Site icon Dubawa

Babu sheda Ribadu ya bayyana Tinubu da Akpabio cikin manyan masu cin hanci da rashawa

No evidence Ribadu named Tinubu, Akpabio as most corrupt governors

Nuhu Ribadu,tsohon shugaban EFCC. Asalin hoton: Daily Trust.

Da’awa: Wani mai amfani da shafin X yayi da’awa cewa Nuhu Ribadu ya bayyana Shugaba Bola Tinubu da Orji Kalu da Godswill Akpabio a cikin manyan masu cin hanci da rashawa guda biyar a lokacin da suke gwamnoni a 2006.

Babu sheda Ribadu ya bayyana Tinubu da Akpabio cikin manyan masu cin hanci da rashawa

    Hukunci: Babu isassun shedu, ko da dai cewa Ribadu ya bayyana cewa 31 daga cikin 36 na gwamnoni da suke kan mulki a 2006 suna fuskantar binciken EFCC, cewa “Biyar na gaba” ko “mafiya cin hanci” wannan shine abin da ke yawo a shafukan sada zumunta.

    Cikakken Bayani

    A ranar 23 ga Fabrairu,2026 wani mai amfani da shafin X mai suna @DrKalu yayi da’awa kamar yadda za a gani a nan cewa Nuhu Ribadu tsohon shugaban hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya (EFCC) wanda kuma yanzu shine mashawarcin shugaban kasa kan harkokin tsaro ga Shugaba Tinubu ya bayyana sunayen Bola Tinubu da Godswill Akpabio da Orji Kalu cikin manyan masu cin hanci a gwamnoni da suka yi mulki a 2006.
    Ya ce dukkaninsu suna rike da manyan kujerun siyasa a wannan gwamnati, duk da cewa an bayyana su da zama shugabanni mafiya cin hanci da rashawa.

    “A shekarar 2006 shugaban Hukumar EFCC Nuhu Ribadu  ya bayyana a gaban majalisar dattawa inda ya bayyana sunayen gwamnoni biyar da suka fi kaurin suna a harkar cin hanci da rashawa, wadanda hukumar ta EFCC ke sanya idanu akansu Orji Kalu na jihar Abia da  Ahmed Bola Tinubu na Lagos da Ahmed Sani Yerima, na jihar Zamfara da Godswill Akpabio na Akwa Ibom da George Akume na jihar Benue da Chimaroke Nnamani na jihar Enugu,” kamar yadda mai da’awar ya zayyano.

    Wannan wallafa ta samu martani kala-kala daga masu amfani da shafin na X inda wasu ke bayyana ci gaban da aka samu a matsayin abun a yaba.

    “ Wannan tuni ne na abin kunya da ya nuna irin dolantakarmu mu mutane, wadannan mutane da shugaban yaki da cin hanci da rashawa ya zarga da zama a gaba-gaba a cin hanci da rashawa yanzu suke rike da madafun iko da kujerun majalisa, sannan wanda yayi zargin shi ke zama mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro na shugaban kasa, cin hanci da rashawa sanye da babbar riga,” a cewar @jindu7.

    @StephenMat36723, shima wani mai amfani da shafin yayi nasa rubutun da cewa “wadanda ke cewa Najeriya na samun jagorancin masu aikata miyagin laifuka, gaskiya suke fada, sai kuma wani ya zauna yana jiran ganin shugabanci nagari daga wadannan mutane.?”

    Mun gudanar da binciken gano gaskiya kan wannan da’awa ganin yadda take da sarkakiya da ma irin mutanen da ake zarga a ciki.

    Tantancewa

    Da farko mun lura cewa shi wannan mai amfani da shafin na X ya bayyana a jawabinsa cewa “gwamnoni  biyar ne” sai kuma ya jero sunaye guda shida. Sai kuma ya bayyana sunaye 7. 

    A karshe alama ta nunar da cewa shi kansa hoton ya kwafo shi ne daga wani waje 

    DUBAWA ta gano cewa irin wannan da’awa an yi ta a baya wacce ita ma wani mai amfani da shafin na X  ne yayi a watan Fabrairu,2024.  

    Me ya faru a shekarar ta 2006?

    A watan Satumba, 2006, Ribadu a matsayin shugaban EFCC yayi  bayani ga kwamitinm majalisar dattawan Najeriya inda yace EFCC na gudanar da bincike kan gwamnoni 31 daga cikin 36 kan batun ya shafi cin hanci da rashawa.

    A wannan karo sai ya ba da misali da gwamnan Abia Kalu, yace Hukumar EFCC ta samu shedu kansa kan batu na almundahna da sata da cin hanci da rashawa da amfani da ofis ba bisa ka’ida ba da karkatar da kudaden al’umma” ya kara da cewa Kalu yayi amfani da sunan wani kamfani na iyalansa wajen karkatar da kudade da yawansu ya kai miliyan dubu 25 daga asusun jihar.

    Sai dai kuma babu wasu bayanai da al’umma suka samu da ke nuna cewa bayanai ne daga majalisar dattawan ko wata kafar yada labarai sahihiya da a hukumance ta nuna jerin sunayen “gwamnoni biyar mafiya cin hanci” aga sunayen kamar yadda mai da’awar ya nunar.

    Yayin da  Bola Tinubu da Orji Kalu da Sani Yerima da  George Akume da  Chimaroke Nnamani suke zama gwamnoni ne a wancan lokaci, Akpabio, wanda shine shugaban majalisar dattawan Najeriya na yanzu ba gwamna ba ne a 2006, a wancan lokaci kwamishina ne shi a jihar Akwa Ibom karkashin mulkin Gwamna Victor Attah. Duk da cewa ya shiga neman takara a karkashin inuwar jam’iyyar PDP don neman daga tutar jam’iyyar ya kuma samu a 2006, ba a zabe shi ba, ba a kuma rantsar da shi ba har sai a watan Mayu, 2007.

    Ribadu daga baya ya janye kalaman kan Tinubu da Akume da Kalu 

    A watan Fabrairu,2025 a matsayi na mashawarcin shugaban kasa kan harkokin tsaro Ribadu ta hanayar lauyansa a hukumance yaki amincewa 

    Cewa ya taba fadin hakan, a bayyane ko a sirrance cewa Bola Tinubu ko  George Akume ko Orji Uzor Kalu  “sune suka fi sata” daga baitil malin al’umma ko ya taba bayyana su a matsayin “barayi.”

    Ko da yake wannan bai ci karo da batun na Kalu a gaban majalisar dattawan ba a 2006, sai dai kai tsaye za a iya cewa yaci karo da fadin cewa Tinubu da Akume da Kalu sune kan gaba a fagen cin hanci da rashawa cikin gwamnonin. 

    Ya zuwa yanzu cikin kafafafan yada labarai da suka zayyano wadannan jihohi da gwamnoninsu a cikin jerin sunayen sune kafafan yada labaran Nairaland da Proshare. DUBAWA kuma ba za ta karbi wadannan cikin shedu da za ta kafa hujja da su ba a dangane da wannan labari.

    A Karshe

    Duk da cewa akwai shedu da suka nunar da labarin cewa gwamnoni 31 daga cikin 36 da suka shiga karkashin binciken EFCC, bayyana “biyar na gaba-gaba” ko “wadanda suka fi cin hanci”zaa iya cewa bai wuce labari ba irin na kafafan sada zumuntar zaman

    Exit mobile version