Site icon Dubawa

Maganar cewa an kirkiri shafin yanar gizo da AI don karyata digirin girmamawa na Rarara ba gaskiya ba ce

Rarara yana karbar digirin girmamawa. Hakkin Mallaka: Rabi’u Garba Gaya

Rarara yana karbar digirin girmamawa. Hakkin Mallaka: Rabi’u Garba Gaya

Da’awa: Wani jarumin barkwanci ya yi ikirarin cewa an yi amfani da AI wato manhajar da ke kwaikwayon dabi’un dan adam, aka kirkiri wani shafin yanar gizo da ya fitar da sanarwar nesanta jami’ar European-American University da ta nesanta kanta daga digirin girmamawa da aka bai wa mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara.

Maganar cewa an kirkiri shafin yanar gizo da AI don karyata digirin girmamawa na Rarara ba gaskiya ba ce

Hukunci: Yaudara ce. DUBAWA ta gano cewa tun 2018 aka yi rajistar shafin ba sabo ne ba.

Cikakken bayani

Wani mai  barkwanci, Mohammed Lawal Masa’ud, ya wallafa bidiyo a shafin Instagram inda ya yi ikirarin cewa European-American University ba ta nesanta kanta daga digirin girmamawa da ta bai wa mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara ba.

Ya kara da cewa wasu ne kawai suka yi amfani da fasahar kirkirarryiyar basira wato AI suka kirkiri wani shafin yanar gizo da ya fitar da sanarwar nesanta kanta, don bata wa Rarara suna.

Bayan da aka yada wani bidiyo, ya jawo muhawara sosai a kafafen sada zumunta, musamman ganin yadda Rarara ya shahara wajen rera wakokin siyasa a Najeriya.

Wannan ne ya sa DUBAWA bincike don gano shin an kirkiri shafin ne domin yada labarin.

Tantancewa

DUBAWA ta duba shafin yanar gizo da aka ce AI ta kirkira shi wato European-American University

Bincike ta hanyar shafin neman bayanan shafukan yanar gizo na whois.com ya nuna cewa an yi rajistar wannan shafi tun daga Jan 24. 2018, ba a baya-bayan nan ba.

Wannan na nuni da cewa ba kirkirar gaggawa aka yi domin bata wa wani suna ba.

Maganar cewa an kirkiri shafin yanar gizo da AI don karyata digirin girmamawa na Rarara ba gaskiya ba ce

Bugu da kari, manyan kafafen yada labarai masu inganci kamar BBC Pidgin, The Guardian da Premium Times sun ruwaito jami’ar na nesanta kanta daga digirin da ake cece-kuce kansa.

A shafin yanar gizon jami’ar, European-American University (EAU) ta fitar da sanarwa cewa babu wani taron karramawa da ta shirya a Abuja, kuma babu digirin digirgir na girmamawa da ta bai wa Dauda Kahutu Rarara. 

Sun ce waɗanda suka shirya taron na Abuja sun nuna kamar sun wakilci jami’ar, amma babu wata izini, kuma jami’ar ba ta amince da wannan taron ba.

A karshe

Ikirarin da jarumin barkwanci Mohammed Lawal Masa’ud ya yi cewa wani ya kirkiri shafin yanar gizo da AI domin bata wa Rarara suna, yaudara ce.

Exit mobile version