Labarin da ya shuhura na cewa Trump ya yi wa Tinubu kakkausar suka kan fashewar bama-bamai a Maiduguri na bogi ne

Da’awa: Wani mai amfani da shafin X ya  wallafa labarin da ke cewa Trump ya yi wa Tinubu suka kan bama-baman da suka fashe a Maiduguri.

Labarin da ya shuhura na cewa Trump ya yi wa Tinubu kakkausar suka kan fashewar bama-bamai a Maiduguri na bogi ne

Hukunci: Karya ce: DUBAWA ta tantance duk bayanan da Trump ya wallafa kwanan nan a shafinsa na soshiyal media Truth Social – wanda Trump ya kirkiro ya kaddamar da kansa a watan Fabrairun 2022 – inda ta gano cewa duk tsokacin da ya yi ya mayar da hankali ne a kan yakin Amurka da Iran da harkokin siyasarsu na cikin gida. Babu wanda ke da dangantaka da Najeriya ko gwamnatin ta.

Cikakken bayani

Akalla mutane 23 suka hallaka yayin da wasu 100 kuma suka yi rauni bayan da aka  ji fashewar bama-bamai da dama a Maiduguri ranar Litini 16 ga watan Maris 2026. Wannan harin ya afku ne a bakin kofar shiga Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri da wadansu kasuwanni biyu wadanda aka fi sani da Post Office da kuma Kasuwar Monday. Binciken farko ya nuna cewa masu kunar bakin wake ne suka aiwatar da harin. 

A halin da ake ciki dai shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bar Abuja ya tafi birnin Landan inda zai gana da Sarki Charles na III dan tattauna batutuwan da suka shafi tsaro, kasuwancin da harkokin gwamnati. 

A cikin wannan yanayin ne wani mai amfani da shafin X, @iOccupyNigeria (kamar yadda zaku iya gani a nan), ya wallafa wani labari a shafinsa ya na cewa shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi wa Tinubu kakkausar suka dangane da yadda ya ke kula da lamarin tsaron kasar. 

“Wannan lamarin ya lalace baki daya. Manyan hare-hare a Maiduguri yau. Asibiti, babbar kasuwa da Post Office – wajen tura sakonni – duk an kai hari! Mutane da dama wadanda ba su ji ba su gani ba duk sun hallaka,” kadan daga cikin martanin da ake zargi Trumo ya wallafa.

“Irin abubuwan da kan faru ke nan idan BABU SHUGABANCI sa’annan an bude iyakoki wa ‘yan ta’adda! Yayin da kasarsa ke fuskantar wani yanayi na GAGGAWA, shugaba Tinubu ya na ziyarar ran gadi a Burtaniya,” a cewar Trump. 

Daga ranar Talata 17 ga watan Maris shafin X din ya nuna cewa an kalli labarin har sau  483,900, an yi tsokaci 760, an sake yadawa sau 4,200 ya sami alamar like, 8,600 sa’annan wasi 1000 sun adana shi a shafinsu. 

Yayin da kadan daga masu amfani da shafin suka bayyana shakkun su dangane da sahihancin bauani, wadansu sun amince cewa ra’ayin Trump ke nan dangane da batun.

“Wannan bai ma yi kama da Trump ba,” a cewar @donsegs7 .

“Me ya sa za ka wallafa wannan? Bayan ba ka tantance ko gaskiya ne ko karya ba???” @AliuZekeri49825 ya rubuta.

“Wannan ya nuna inda rashin tsaro ya kai ke nan a Najeriya,” a cewar @JerryBr72287575

“Dubi irin abun kunyar da muke fuskanta kowace rana saboda rashin shugabanci nagari’” a cewar Sby107 .   

Ganin yadda wannan batun ke da sarkakiya ne muka dauke nauyin tantance gaskiya.

Tantancewa

DUBAWA ta tantance shafin Trump na Truth Social, @realDonaldTrump,  inda ya kan bayyana ra’ayoyin shi ya kuma yi bayani kan abubuwan da ya ke yi. Ba mu sami wani abun da ya danganci harin Maiduguri ba kamar yadda mai amfani da shafin X ya bayyana.

Haka nan kuma mun gano cewa babu labarin da ke da alamar tantancewar da aka sani da shafukan da aka riga aka tantance su a hukumance. Ko da shi ke su bayanan Trump kan dauki wata alama mai launin ja wadda ke nuna cewa an tantance shafin a kan dandalin Truth Social, – wato dandalin wadda mallakar Trump ce.

Labarin da ya shuhura na cewa Trump ya yi wa Tinubu kakkausar suka kan fashewar bama-bamai a Maiduguri na bogi ne

The claimant’s post.                            One of Trump’s original posts on Truth Social.

Mun kuma binciki shafukan Trump din al Facebook da  X inda a nan ma ba mu sami wani abu da ya danganci batun ba.

DUBAWA ta kuma duba ko wata kafa mai sahihanci ta dauki labarin ko ma ta yi amfani da kadan daga cikin bayanan da ya yi amma babu. Sai dai, jaridar Punch ta rawaito cewa fadar shugaban kasa ta bakin babban mai baiwa shugaban kasa shawara kan kafafen yada labarai da sadarwa, Sunday Dare ya karyata labarin. Kafar ta kuma bayyana cewa Dare ya tafi shafin ma na X ya sake karyata labarin a wurin.

A Karshe

Labarin da ke nuna cewa Trump ya soki Tinubu kan bama-baman da suka fashe a Maiduguri karya ne. DUBAWA ta duba shafukan soshiyal media na Trump inda ake da’awar wai labarin ya yi asali amma ko daya ba mu ga wani abu mai kamar haka ba.

Exit mobile version