Site icon Dubawa

Mako a Takaice: Da’awa Biyar da ta fi Daukar Hankali da DUBAWA ta Tantance a Wannan Mako

Round-Up: Peter Obi’s investment scheme, Access Bank free surgery, other top claims verified last week

Yayin da labaran da ba haka suke ba ke kara yawo a shafukan sada zumunta, tsofaffin bidiyo da hotuna da ake sake yadasu don cimma wata da’awa sune suke kan gaba a makon da ya gabata.

Wadannan sune kashi-kashi na manyan da’awowi da muka rarrabe.

1. Mayaka da ke dauke da makamai mabiya addinin Kirista sun kai farmaki ga matafiya mabiya addinin Islama a Mangu jihar Plateau

Wani mai amfani da shafin Facebook, Northern Nigeria Hub, yayi da’awa cewa wani shedar gani da ido a Sabon Gari yayin zargin masu tada kayar baya mabiya addinin Kirista a yankin Mangu sun tsare hanya a Sabon Gari a karamar hukumar Mangu a ranar 2 ga watan Mayu,2026. Mai amfani da shafin yace matafiya mabiya addinin Islama an fito da su daga cikin mota tare da kashe su yayin da jami’an tsaro da ke wajen suka kasa yin komai don hana farmakin. 

DUBAWA ta gano cewa da’awar yaudara ce, lamarin ya faru ne a watan Yuni,2025, sannan babu wani bidiyo da ya shahara da ya goyi bayan wannan da’awa.

2. Bidiyon katuwar macijiya (mesa) ta bayyana tana tsallaka titi a katafariyar gonar Okomo

Wani bidiyo da ya bayyana ya nuna yadda katoton maciji nau’in mesa ke tsallaka titi yana shiga gonar kwakwar manja, bidiyon da ya yadu tamkar wutar daji.

Wani shafin Facebook mai suna Port Harcourt specials ya nuna wata da’awa da ta nuna wani lamari da ya faru a babbar gonar kwakwar manja a jihar Edo.

Taken labarin ya rubuta cewa, “Wani babban maciji ya bayyana yana tsallaka titi a gonar kewakwar manja a jihar Edo.”

Idan ka kalli bidiyon a cikin tsanaki ya nunar da cewa wannan bidiyo na karya ne kamar yadda aka gano bayan amfani da dabafrun gano asalin bidiyon ta hanyar kirkirarriyar fasahar AI wacce ta gano cewa bidiyon asali ba haka yake ba.

     3. FG announced N300bn to expand two time zones in Nigeria

A ranar 1 ga watan Mayu,2026 wani mai amfani da shafin X @Morris_Monye,ya fitar da rade-radin cewa a Najeeriya ba a lokaci guda gari ke wayewa ba, rana na fitowa da wuri a yankin Kudu maso Gabshin Najeriya da Arewa maso Gabshin kasar kafin ta waye a Legas. Daga nan sai wani mai amfani da shafin na X yayi da’awar cewa gwamnatin tarayya ta ware naira miliyan dubu 300 don samar da sauyin game da batun na wayar gari da faduwar rana, ya zamana kasar na da lokuta guda biyu.

A lokacin da muka bincika mun gano cewa babu wata sheda daga fadar shugaban kasa cewa Najeriya ta bayyana kashe milin dubu 300 don fadada samar da mabanbanta lokutan wayewa da faduwar rana.  

The special adviser to the president on information and strategy, Bayo Onanuga, also debunked the claim.Mai bawa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da tsare-tsare Bayo Unanuga yayi watsi da wannan da’awa.

4. Dakarun sojan Najeriya sun kama mayakan Boko Haram 488 a jihar Abia

A baya-bayan nan wani mai amfani da shafin Facebook yayi da’awar cewa dakarun sojan Najeriya sun kama mayakan Boko Haram 488 a cikin motoci kirar bas 35.

DUBAWA ta yi bincike inda ta gano cewa bidiyon da aka saka bashi da alaka da batun wani lamari ne da ya farun  tun a shekarar 2014, bashi da alaka da batun matsalar tsaro ko batun Boko Haram a jihar Abia.

5. Double promotion letter from Federal University, Ado-Ekit

An X user, @StelxyG, claims that The Federal University, Ado-Ekiti, awarded an electrical and electronics student, Kolapo Segun, a double promotion for attaining a Cumulative Grade Point Average (CGPA) of 4.92. Upon review, DUBAWA identified multiple inconsistencies in the letter. The institution named “Federal University Ado-Ekiti” does not exist, as the only similar institution in Ekiti is the Federal University Oye-Ekiti, while Ado-Ekiti only hosts the Federal Polytechnic Ado-Ekiti.

Exit mobile version