganta hoton da kauyen Kurawa na Sabon Birni ba bare ma wani rikicin da ya faru a jihar Sokoto. 

A Karshe

Da’awar wai hoton na nuna kissan da masu garkuwa da mutane suka yi a kauyen Kurawa da ke kararmar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto karya ne kawai. 

Wannan aiki an aiwatar da shi karkashin cibiyar koyon Aikin Jarida da Kirkire-kirkire da Ci gaba (CJID) da OSINT  tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai.

Exit mobile version