Rabe-raben Asusun Ba da Lamuni na IMF ya sanya Najeriya a Gaba Wajen ba da Gundunmawa a Mizanin Tattalin Arziki na GDP a Duniya

A baya-bayan nan rahoto da Asusun ba da Lamuni na IMF ya fitar ya sanya Najeriya cikin kasashe 10 da suka fi ba da gudunmawa a mizanin ci gaban tattalin arziki na  (GDP) a 2026.

A cewar Asusun na IMF Najeriya na cikin kasashe da ke gaba-gaba da za su ba da gudunmawa wajen bunkasar tattalin arzikin duniya a 2026, inda ake sa rai za ta ba da kaso 1.5%  na ta gudunmawar ga tsarin ci gaban tattalin arzikin na duniya a ma’aunin na GDP.

A wannan sabon tsari Najeriya ta sha gaban Afurka ta Kudu a mizanin na GDP a 2026.duk da cewa Afurkan ta Kudu na gaba da yawan abin da take fitarwa a wannan hasashe na Asusun ba da Lamunin na IMF.

Najeriya a tsarin na GDP ana sa rai za ta bunkasa da kaso 4.4% a 2026,inda za ta daga daga mataki na  4.2% a 2025. Ita kuwa Afurka ta Kudu ta daga nata hasashen GDP zuwa  1.4% daga 1.2% a 2025.

A can saman jadawalin Chaina, ita ake sa rai ta ba da kaso 26.6% ga bunkasar ta duniya inda Indiya ke biya mata baya da ba da kaso 17.0%.  Amurka ita ce ta zo a matsayi na uku inda ake sa rai ta ba da kaso 9.9%.

Sauran kasashen sun hadar da Indonesia (3.8%) da Turkiya (2.2%) da Saudiya (1.7%) da Vietnam (1.6%) da Najeriya da Brazil (1.5%) da Jamus  (0.9%).

Kasashen nan guda biyu Chaina da Indiya ana hasashen su za su ba da kusan rabi  a gudunmawar bunkasar tattalin arzikin duniya a 2026. Asusun Ba da Lamunin na IMF yayi hasashen bunkasa ta fuskar tattalin arziki a yankin na Asiya da kasashe masu tasowa a 2026.

A baki daya tsammanin bunkasar da ake a duniya ya tsaya ga kaso 3.3% a 2026, yayin da a zahirance ake sa rai kasashen masu bunkasa da tasowa ta fuskar tattalin arziki za su ba da kaso  5.0%  na GDP a 2026.

Kasashen Afurka Kudu da Sahara ana sa rai su bunkasa da kaso 4.6%  a 2026 abin da ya nunar da kari kan kaso 4.4% a 2025. A cewar Asusun na IMF wannan bunkasa na da nasaba da kayayyaki da ake fitarwa da kokari na samar da daidaito ta fuskar tattalin arziki da sauya tsarin tattalin arziki na wasu kasashen a nahiyar.

Me hakan ke nufi ga Najeriya?

Yayin da wadannan ma’aunai na tattalin arziki ke nuna cewa an samu ci gaba, wannan bai nuna samun ci gaba ga mutanen da ke can kasa ba, kasancewar suna ta fafutuka da hauhawar farashin kayayyaki da tarnaki na tsare-tsare.

A wani rahoto, Bankin Duniya yayi karin haske cewa Najeriya ta samu ci gaba a matakan da take dauka ta fuskar tattalin arziki, sai dai wannan bai samar da inganta rayuwa ba ta mafi akasarin ‘yanNajeriya. 

A rahoto na baya-bayan nan daga PwC yayi hasashen cewa za a samu karin kaso  62% na yawan masu fama da talauci a 2026, inda za a samu mutane miliyan 141 da ke rayuwa a cikin yanayi na talauci.

Ta kara da cewa kimanin mutane miliyan 33.1 ‘yanNajeriya za su fuskanci matsala ta rashin abinci a 2026 saboda matsin tattalin arziki da rikicin da ke faruwa a Arewacin Najeriya, inda anan ne ake samar da abincin. 

A Karshe

Hasashen da Asusun ba da Lamuni na IMF yayi inda ya sanya Najeriya cikin kasashe da za su ba da gudunmawa a bunkasar mizanin tattalin arziki na GDP, wannan ba zai rasa nasaba ba da wasu tsare-tsare da mahukuntan kasar na yanzu suka yi ba ta fuskar tattalin arziki ba, inda gizo ke sakar shine  irin wannan ci gaba na tattalin arziki dole sai an gani a gidajen al’umma, kasancewar al’umma da dama na ci gaba da fama da matsi na tattalin arziki a kasar.

Exit mobile version